Me ya sa Amurka ke son sake dawo da hulɗa da Nijar da Mali da Burkina Faso?

A man covered with a Russian flag waves his arms and shouts as supporters of Niger's military leaders gather to demonstrate outside the Niger and French airbases in Niamey on August 27, 2023

Asalin hoton, AFP via Getty Images

    • Marubuci, Paul Melly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa analyst
  • Lokacin karatu: Minti 5

Amurka na yunƙurin fara ɗasawa da ƙasashe uku na Afirka ta yamma da suke fama da rikice-rikicen ƴanbindiga, waɗanda gwamnatin sojojinsu suka ɓata da Faransa, suka koma alaƙa da Rasha.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa Nick Checker, shugaban sashen harkokin Afirka zai ziyarci, Bamako babban birnin Mali domin isar da saƙon "girmama ƴancin Mali," sannan ya tsara "sabuwar alaƙa" da ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Amurka za kuma ta ƙara ƙarfafa haɗaka da sauran ƙawayen Mali, wato Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar "a ɓangaren abubuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro."

Sai dai abun da babu a cikin tsare-tsaren ziyara shi ne batun dimokuraɗiyya da ƴancin ɗan'adam, lamarun da aka san ƙasar da ƙoƙarin fifitawa.

Gwamnatin Biden ce ta dakatar da alaƙar soji da Nijar bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin dimokuraɗiyya a ƙasashen uku a tsakanin 2020 da 2023, inda har yanzu tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum ke tsare a gidansa.

Amma alamu na nuna cewa Amurka na canjawa a tsare-tsarenta da ƙasashen waje a cikin wata 12 da suka gabata tun bayan da Donald Trump ya ɗare mulki a wa'adinsa na biyu.

An fara ganin sabon sauyi ne da rufe ayyukan hukumar agaji ta USAID kwanaki kaɗan bayan rantsar da shugaban.

Sanarwar ziyarar ta Checker ta ƙara da bayyana cewa Amurka za ta girmama da mutunta ƴancin ƙasar. Ƙasashen da suke maƙwabtaka da Mali irin su Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso za su yi farin ciki da samun wannan saƙon.

Gwamnatin Trump ta fito fili ta bayyana ƙarara cewa ba ta damu da tilasta komawar ƙasashen mulkin dimokuraɗiyya ba.

Massad Boulos, babban mai bayar da shawara kan harkokin Afirka kuma makusancin Trump ya bayyana wa jaridar Le Mode ta Faransa a bara cewa, "muna son dimokuraɗiyya, amma a tsarinmu, ba mu amince da katsalandan a harkokin wasu ƙasashen ba. Mutane na da ƴancin zaɓin tsarin shugabancin da suke so."

Babu tabbas ko Amurka za ta koma atisayen soji da take a ƙasar Mali da Burkina Faso

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Babu tabbas ko Amurka za ta koma atisayen soji da take yi a ƙasar Mali da Burkina Faso
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A zamanin mulkin Biden, Janar Michael Langley, shugaban sojojin Amurka a Afirka wato Africom a tsakanin 2022 zuwa 2025, ya bayyana cewa mulki mai kyau na tasiri sosai kafin a ƙara amfani da ƙarfin soji wajen magance matsalar tsaro.

Amma a bara, bayan Trump ya koma mulki, ya bayyana cewa taimakawa wajen yaƙi da ta'addanci na da matuƙar muhimmanci a mulkinsa.

Kuma alamu na nuna cewa yana sa ido sosai a Afirka ta yamma, kamar yada Rudolph Attalah, wani babban jami'in yaƙi da masu tayar da ƙayar baya ya bayyana a ziyararsa ta Bamako a bara.

Sannan a watan jiya, mataimakin shugaban Africom, Janar John Brenna ya tabbatar da cewa Amurka na ci gaba da taimakon ƙasashe guda uku wajen yaƙi da matsalolin tsaron da suke fuskanta.

Amurka - kamar ƙasashen turai - tana damuwa matuƙa kan barazanar tsaron da ƙungiyoyin maru iƙirarin jihadi suke yi a yankin Sahel. A wasu rahotannin, ana cewa kusan rabin kashe-kashen da ke da alaƙa da masu iƙirarin jihadi a yankin ake yi.

Duk da cewa yawancin waɗanda ake kashewa ƴan ƙasar ne, amma Amurka da sauran ƙasashe na fargabar idan mayaƙan suka ƙara ƙarfi, za su iya samun wajen zama, lamarin da zai ba su damar faɗaɗa, kuma lamarin ya ta'azzara.

Masana da masu bincike suna bayyana yankin a matsayin "cibiyar ta'addaci ta duniya," lamarin da zai iya zama barazana ga duniya nan gaba.

Ƙasashen yankin Afirka ta yamma na cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasashen yankin Afirka ta yamma na cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya

Haka kuma ayyukan mayaƙan zai iya zama barazana ga safarar kayayyaki masu muhimmanci, musamman ma'adinai.

Yankin na da ɗimbim albarkatun ma'adinai irin su zinare, sannan Mali na da lithium - wanda ke da muhimmanci wajen haɗa wasu magunguna, sannan Nijar na da uranium.

Tuni dai gwamnatin sojin Nijar ta ƙwace babbar cibiyar haƙar ma'adanin uranium ta ƙasar, wato Orano daga hannun ƴan Faransa, sannan tana yunƙurin ƙulla alaƙa da Rasha.

Haka kuma gwamnatin Trump ya fargabar yiwuwar Rasha ta karɓe komai, musamman wajen shigewa gaba kan alaƙar tsaro da ƙasashen uku.

A yanzu Amurka ba ta kallon kasancewar sojojin Rasha a yankin a matsayin wata barazana. Rasha ta tura sojoji kusan 1,000 a matsayin sojojin haya a Mali, sannan akwai waɗanda suke zuwa aikin sintiri a Burkina Faso a Nijar.

Lokacin Attalah ya ziyarci Bamako, ya nuna cewa Amurka ba ta damu da taimakon sojin Rasha a yankin ba.

Amma akwai alamun da ke nuna cewa Amurka ba ta so ta bar Rasha ta yi kaka-gida a harkokin tsaron ƙasashen uku.

Brennan na Africom ya ce Amurka za ta taimaka wa Mali da Burkina Faso da Nijar ne wajen tattara bayanan sirri, sannan ya nuna alamar cewa wataƙila nan gaba za su iya taimaka musu da makamai.

Sai dai babu tabbas ko ƙasar ta shirya tura dakarun sojojinta zuwa ƙasashen, ko kuma sake buɗe sansanin jirage marasa matuƙa da ke Agadez a nijar, inda take da kusan sojoji 800.

Gwamnatin Nijar ce ta tasa ƙeyarsu bayan gwamnatin Biden ta matsa lamba kan komawar ƙasar turbar imokuraɗiyya.

Bayan juyin mulki ne Ecowas ta buƙaci ƙasashen uku su saka ranar da za su gudanar a sababbin zaɓe dmin mulkin dimouarɗiyya.

Hakan ya sa ƙasashen uku suka fice daga ƙungiyar, sannan suka buɗe wata sabuwa mai suna Sahel States (AES).

A yanzu da yankin ke fuskantar matsaloli da yawa, taimakon Amurka wajen tattara bayanan sirri da ma wataƙila yiwuwar taimaka musu da makamai za su taimaka wajen samun nasara kan mayaƙan.

Amma la'akari da aikin sojojin Faransa na shekaru, da inda ta riƙa tura dubban dakaru domin daƙile matsalar, za a iya cewa aikin soji kaɗai ba zai magance matsalar ba baki ɗaya.

Ba za a iya magance matsalar ba sai an magance matsalolin tattalin arziki da talauci da suka yi wa yankin katutu.