Me ya sa muke barci a kan gado?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Zaria Gorvett
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
A yammacin gabar tsibirin Orkney na Scotland, za a ci karo da ƙauyen Skara Brae mai dumbin tarihi da ke garin Bay of Skail.
A Wannan katafaren wurin, mai tarin ciyayi akwai manyan gidaje masu ɗaki ɗaya da ke kewaye da katanga masu kauri da ke lulluɓe da ciyayi da kuma hanyoyin da aka yi da duwatsu a tsakaninsu - an yi watsi da wannan yankin kusan shekara 4500 da suka wuce.
Amma a cikin kowane gida akwai abubuwa guda biyu waɗanda har yanzu suke da wuri a rayuwar zamani - Gadaje.
Gidajen a Skara Brae, da ke arewacin Scotland, galibi suna da siffa iri ɗaya - ɗakuna masu girma kusan daya da kaskon dumama daki a tsakiya da nau'ikan kayan gida masu dumbin tarihi.
Tare da akwatunan ajiya na kaya da aka cika da ɓangarori daban-daban na ajiyan kayan sawa. Kamar akasarin kayan tarihi da aka samu a wannan tsibiri mara bishiyoyi, waɗannan gadaje na tarihi an yi su ne da duwatsu masu kauri.
Duk da haka, suna da dogayen alluna a kawunansu da gefensu , suna da siffar da za a iya gane su nan take.
Idan ba a yi la'akari da rubutun zamanin da da aka yi a kan wasu ba- da kuma wataƙila ƙwarangwal biyu da aka samu jifa-jifa a ƙarkashinsu- za a iya tsammanin cewa na wannan zamanin ne.
Ƴan'adam sun kwashe dubban ɗaruruwan shekaru suna ƙera gadaje.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin littafin 'What we did in bed: a horizontal history' masanin ilimin ɗan'adam Brian Fagan da masaniyar ilimin kimiyya na kayan tarihi Nadia Durrani a Jami'ar California da ke Santa Barbara sun tattara tarihin ci gaban su tun daga farkon lokacin da aka fara ƙera su.
Daga farkon tarihin rayuwar ɗan'adam, ana tunanin cewa wuraren kwana sun ƙunshi tarin ciyayi ne da aka shirya su a kan juna tare da lulluɓe su da ganyayyaki masu laushi, waɗanda ke iya jure wa ƙwari.
Daga nan sai aka fara samun ɓullar gadajen da aka ƙera. Gadajen da aka yi da duwatsu a Skara Brae suna daga cikin tsofaffin da aka taɓa samu, tare da tarin alamu da aka gani a cikin ƙasa a ƙauyen Durrington Walls kusa da Stonehenge - zane-zane na dogayen akwatunan gado na katako, inda wataƙila masu aikin ginin gidajen suka kwana.
Daga shekaru 5,000 da suka gabata, a kusan lokacin da aka fara samun bayyanar fasahohi kamarsu rubuce-rubuce, ƙerarrun gadaje suka fara bullowa a wurare daban-daban a kusan lokaci ɗaya.
Kimanin nisan kilomita 2,735 daga Orkney, a Malta, ramukan binne matatu na al'ada sun bayyana shaidar farkon bullar wannan kayan ɗakin - ciki har da sassakar da aka yi da taɓo na wata mace ta kishingiɗa tana barci cikin kwanciyar hankali, hannu ɗaya a ƙarƙashin kanta, a kan wani dandamali.
Waɗannan gadaje na farko ba wuraren hutawa ba ne kawai. Sau da yawa suna tattare da ma'anoni da ke da alaƙa da mutuwa, a cewar Fagan da Durrani.
A cikin dubban shekarun da suka biyo baya, gadaje sun sauya siffofi - suka ɗauki kamanni daga al'adun mutanen wannan zamanin.
Ga ɗan gajeren tarihin waɗannan wararen na barci a yammacin duniya.

Asalin hoton, Alamy
Masar a zamanin baya - Wuraren hutawa da dandamalin barci
A lokacin da Howard Carter ya buɗe kabarin sarki Tutankhamun a shekarar 1922, ya ci karo da tarin bubuwan da aka ƙera da zinari-kuma shida daga cikin abubuwan gadaje ne.
Kayayyakin na warwatse sakamakon yunkurin fashi da aka yi guda biyu a zamanin baya, sun haɗa da gadon kwaciyar mamaci wanda aka yi masa ado da Zinari inda aka yi zanen kwatankwacin gunkin saniya Mehet-weret da gadon katako mai adon zinari, da kuma gadon tafi-da-gidanka wanda ake naɗewa wanda mai yiwuwa shi ne na farkon irin sa a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar mafi yawan tsoffin gadaje na Masar waɗanda aka yi wa manyan masu hannu da shuni, gadajen Tutankhamun galibi an yi su ne da katako.
Kuma kamar yadda aka saba a wancan zamanin, da matashin sarki yakan dora kansa ne a kan wani matashi mai tauri a madadin wanda ke da laushi.
Ana samun wannan tsarin sau da yawa a yankunan da ke da yanayi mai zafi, inda mai yiwuwa ya inganta yanayin samun iska.
Haka nan ya na iya zama abin sha'awa a matsayin hanyar kiyaye salon gyaran gashi - 'Yan Masar na da, ciki har da kakar Tutankhamun, wani lokacin sukan yi gyaran gashi mai dauke da salo iri-iri, masu kayan ado..

Asalin hoton, Alamy
Roma a zamanin baya - kowanne gado da lokacinsa
Rum a zamanin baya, kamar yadda yake a cikin al'ummomi da yawa, inda mutane ke kwanciya ya danganta ne da matsayinsu a al'umma da matsayin zamantakewa.
Yayin da wasu bayi ke iya kwana kowane dare a kan tabarmar busassun ganyayyaki ko fatun dabbobi, ko kuma kawai su dunƙule a ƙasa, wasu sun fi jin daɗi.
A cikin 2021, masu binciken kayan tarihi sun tono harabar wani tsohon gida a Civita Giuliana, wani yanki na birnin Pompeii na Rumawa, lokacin da suka gano wani ɗakin kwana wanda ya kasance a daskare na kusan shekara 2,000.
Daga cikin tarkacen ɗakin, akwai durowa ta katako, da sauran abubuwa, akwai gadaje guda uku - kuma a ƙarƙashinsu, kwalabe masu ɗauke da ragowar berayen da ke zaune a ƙarƙashinsu.
An yi su da ginshiƙan katako waɗanda aka ɗaure da siririyar igiya da aka jera kamar raga, ba su da katifa, maimakon haka an lulluɓe su ne da barguna.

Asalin hoton, Alamy
A gefe guda kuma, ƴan ƙasa masu wadata suna da gadaje fiye da yadda suka san abin da za su yi da su.
Rumawa sun ƙirƙira samfuran gadaje don ayyuka daban-daban, waɗanda suka haɗa da lectus lucubratorius don karatu, da lectus genialis don sabbin ma'aurata, lectus tricliniaris don zaman jama'a da cin abinci, da kuma lectus kubicularis na barci. Har ma suna da gadon da aka keɓe don yin jana'iza.
Yawancin waɗannan gadaje sun kunshi wani dandamali da aka yi da karfe, wanda aka ɗaura masa siririn katifa.

Asalin hoton, Alamy
Turai a zamanin baya - ƙwari da katifa masu kauri
A ƙarni na 17, Turawa suna da nau'o'in gadaje da za a zaba daga ciki.
Akwai gadajen akwatuna da gadaje masu igiya - waɗanda dole ne a ɗaure su akai-akai, wanda mai yuwuwa ya sa turawa suka kirƙiro da kalmar "sleep tight" - da kuma manyan gadaje na katako masu ginshiƙai hudu.
Amma ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙunshe a kowanne gado na wannan zamanin shi ne katifa mai kauri.
Waɗannan buhunan, waɗanda wani lokaci suke da matuƙar girma, an yi su ne da ƙaƙƙarfan kayan saƙa , waɗanda aka fi sani da “ticking”.
Ana iya cika su da da abubuwa iri-iri, daga gashin tsuntsu zuwa busasshen ciyawa.
Abin da aka cika katifar da ita na da matuƙar tasiri kan yanayin barcin wanda ke amfani da ita.
In ji littafin nan 'At Day’s Close: A History of Nighttime', wani matafiyi da ya ratsa ƙasar Switzerland a shekara ta 1646 ya yi gunaguni sosai game da yadda ya kwana a katifar da aka cika ta da ganyayyaki, wanda ya yi ta wani irin ƙara kuma ta huda masa fata.

Asalin hoton, Alamy
Ko da yake ya kamata - ko aƙalla dai ya kamata - a riƙa shanya katifu masu kauri akai-akai, sun kasance matattaran ƙwari masu cizo.
Gami da al'adar da ta yi yawa a lokacin ta raba gado tare da wasu mutane da yawa, wanda suka hada har da baƙi, galibi ƙwari sukan addabe su.

Asalin hoton, Getty Images
Ingila a zamanin Sarauniya Victoria
Ya zuwa karni na 19, rashin daidaito a Ingila ya kai matsayi mafi girma, yayin da marasa ƙarfi ke kokawa kan rashin samun abin rayuwa a lokacin da ake samun bunƙasar masana'antu.
Wannan, tare da ƙaruwar yawan al'umma, ya haifar da annobar rashin matsuguni a garuruwa da birane.
A London, ƙungiyoyin agaji sun fito da wasu hanyoyin da ba a saba gani ba. Ɗaya daga ciki ita ce "fourpenny coffin" – wasu kwalaye masu siffar akwatin gawa da aka jejjerasu, inda mutane za su iya biyan 'penny' huɗu don su kwana a ciki.
Wani kuma shi ne gadon igiya, wanda kuma aka sani da "two-penny hangover", wanda ɗaruruwan mutane ke zama a kan benci sai su jingina kan wata doguwar igiya, har zuwa safiya lokacin da aka yanke ta - ba zato ba tsammani.
Wannan mai yiwuwa shi ne inda aka samo asalin kalmar "hangover".
Ga masu hannu da shuni kuwa, barcinsu na gab da ya ƙara inganci sosai.
A ƙarshen 1900s wani Bajamushen mai ƙirƙira ya shigar da takardar shaidar mallakar katifa ta farko da ake haɗawa da ƙarfe - wanda ya sauya yadda lamarin barci ya ke.
A yau akwai ƙarin nau'o'in katifu fiye da kowane lokaci, inda ake da gadajen kumfa da gadajen ruwa da gadajen da ake ɗumamawa masu zafi, gadaje masu hawa biyu, da gadaje na Ottoman da gadaje masu rufi… da dai suransu.
Za mu iya yin mamakin abin da mazaunan Skara Brae za su yi da su.










