Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
MDD ta yi gargadi mai tsanani kan yuwuwar bala'in nukiliya a Ukraine
Shugaban hukumar da ke sa ido kan harkokin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya gaya wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa wadanda suke harba makamai a tashar nukiliya ta Zaporizhzhia da ke Ukraine suna wasa ne da wuta yana mai gargadi da irin bala’in da zai iya faruwa a sanadin hakan.
Mista Grossi wanda bai zargi wani bangare da laifi ba, shi da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres sun bukaci da a gaggauta kebe wani sashe a tashar wanda ba za a yi wani aiki na soji ba domin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiyar tashar nukiliyar wadda Rasha ta karbe iko da ita.
Shugaban hukumar ta nukiliya ta duniya IAEA, dalla-dalla ya yi bayani kan irin tarin damuwar da yake da, wadanda ke nuna cewa ana ci gaba da keta haddin zaman lafiyar wannan tasha ta nukiliya mafi girma a Turai.
Da kuma cewa ma’aikatan tashar na aiki c8ikin wani mawuyacin hali tare da kasancewar sojoji da kayan yaki da motocin dakarun na Rasha a wurin.
Rafael Grossi ya ce kasancewar akwai jami’na hukumarsa biyu da aka bari a tashar, hakan yana da matukar muhimmanci domin za su bayar da cikakken bayani na kai tsaye game da duk wani abu da zai faru a tashar.
Ya ce hukumr ta IAEA a shirye take ta tattauna da dukkanin bangarorin ba tare da bata wani lokaci ba, domin amincewa a kan wani mataki mai sauki wanda kuma yake na dole wato tsarin da zai kare tashar.
Shi kuwa Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, cewa ya yi dole ne dakarun Rsaha su ja baya nesa da da'irar da ba a ayyukan soji a tashar.
Sannan su kuma sojojin Ukraine suma kada su shiga wurin.
A wani rahoto na wucin-gadi, hukumar nukiliya ta duniya ta yaba wa ma'aikatan tashar 'yan Ukraine kan yadda suka tsaya kai fata wajen ganin ayyukan tashar na ci gaba da gudana.
Shi ma da yake jawabi ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, shugaban hukumar ta nukiliya Rafael Grossi, ya ce ana bukatar daukar mataki na gaske domin kaucewa bala'i daga tashar.
Jakadan Rasha a Majalisar ta Dinkin Duniya Vassily Nebenzia ya ce kasarsa ta yi maraba da zaman dindindin na jami'an hukumar nukiliya ta duniya a tashar.
Amma kuma ya kara zargin sojojin Ukrine da laifin hrba makamai tashar.
Su kuwa Amurka da Birtaniya sun kara nanata cewa gaba daya laifin na Rasha ne.
Sun yi kira ga gwamnatin Rashar da ta janye dakarunta daga tashar nukiliyar ta Zaporizhzhia da ma duk wani yanki na Ukraine.