Matsalolin da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa ya fuskanta – YIAGA

Masu zaɓe

Ɗaya ɗaga cikin ƙungiyoyin da suke sa ido a zaben shugaban ƙasa da ƴan majalisar tarayyar Najeriya YIAGA Afrika ta ce an samu jinkirin malaman zaɓe a mazaɓu da dama a duka faɗin ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Dokta Husaini Abdu ya shaida wa BBC cewa kashi 21 cikin 100 na rumfuna ne kawai suka fara zaɓe da ƙarfe 8:30 na safe kamar yadda ya kamata.

Yayin da har karfe 10:00 na safe kashi 40 na rumfuna ne kawai suka fara zaɓe.

Husaini Abdu ya ce matsalar za ta iya shafar zaben, musamman wajen cunkoson jama’a a rumfunan zaɓe.

Ya ƙara da cewa an samu jinkirin ne saboda ƙarancin motocin da ya kamata su yi safarar masu aikin zaɓe.

Ya ce haka kuma sun lura da cewa na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a BVAS ba ta aiki yadda ya kamata ba a wasu wuraren.

Shugaban na YIAGA ya ƙara da cewa an kuma samu matsalolin sauyawa wasu mutanen rumfunan zaɓe. Kuma a cewarsa ba a yi rabon rumfunan zaɓen yadda ya kamata ba.

Dokta Husaini Abdu ya yi kira ga hukumar zaben ƙasar mai zaman kanta INEC ta ƙara lokacin zaɓe a wuraren da aka samu jinkiri.

To sai dai yayin wani taron manema labarai, shugaban hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ce duk waɗanda suka hau layi kafin 2:30 za su samu damar kaɗa ƙuri’unsu komai tsawon lokacin da za a ɗauka.

Haka kuma kwamishinan hukumar zaɓen a jihar Kaduna ya faɗa wa BBC cewa duk inda aka samu jinkiri to za a ba su damar yin zaɓe a cikakken lokacin da ya kamata su samu.