Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da aka kusa cire wa harshe kan ciwon kansa mai alaƙa da jima'i
- Marubuci, Leigh Boobyer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Wales
- Lokacin karatu: Minti 4
An kusa yanke wa wani magidanci harshensa bayan fitowar wani ƙurji a bayan gemunsa, wanda aka gane cewa cutar kansa ce.
Anthony Perriam ya je ganin likita ne bayan jin kumburi a gyamurwa, daga nan ne aka gano cewa yana ɗauke da cutar kansa a da ta shafi kansa da wuyansa, mai alaƙa da cutar sanyin HPV da aka fi kamawa ta hanyar jima'i.
HPV wasu gungun ƙananan ƙwayoyin cuta ne da suka fi shafar fatar ɗan'adam, wadanda a mafi yawan lokuta ba su haifar da wata matsala, sai dai wasu daga cikinsu na iya haifar da cutar kansa ko kuma ƙurajen matse-matsi.
Anthony, wanda ke zaune a birnin Cardiff, ya ce "abin da kawai na taɓa ji shi ne ƙwayoyin cutar HPV na da alaƙa da cutar kansar bakin mahaifa. Ban taɓa tunanin cewa tana iya haifar da cutar kansa kamar wannan ba, musamman ga maza."
Wannan labari na kunshe da hotuna da za su iya tayar da hankali.
Anthony ya kara da cewa: "Ina kallon kaina a matsayin mutum wanda ya yi sa’a tunda a yanzu zan iya cin abinci da kuma magana, amma in da na yi jinkiri kadan, to da na rasa harshena ko kuma na mutu.”
Akasarin masu kamuwa da kwayoyin cutar HPV na warkewa da kansu, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin Wales.
Amma takan iya haifar da kurajen matse-matsi ko ma ta haifar da cutar kansa - kamar kansa a kai ko wuya, ga maza, ko kuma ta bakin mahaifa, ga mata.
Hukumar Lafiya ta Birtaniya na bayar da shawarar yin allurar rigakafi ga yara ‘yan shekara 12 da 13 da kuma mutanen da suka fi shiga hadarin kamuwa da kwayoyin cutar HPV.
“Idan ka ga wani kumburi, ko da ba ya maka ciwo, to ka je a duba,” in ji shi.
“Ba a cika magana sosai kan irin wannan nau’in kansa ba, musamman a tsakanin maza. Daukar mataki da wuri zai iya taimakawa wajen cetin rai.”
Duk da cewa bai ji wasu alamun rashin lafiya ba, hoton CT scan da MRI duk sun tabbatar cewa yana dauke da cutar a watan Maris na 2023.
“A lokacin ina da ‘ya’ya masu shekara shida da mai shekara uku. Su ne wadamda na fi damuwa da su. Hankalina ya tashi saboda su,” in ji mutumin mai shekara 41.
An cire kulalai 44 daga wuyan Anthony, sai kuma babban kulun a kasan harshensa, wanda aka cire ta hanyar tiyatar na’ura.
“Sun ce mini sun gano shi a kan lokaci,” in ji shi.
“Daya daga cikin kulalen na gab da fashewa. In da ya fashe da cutar ta bazu.”
Ya sha wahala wajen gashi da kuma kona cutar, sai da kibarsa ta zabge da kimanin kilo 22.
“Gaba daya miyauna ya kafe,” in ji shi.
“Hatta shan ruwa wahala yake ba ni.
“Na zama babu karfi a jikina har sai da ta kai ga ina amfani da keken guragu.”
Ya kara da cewa: “zama a keken guragu ana tura ni zuwa wurin gashi har sai da ya fara taba lafiyar hankalina.
“To amma iyalina sun karfafa mini gwiwa har na samu sauki.”
Mece ce kwayar cutar HPV?
HPV kwayoyin cuta ne da ke shafar fatar mutum, kuma akwai nau’ukanta sama da 100.
Ana iya daukar kwayar cutar ta hanyar haduwar fatar wajen al’aura, ko lokacin saduwa ko kuma lasan al’aura da baki.
Ana yin rigakafinta a tsarin bayar da rigakafi na yankin Wales, kuma an fi son yin rigakafin a lokacin da yara suka kai shekaru 12 ko 13.
Asibitin University Hospital na yankin Wales ya ce rigakafin ya rage yawan masu kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa da kashi 90% a tsakanin mata da ke tsakanin shekara 20 zuwa 30, tun bayan da aka kaddamar da yin rigakafin a shekarar 2008.
Wani kwararren likitan kunne da hanci da kuma makoshi a hukumar kula da lafiya ta Cardiff da Vale, Sandeep Berry ya bukaci iyaye su yi kokarin ganin ‘ya’yansu sun samu rigakafin.
Ya ce: “An shafe shekaru ana amfani da rigakafin HPV a fadin duniya, ba ta da matsala kuma tana aiki sosai, kuma tana cikin jerin rigakafin da ake bai wa yara a Wales.
“Tana taimaka wa yara mata da maza su kasance cikin koshin lafiya, kare kamuwa da cutar kansa mai alaka da HPV da kuma inganta lafiyar al’umma baki daya.
“Ana yin rigakafin ne a lokacin da garkuwar jiki take da karfi sannan kuma yara ba su fara saduwa ba.”