Kumbon China ya faɗo cikin duniyar Earth baya harba shi samaniya

Kumbon zuwa sararin samaniya na China ya faɗo duniyar ɗan Adam cikin Tekun Indiya da Pacific, a cewar hukumomin China da Amurka.

Hukumar kula da ayyukan sararin samaniya ta China ta ce akasarin ɓaraguzan kumbon mai suna Long March 5 sun ƙone a sama, tana mai cewa ya dawo duniya ne ta Kogin Sulu da ke yankin Pacific.

Tun da farko masana sun ce abu ne mai wuya kumbon ya faɗo a wuraren da mutane ke zaune.

Faɗowar sakaka da kumbon ya yi ta sa ana nuna damuwa game da kula da tarkacen kumbon da ke kai mutane sararin samaniya.

Hukumar sararin samaniya ta Amurka, Nasa, ta sha kiran takwararta ta China da ta dinga tanadar yadda kumbon zai dinga tarwatsewa zuwa ƙananan tarkace idan ya tashi faɗowa.

Cikin wani saƙon Tuwita, Bataliyar Sararin Samaniya ta Amurka ta ce kumbon Long March 5 "ya faɗo ne da misalin ƙarfe 10:45 na safe (5:45 na yamma agogon Najeriya da Nijar)".

Gurbin da hukumomin suka bayar na faɗowar kumbon ya dace da wani wuri a Kogin Sulu da ke gabas da wani Tsibirin Palwan na ƙasar Philippines, wadda ke arewacin yankin Pacific.

Kumbo-kumbo na China da ke kan hanyar zuwa tashar sararin samaniyarta da ba a kammala ba, wadda ake kira Tiangong, ba su da fasahar da za a iya saita faɗowar tasu.

Harba kumbon na baya-bayan nan shi ne na ranar Lahadi, inda Long March 5 ya ɗauki wani samfurin gwaje-gwaje zuwa tashar ta Tiangong.

Gwamnatin China ta faɗ a ranar Laraba cewa faɗowar kumbon ba za ta saka rayuwar kowa cikin haɗari ba a ban-ƙasa saboda da alama zai faɗa ne cikin ruwa.

Sai dai kuma, akwai yiwuwar wani ɓangare na tarkacensa su faɗo a kan gidajen mutane, kamar yadda ya faru a watan Mayun 2020 inda ya lalata wasu gine-gine.

Kafin ya faɗo, kumbon wanda babu komai a cikinsa yana kusa da wata kusurwar duniyar Earth, inda daga nan aka saita shi don ya sauka amma ba tare da linzami ba.

An harba kumbon na Long March 5 sau biyu kafin yanzu, ɗaya a watan Mayun 2020, na biyun kuma a Mayun 2021 ɗauke da kayayyaki zuwa tashar Tiangong. A duka lokutan biyu, ɓaraguzai na faɗowa kan duniyar Earth a ƙasashen Indiya da Ivory Coast.

Hakan ya biyo bayan wani kumbon gwaji da ya afka a Tekun Pacific a 2018. Sai dai ba a taɓa samun wanda lamarin ya jikkata ba, amma dai ya jawo suka daga masana harkokin samaniya.