Kamaru ta maye gurbin koci Brys bayan cacar baki da Eto'o

Asalin hoton, Getty Images
Kamaru ta maye gurbin koci, Marc Brys ba tare da ya ja ragamar wasa ko ɗaya ba - bayan cacar baki da shugaban hukumar ƙwallon kafar kasar, Samuel Eto'o.
An sanar da naɗa, Martin Ndtoungou a matakin kociyan riƙon ƙwaryar tawagar ta Indomitable Lions a wani taron gaggawa na kwamitin hukumar ta Fecafoot.
A wani jawabi da hukumar ta fitar ta ce ''Ta sallami, Brys saboda kalaman rashin girmamawa da wasu halayya marasa ƙyau daga kocin da mataimakansa.''
Cikin watan Afirilu ma'aikatar wasanni ta Kamaru ta naɗa Brys sabon kociyan Indomitable Lions, amma hukumar ƙwallon kafar kasar ta nuna ɓacin ranta kan matakin.
Eto'o tsohon ɗan wasan Barcelona da Inter Milan da kuma Chelsea ya tanadi sunayen fitattun kociyan da ya kamata a tuntuba, amma tun kan ya gabatar da su domin yin zawarcin aiki, sai ya ji an ɗauki Brys, mai shekara 62.
Eto'o da Brys sun hadu a hukumar ƙwallon Kamaru a Yaounde ranar Talata, sai dai wani bidiyo a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da suke cacar baki a tsakaninsu daga baya kociyan ya yi tafiyarsa.
An kuma ga Eto'o, wanda ke jan ragamar shugabancin Fecafoot tun cikin Disambar 2021 na tattaunawa da jami'an ma'aikatar wasannin da yadda suka samu rashin jituwa.
Har yanzu ma'aikatar wasanni ba ta ce komai ba kan lamarin da take takaddama tsakani da hukumar ƙwallon kafar kasar.
Wannan lamarin na faruwa a lokacin da za a ci gaba da wasannin neman shiga gasar kofin duniya a watan gobe, inda Kamaru za ta karbi bakuncin Cape Verde ranar 8 ga watan Yuni daga nan ta kai ziyara Angola ranar 11 ga watan Yuni.
Ana sa ran Ndtoungou, mai shekara 66, zai bayyana 'yan wasan da za su buga wasan biyu a watan goben a taron da zai gudanar ranar Alhamis.
Kamaru tana jan rukuni na hudu da maki hudu a wasa biyu, inda duk wadda ta ja ragamar kowanne rukuni za ta samu damar shiga gasar kofin duniya a 2026 da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada.











