Wane ne Musa al-Sadr, jagoran Shi'a a Lebanon da ya yi ɓatan dabo a 1978?

- Marubuci, Moe Shreif
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
- Lokacin karatu: Minti 10
Gargaɗi: Labarin na ɗauke da hotuna masu tayar da hankali
Wani masanin kimiyyar kwamfuta a jami'a da ke arewacin Ingila yana nazarin hoton wata gawa a ƙoƙarinsa na warware wani muhimmin abin da ya shigewa mutane duhu da ya daɗe yana ci wa al'umma a Gabas ta Tsakiya tuwo a ƙwarya tsawon kusan shekaru 50.
"Ga yadda fuskar gawar take a yanzu?" in ji Farfesa Hassan Ugail na Jami'ar Bradford, yayin da yake kallon hoton fuskar gawar da ta ruɓe da aka gyara ta hanyar amfani da fasahar zamani kafin a saka shi cikin wata na'ura ta musamman don binciken BBC.
Asalin hoton dai ɗan jarida ne ya ɗauka a shekarar 2011, lokacin da ya ga gawar a wani ɓoyayyen ɗakin ajiye gawa a birnin Tripoli na Libya, inda aka gaya masa cewa wataƙila wannan shi ne malamin addinin da ya shahara, Musa al-Sadr, wanda ya ɓace a Libya tun 1978.
Ɓacewar Sadr ta haifar da jita-jita da kuma ƙagaggun labarai marasa adadi.
Wasu na ganin an kashe shi ne, yayin da wasu ke da'awar cewa har yanzu yana raye a wani wuri a Libya.
Ga mabiyansa masu kaunarsa, ɓacewar tasa ta zama abin jan hankali kamar yadda kashe shugaban Amurka John F. Kennedy a 1963 ya jawo ce-ce-ku-ce.
Saboda wannan binciken da muka gudanar na tsawon lokaci, an taɓa tsare ni da tawagar BBC a Libya na tsawon kwanaki.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saboda daraja shi da mabiyansa ke yi masa, sun shiga cikin tsananin damuwa – ba wai kawai a matsayin jagoran siyasa wanda ya tsaya tsayin daka wajen kare hakkin Musulmin Shi'a na ƙasarsa ta Lebanon a lokacin da aka nuna musu wariya ba, har ma a matsayin babban jagoran addini gaba ɗaya.
Mabiya Musa al-Sadr sun ba shi laƙabin jagora, wata girmamawa da ke da wuya a bai wa malamin mazhabar Shi'a mai rai, wadda suka ba shi ne saboda aikin da ya yi wa mabiya mazhabar.
Ɓacewarsa ta ƙara ƙarfafa tasirinsa, domin ta yi kama da abin da ya faru da Imami na 12 na Shi'a Imamiyya wato Imam Mahadi da mabiya mazhabar suka yi imanin ya ɓuya a ƙarni na 9.
Musulmai mabiya Shi'a Imamiyya sun yi imanin cewa Imam na 12 bai mutu ba, kuma zai dawo a ƙarshen zamani domin samar da adalci a duniya.
Har ila yau, ɓacewar Sadr ta sauya tafarkin ɗaya daga cikin yankuna mafi rikitarwa a duniya ta fuskar siyasa da addini da ƙabila – wato Gabas ta Tsakiya.
Wasu sun yi imanin cewa jagoran ya yi amfani da tasirinsa wajen dakile yunkurin al'ummar ƙasar Iran, kafin ya ɓace, a daidai lokacin juyin-juya halin ƙasar.
Akwai ƙoƙarin da Jami'ar Bradford ta yi wajen gano gawarsa. Dan jaridar da ya ɗauki hoton ya ce gawar na da tsayi sosai kamar yadda ake cewa Sadr yana da tsayin mita 1.98m (ƙafa 6 da inci 5 kenan), amma fuskar gawar ba ta bayyana sosai ba.
Shin ko wannan zai warware abin da ya shigewa mutane duhu?
Ni daga ƙauyen Yammouneh ne nake, a tsaunukan Lebanon, inda aka bayar da labarin sanyi mai tsanani na shekarar 1968, lokacin da ambaliyar dusar ƙanƙara ta lalata ƙauyen, wanda Musa al-Sadr ya taka dusar ƙanƙara mai zurfi don zuwa taimaka wa mutanen ƙauyen.

Asalin hoton, Imam Sadr Foundation
Abin mamaki da mutanen ƙauyen ke nunawa wajen ba da labarinsa a yau, yana bayyana yadda aka mayar da shi tamkar camfi.
Wani daga cikinsu ya faɗa min cewa yana tuna lokacin da Sadr yana ɗan shekara huɗu: "Kamar a mafarki inda yake tafiya a kan dusar ƙanƙara da yadda dukkan mutanen ƙauyen ke bin sa, ni ma na bi shi kawai saboda mu taɓa rigarsa."
A shekarar 1968, ba a san Sadr sosai ba a ƙauye mai nisa kamar Yammouneh, amma a hankali ya fara samun suna a faɗin ƙasa.
Amma zuwa ƙarshen shekarun 1960, ya zama babban mutum a Lebanon inda aka san shi da kira ga tattaunawar addinai daban-daban da kuma haɗin kan ƙasa.
Ya yi suna har ya kai matsayin da ake kiran sa da 'jagora' da mabiyansa suka ba shi.
A shekarar 1974, Sadr ya kafa ƙungiyar fafutukar neman ƴanci ga mutanen da aka takewa haƙƙi, wata ƙungiya ta zamantakewa da siyasa wadda ta nemi a bai wa Musulmi mabiya mazhabar Shi'a wakilci na adalci a gwamnati, tare da 'yantar da talakawa daga wahalhalu na tattalin arziƙi da zamantakewa ba tare da la'akari da addininsu ba.
Ƙudurinsa na guje wa wariyar addini ya kai har ma yana yin wa'azi a cikin majami'un Kiristoci.

Asalin hoton, Imam Sadr Foundation
A ranar 25 ga watan Agusta 1978, Sadr ya yi tafiya zuwa Libya bayan an gayyace shi ya gana da shugaban ƙasar a lokacin, Kanal Muammar Gaddafi.
Shekaru uku kafin wannan lokaci, Lebanon ta fada cikin yaƙin basasa inda mayaƙan Falasɗinu suka tsunduma cikin rikicin addinai wanda da yawa daga cikinsu suna zaune a kudancin Lebanon, wurin da yawancin mabiyan Sadr suke.
Falasɗinawan ne suka fara yin musayar wuta da Isra'ila a kan iyaka, kuma Sadr a lokacin yana son Gaddafi, wanda yake goyon bayan Falasɗinu, ya shiga tsakani don kare rayukan fararen hula a Lebanon.
A ranar 31 ga watan Agusta, bayan kwana shida yana jiran haɗuwa da Gaddafi, an ga lokacin da aka ɗauki Sadr daga wani otal a Tripoli cikin motar gwamnati ta Libya. Bai sake bayyana ba tun daga wannan lokaci.
Daga baya jami'an tsaron Gaddafi suka yi iƙirarin cewa ya bar ƙasar zuwa Rome, amma bincike ya tabbatar da cewa wannan ba gaskiya ba ne.
A zamanin Gaddafi, aikin jarida mai zaman kansa abu ne da ba zai yiwu ba. Sai dai a shekarar 2011, lokacin da 'yan Libya suka yi tsayin daka a lokacin juyin-juya hali wato 'Arab Spring', sai ƙofar bincike ta fara ɗan buɗewa.
Kassem Hamadé, ɗan jarida kuma ɗan Lebanon ɗan asalin Sweden wanda ya ruwaito tashe-tashen hankulan, ya ji labarin wani ɓoyayyen ɗakin ajiye gawa a Tripoli da wata majiya ta ce mai yiwuwa yana ɗauke da gawar Sadr.

An samu gawarwaki har guda 17 a cikin firji a ɗakin da aka nuna masa - ɗaya daga cikinsu ta yaro ce sauran kuma duka ta manya ce. An shaida wa Kassem cewa gawarwakin sun kwashe fiye da shekaru 30 kuma hakan ya dace da lokacin da Sadr ya ɓace. Gawa ɗaya kawai a ciki ta yi kama da ta Sadr.
Kassem ya faɗa min: "Wannan akwatun (in ji ma'aikacin mutuwaren) buɗe ta, sai ya buɗe gawar kuma abubuwa biyu ne suka kiɗima ni."
Da farko, Kassem ya ce kallon fuskar gawar da kalar fatar da gashinta na kama da na Sadr duk da daɗewar gawar.
Abu na biyu kuma kamar yadda ya faɗi an kashe mutumin ne.
Ko kuma aƙalla zaton Kassem ne bisa dogaro da ƙwarangwal ɗin kan gawar. Abin ya yi kama da an naushi gawar ne a goshi ko kuma harsashi ya fasa saman idanun ɓangaren hagu.
To sai dai ta ya za mu tabbatar cewa wannan gawar ta Sadr ce?

Asalin hoton, Kassem Hamadé
Mun ɗauki hoton da Kassem ya ɗauka na gawar inda muka kai ga tawagar ƙwararru a jami'ar Bardford da suka kwashe shekaru fiye da 20 suna aiki kan basirar gano fuskar ɗan'adam. Basirar na tantance kamanni musamman a lokacin da kamar ta yi yawa sosai a hotuna, kuma ana da yaƙinin dacewa a kan aikinsu ko da kuwa hotunan na da tangarɗa.
Farfesa Ugail wanda shi ne jagoran tawagar, ya amince da ya kwatanta hoton gawar da wasu hotuna guda huɗu na Sadr da aka ɗauka a wurare daban-daban a lokacin yana raye.
Manhajar ta bai wa hoton gawar maki 100 kuma yawan lamba shi ke nuna dacewar hoto da haƙiƙanin mutumin ko kuma wani daga danginsa.
Idan kuma hoton ya samu lamba 50 hakan na nufin mutumin bai da alaƙa da Sadr. To amma tsakanin 60 da 70 na nufin shi ne ko kuma danginsa. 70 ko fiye da haka ka iya zama mutumin ba tare da tantama ba.
Hotuna sun samu makin daga 60 abin da ya yi sama "yiwuwar na da ƙarfi" cewa Sadr ne, in farfesa Ugail.
Domin tabbatar da hakan Farfesa Ugail ya yi gwama hoton da na hotunan dangin Sadr guda shida da kuma wasu hotunan mutane 100 da aka zaɓo ba bisa tsari ba da ke kama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hotunan danginsa sun samu maki mai yawa da aka gwama su da na gawar fiye da na sauran mutanen da aka zaɓo babu wani tsari. Sai dai sakamakon ya kasance gwami tsakani hoton da aka ɗauka a mutuware da kuma hotunan Sadr lokacin yana raye.
Hakan ya nuna akwai ƙarkarfar yiwuwar cewa Kassem ya ga gawar Sadr. Kuma kasancewar ya ga kan gawar da miki ya fahimci cewa kashe shi aka yi.
A watan Maris na 2023, shekaru kimanin huɗu bayan da na fara ganin hotunan Kassem lokacin za mu iya tafiya zuwa Libya domin yin magana da shaidu sannan kuma mu nemi gawar ta Sadr.
Muna sane da labarin na da sosa rai amma duk da haka mun sha mamakin martanin ƙasar Libya.

Mun je Tripoli a zuwan neman gawar karo na biyu. Kassem wanda ke yi wa tawagar ta BBC rakiya ya kasa tuna sunan yankin da ya ziyarta a 2011, sai dai ya ce unguwar na kusa da wani asibiti.
Kwatsam, sai Kassem ya ce: "Ga ta nan. Na tabbata da haka. Wannan ne ginin da ke ɗauke da mutuwaren."
Wajen ginin kawai muka iya ɗaukar hoto saboda jami'an leƙen asirin Libya suka kwashe mu suka hana mu ɗauka ba tare da wani ƙwaƙƙwaran bayani ba.
An kai mu gidan yari da jami'an tsaron Libya ke gudanarwa inda aka rufe mu a wani wurin kaɗaici bisa zargin mu da leƙen asiri. An rufe mana fuskokinmu karo da yawa a lokacin da ake yi mana tambayoyi.
Mun zauna a gidan yarin har tsawon kwanaki shida to amma daga baya bayan da matsin lamba ya yi musu yawa sun sake mu sannan suka tasa ƙeyarmu.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu mutanen dai sun yi amannar cewa Sadr ya daɗe da rasuwa.
Dr Hussein Kenaan, ftsohon malamain jami'a ɗan Lebanon da ke aiki a Amurka ya ceya ziyarci ofishin ƙasashen wajen na Amurka a birnin Washinton a shekarar da Sadr ya yi ɓatan dabo a 1978, kuma aka shaida masa cewa sun samu rahoton an kashe shi.
Tsohon ministan shari'a na ƙasar Libya, Mustafa Abdel Jalil shi ma ya shaida wa Kassem hakan a 2011: A rana ta biyu da ta uku, sun yi jabun takardunsa cewa zai yi balaguro zuwa Italiya. Sannan suka kashe shi a cikin gidan yarin Libya."
Ya ƙara da cewa: "Gaddafi ne ke da wuƙa da nama a dukkan abubuwa."
Tambayar ita ce to idan Gaddafi ne ya bayar da umarnin kisan Sadr, to me ya sa?
Wani tunanin kamar yadda wani ƙwararre ɗan Iran, Andrew Cooper ya ce shi ne Gaddafi ya samu karsashi ne daga wasu ƴan ƙasar Iran masu ra'ayin mazan jiya cewa Sadr na neman daƙile juyin-juya halin da ake shirin yi a ƙasar.
Sadr ya taimaka wa da dama ƴan Iran masu son kawo sauyi waɗanda ke son kawo ƙarshen gwamnatin Shah Mohammad Reza Pahlavi. To amma ra'ayinsa na sassauci a kan Iran ya sha bambam da na masu ra'ayin mazan jiya kuma hakan ya sa aka tsana shi.
Mako guda kafin ɓatansa, kamar yadda Cooper ya ce, Sadr ya rubuta wa Shah wasiƙa cewa zai taimake shi. To amma bayanai sun nuna an kwarmata wasiƙar ga masu ra'ayin mazan jiya na ƙasar ta Iran.

To sai dai ba Iraniyawa ba ne kaɗai ke son ganin kwanan Sadr ya ƙare.
Gaddafi yana tallafa wa Falasɗinawa da makamai domin kai wa Isra'ila hare-hare daga Kudancin Lebanon - kuma an ambato Sadr yayin watan tattaunawa inda yake fayyace irin ƙoƙarinsa na samar da mafita tare da ƙungiyar PLO mai fafutukar samawa Falasɗinawa ƴanci.
Akwai yiwuwar PLO ta yi amannar Sadr bisa tsoron saka rayuwar al'ummar Lebanon cikin haɗari, wataƙila ya nuna wa Gaddafi cewa ya juya akalarsu.
A daidai lokacin da wasu da dama ke da imanin cewa Sadr ya rasu wasu kuwa na cewa har yanzu da ransa.
Waɗannan kuwa sun haɗaka da ƙungiyar da Sadr ya kafa a shekarun 1970 wadda yanzu haka take da ƙarfi a Lebanon da ake kira Amal.
Shugaban ƙungiyar, Nabih Berri wanda yanzu shi ne kakakin majalisa ya yi amnannar cewa Sadr wanda yanzu haka ya kai shekaru 97 da haihuwa ya rasu. To sai dai yana da damar nuna cewa ya rasun ko kuma a'a.
A 2011 lokacin da Kassem ya ziyarci mutuwaren ta sirri, ba wai kawai ya ɗauki hoton gawar ba ne ita kadai.
Ya kuma yi ƙaƙarin zaro wasu silin gashin gawar, da manufar yin amfani da su a gwajin ƙwayar DNA. Ya bayar da su ga manyan jami'ai a ofishin Berri domin su yi amfani da su a binciken.
Wasu manya-manyan jami'ai da suka haɗa da waɗanda gwamnatin Lebanon ta naɗa su binciki yadda ɓatan Sadr ya kasance ba su yarda da binciken namu ba.
Harwa yau mun kuma gabatar wa da ɗan Sadr, Sayyed Sadreddine Sadr hoton gawar mahaifin nasa kuma shi ma ya ce wannan ba mahaifinsa ba ne.

Asalin hoton, Imam Sadr Foundation
Duk da cewa ba a gasgata binciken na BBC ba amma mun gane yayin binciken cewa har yanzu abu ne a fili tsakanin mabiya ƙungiyar Amal cewa Sadr na raye.
A kowace ranar 1 ga watan Agustan kowace shekara ana bikin tuna wa da ɓatan Sadr.
BBC ta kuma nemi hukumomin Libya da su ce wani abu kan binciken sannan kuma su fayyace me ya sa jami'an leƙen asirin Libya suka kama tawagar ta BBC. Ba mu su ce mana uffan ba.











