Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kun san me ya sa kasuwancin gwal ke da riba mai gwaɓi?
- Marubuci, Debula Kemoli
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 3
Farashin gwal a duniya na ci gaba da tashi, inda a yanzu farashin giram ɗaya ya kai dala dubu hudu bayan tashin da ya yi a watan Afrilun da ya gabata.
Yanzu masu zuba jari na duba hanya mafi sauƙi sakamakon halin rashin tabbas na siyasa da tattalin arziki.
A yanzu haka ana cikin halin rashin tabbas kan kasuwancin gwal ɗin bayan Shugaba Donald Trump ya sanar da shirin sanya haraje-haraje a kan dukkan kayayyakin da ake shiga da su ƙasarsa.
To sai dai masu sharhi sun ce wani abu da ke damun masu zuba jari kuma shi ne jan ƙafar da ake samu wajen sakin bayanan tattalin arziki a yayin da gwamnatin Amurka ta rufe hanyoyin samun bayanan makonni biyu da suka gabata.
Farashin gwal ya tashi saboda jita-jitar da ake yaɗawa cewa kuɗin ruwa zai sauko saboda matsin lamba daga shugaba Trump.
Idan kuɗin ruwa ya sauka, to tsabar kuɗi ma darajarsa za ta ragu abin da zai sa kasuwancin gwal kuma ya samu ɗagawa da jan hankalin masu zuba jari.
A al'adance dai ana yi wa gwal kallon wani abu mai muhimmanci da kuma kadara wadda ya ke taimakawa mutane idan sun shiga halin matsi.
Idan aka samu faɗuwa a harkar hada-hadar kasuwanci, to farashin gwal ma zai iya faɗuwa inda anan ne mutane da dama ciki har da gwamnatoci da masu zuba jari za su sayi gwal ɗin da yawa, a cewar Dr Philip Fliers, masanin tattalin arziki da tarihi a Jami'ar Belfast.
Ba kowanne mutum ne mai zuba jari ke iya sayen ainihin gwal ɗin ba.
Wasu masu jari na zuba kuɗinsu a cikin hada-hadar gwal ɗin amma ba sayan gwal ɗin suke ba a zahiri.
Masu zuba jarin na zuba kuɗinsu a cikin hada-hadar canji.
Bayanai sun ce ana zuba jarin dala biliyan 64 a ɓangaren hada-hadar gwal a cikin shekarar da muke ciki a cewar wata ƙungiyar masu kasuwancin gwal ta duniya.
A watan Janairun 2020, bayan ɓarkewar annobar korona ke nan, farashin gwal ya yi tashin gwauron zabi, to amma a watan Maris ɗin shekarar, sai farashin ya fara sauka.
Gwal dai na da wata daraja ta musamman a harkar zuba jari musamman a lokacin da ake cikin halin rashin tabbas a game da tattalin arzikin kasa ko duniya, ba wai saboda darajarsa ba, saboda tarihin da ya ke da shi.
Kama daga fuskar gwal da aka yi ta Tutankhamun a zamanin baya a Masar da kujerar sarauta ta Asante a Ghana da kuma kujerar sarauta ta Padmanabhaswamy a India, waɗanda duk aka yi su da gwal.
Hakan ya nuna irin muhimmancin da ma'adinin ke da shi a tarihi da addinance da kuma matsayi.
Ba abin mamaki ba ne irin yadda mutane ke ɗaukar gwal a matsayin wata hanya ta ajiyar dukiya.
Mutane kan sayi gwal domin su ajiye a matsayin kadara saboda darajar da yake da ita.
To amma wasu kuwa kan zuba jari ne a harkar kasuwancin gwal din saboda ribar da ake samu ba don su siya su ajiye ba.
Wasu kan sayi gwal da yawa sai su ajiye ko kuma su sayar ta yadda suke amfani da kuɗin sai su zuba jari a wani ɓangare.
Gregor Gregersen, wanda shi ne babban dillalin gwal a Singapore, ya ce yawancin masu siyan kayansa mutane ne da suka jima suna ajiye da gwal wanda aƙalla sukan ajiye gwal ɗinsu fiye da shekara hudu, daga baya sai su kawo su don canja su ko kuma sayar da su.