Abu uku da ke janyo fitar jini a ba-haya

Mace zaune riƙe da kanta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama na shiga fargaba idan suka ga jini a ba-hayarsu, sai dai sau tari ba abin damuwa bane.
Lokacin karatu: Minti 3

Abu ne da za a iya cewa ba komai bane, amma idan muka gan shi zai iya janyo babbar damuwa.

Mutane da yawa na firgita idan suka ga jini a ba-hayarsu, inda suke tunanin akwai abin damuwa, kamar ko cewa sun kamu da kansar hanji.

Sai dai, akwai wasu abubuwa da dama da ke janyo jini a kashin mutum, wasu suna da haɗarin gaske fiye da saura

Fermín Mearín, darektan wata cibiya da kula da tsarin narkewar abinci a Sifaniya, ya bayyanawa BBC dalilan da suka fi janyo ganin jini a ba-haya.

Ciwon basir ko tsagewar dubura

Yawanci ya kan haifar da samuwar jajayen jijiyoyin jini, wanda za iya gani bayan fitowar hanji.

Likita

Asalin hoton, Getty Images

"Wannan manuniya ce cewar jini na fita daga ƙasan mutum kuma abin da ya janyo shi ya fito ne daga dubura, a cewar Dakta Mearin.

Ba a cika gane irin wannan matsala da wuri ba har sai an yi gwaji.

Za a iya gane tsagewar dubura ta hanyar yin duba cikin tsanaki. Ƴar karamar tsagewa ce a cikin dubura wadda ke afkuwa ga mutanen da ke wahala wajen yin ba-haya ko kuma yin mai tauri - kuma abin yana da zafi sosai.

Tsananin ciwon ciki da gudawa

Bayyanar cututtuka irin kumburi a cikin hanji na janyo tsananin zafi da kuma gembon ciki.

"A wannan yanayin, baya ga kumburin ciki, ana fuskantar gudawa da kuma ciwon ciki sau da yawa," in ji Mearín. Yawancin lokaci suna shafar hanji, kodayake cutar kansar hanji na shafar ƙananan hanjin mutum a wasu lokuta.

Hanjin mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lamarin na janyo gudawa da kuma ciwon ciki.

A nan, ba-hayar mutum na zama daga ja zuwa mai ɗan duhu-duhu, wato mai launuka mabambanta. "Inda yake ciwo a cikin yana kusa da dubura a nan," in ji Mearín.

Taurin ba-haya

Idan kashi ya yi baƙi ko kuma tauri, hakan yana iya nuna akwai zubar jini a cikin ciki.

A wannan yanayin, ya zama dole a yi gwajin hanyar kai abinci a cikin ciki domin gano ko akwai zubar jini a ciki.

A mafi yawan lokuta, bayyanar jini baya nufin akwai wani dalili mai tsanani.

Amma idan jinin ya yi duhu-duhu kuma ya fito da ba-hayar, yana iya nuna cewa ya fito ne daga hanji ko wani wuri.

A nan, likitoci suna ba da shawarar yin gwajin ciki don gano ko an kamu da kansar hanji ko kuma raunuka na jijiyoyin jini.

kayan cikin mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwajin ciki na sanya a gano ko an kamu da kansar hanji ko kuma raunuka na jijiyoyin jini.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wasu ƙasashe, akwai shirye-shirye na musamman na gwajin kansar hanji da ake yi wa al'ummomi waɗanda suka kai wasu shekaru.

Waɗannan shirye-shirye sun ce ganin jini a kashin mutum, alama ce ta barazanar kamuwa da kansar hanji.

Idan aka gano jini a ba-hayar mutum, ana sake yi musu gwaje-gwaje - abin da ke janyo fargaba a zuƙatan mutane da dama.

"Mutane na zuwa nan cike da tsoro, sai dai yawancin lokuta ba barazanar kamuwa da kansa ba ce," in ji Mearin.

Likitoci na komawa yi wa mutanen da suka haura shekara 50 ko ƴan uwansu ke da tarihin kasancewar kansar hanji gwaje-gwaje, don duba cikinsu - musamman hanji.

Duk da cewa akwai muhimmanci a san wani irin launin ba-haya ake gani, akwai buƙatar gane cewa cin wasu nau'in abinci kan yi tasiri kan afkuwar haka.

Alal misali cin tumatir kan sauya launin ba-haya zuwa ja - yayin da shan cakuleti baƙi kan mayar da shi ya yi baƙi.

A kowane irin yanayi, idan aka ga jini a cikin ba-haya, yana da muhimmanci a je a ga likita da wuri domin ɗaukar matakin da ya dace.