Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya a Sifaniya ta tilasta ɗage wasan Valencia
An ɗage wasan da Valencia za ta yi da Parla Escuela a gasar Copa del Rey bayan wata mummunar ambaliyar ruwa ta m,amaye wasu yankuna a ƙasar Sifaniya.
Akalla mutane 62 ne suka mutu bayan mamakon ruwan sama da aka samu a ƙasar, inda garin Chiva da ke kusa da Valencia ya samu ruwan sama na sama da shekara guda cikin sa'o'i takwas.
A ranar Laraba ne Valencia za ta ziyarci Parla wadda ke tazarar mil 15 daga Madrid babban birnin Sifaniya.
An ɗage wasan zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) ta ce tana “aiki tukuru” tare da ƙungiyoyin da abin ya shafa kuma za a iya sake shirya wasu wasannin ranar Alhamis.
A ranar Asabar ne Valencia za ta karbi baƙuncin zakarun gasar La Liga Real Madrid a filin wasa na Mestalla.