Su wane ne ƴan Najeriya da Saudiyya ta saki bayan zargin su da safarar ƙwaya?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Saudiyya sun saki wasu ƴan Najeriya uku da aka tsare a birnin Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ce ta sanar wa manema labarai batun sakin mutanen uku, waɗanda ta ce sun ɗauki akwatunan miyagun ƙwayoyin suka shiga jirgin Ethiopian Airline daga Kano zuwa ƙasar ta Saudiyya a ranar 6 ga watan Agusta, 2025, domin yin umara.
Mutanen dai sun kwashe kusan wata ɗaya suna tsare a birnin Jiddah kafin hukumomin ƙasar suka tabbatar da cewa ba su da hannu a safarar ƙwaya da ake tuhumarsu da ita.
Mutanen da aka saki
Mutanen da aka kama kuma aka saki su ne:
- Maryam Hussain Abdullahi daga jihar Jigawa
- Bahijja Abdullahi Aminu daga jihar Kano
- Abdulhamid Saddiq daga jihar Jigawa
Mijin ɗaya daga cikin matan da aka saki ya bayyana cewa tare suka isa ƙasar ta Saudiyya amma aka riƙe ta bisa zargin kama ta da ƙwayoyi.
"Gaskiya mun shiga cikin dimuwa da alhini amma yanzu muna cikin kwanciyar hankali.
"Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su kama hanyar komawa Najeriya daga Saudiyya." kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Ta yaya aka sako su?

Asalin hoton, NDLEA/FB
Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta ce ita ce ta shiga tsakani domin ganin an saki mutanen.
Mataimakin shugaban hukumar ta NDLEA, Abdul Ibrahim ya shaida wa cewa "Dama a wata biyu da suka wuce, shugaban hukumar, Buba Marwa ya yi yarjejeniya da hukumomin Saudiyya kan cewa idan an kama ƴan Najeriya a sanar mana.
"Bayan an sanar da shi sai aka tanadi duk wasu shaidu da ake buƙata, kamar bayanai da bidiyoyin kyamarorin CCTV aka nuna wa jami'an Saudiyya," in ji jami'in na NDLEA.
Ibrahim ya ce bayanan da aka nuna, ciki har da yadda wasu ma'aikata suka sanya wa mutanen ƙwaya a cikin kaya, sun tabbatar wa mahukuntan Saudiyya cewa ba su ne suka aikata laifin ba.
Ya bayyana cewa an kama ma'aikatan jirgi da na filin jirgin sama da aka kama waɗanda ake zargi da aikata laifin, wadanda tuni aka gurfanar da su a kotu domin yanke hukunci.
Wannan ba shi ne karon farko da ake kama matafiya daga Najeriya bisa zargin shiga da miyagun ƙwayoyi ƙasar ba, duk kuwa da cewa ba da saninsu ba ne.
A shekara ta 2019 an taɓa kama wata matashiya ƴar Najeriya a ƙasar ta Saudiyya bisa zargin safarar ƙwaya.
Matashiyar ta shafe watanni a tsare a kurkukun Saudiyyakafin daga bisani aka sake a ranar 30 ga watan Afrilun 2019 bayan an gano cewa ba ta da laifi, wasu ne suka yi mata sharri.
Mene ne hukuncin safarar ƙwaya a Saudiyya?
Akwai tsauraran hukunce-hukunce kan mutranen da aka kama da laifin safarar ƙwaya a Saudiyya.
Idan aka kama mutum zai iya kwashe dogon lokaci a ɗaure kafin gabatar da shi a kotu.
Hukunci mafi tsauri da ake yanke wa mutanen da aka samu da laifin safarar ƙwaya shi ne kisa, kamar yadda dokar ƙasar Saudiyya ta tanada.
Ma'ikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta ce idan aka kama mutum da laifin safarar ƙwaya a karon farko, ana yi masa hukunci da ɗauri a gidan yari, ko bulala ko cin tarar kuɗi ko kuma a hada masa duka.
Amma da zaran aka sake kama mutum to za a iya yanke masa hukuncin kisa.
Masana kan harkar sufurin jiragen sama a Najeriya na ganin ya zama wajibi hukumomi su tsaurara yadda suke gudanar da bincike a filayen jiragen sama kuma a riƙa yanke tsauraran hukunce-hukunce kan mutanen da aka kama da laifin sanya haramtattun abubuwa cikin kayan matafiya.
Yadda aka kama su
A ranar 6 ga watan Agustan 2025 ne mutanen ukun suka hau jirgin Ethiopian Airlines ET940 daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano International Airport zuwa Jeddah domin gudanar da Umrah.
An kama su ne a ranar 25 ga watan Agustan 2025 bayan wasu gungun mutane da ke aiki a filin jiragen saman MAKIA suka manna takardun ɗauke da sunayensu a wasu jakunkuna da ke ƙunshe da muyagun ƙwayoyin.











