'Ni ba macuci ba ne' - in ji Pogba kan ta'ammali da kwayoyin kuzari

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na Juventus Paul Pogba ya ce shi 'ba macuci ba ne' amma ya amince da kin amincewa da gwajin kwayoyi masu ƙara kuzari da ya kai ga dakatar da shi.
A farkon wannan watan ne aka rage dakatarwar da aka yi wa Pogba daga shekara huɗu zuwa wata 18, bayan kotun shari'ar wasanni ta amince da ta'ammalin da yake a kwayoyin ba da gangan ba ne.
A watan Fabirairu ne hukumar yaki da ta'ammali da kwayoyi ta Italiya (Nado) ta dakatar da ɗan wasan mai shekara 31, bayan gwajin da aka yi masa ya nuna akwai wani sofane na sinadarin testosterone da ke ƙara kuzari - kuma yana ƙara juriya ga tsarin jikin ɗan adam.
"Ni ba macuci ba ne, ba haka nake ba," kamar yadda Pogba ya shaida wa Sky Sports.
"Ni mutum ne da ke son wasanni, Ina son wasan kwallon kafa kuma ba zan taba yin cuta a cikinsa ba. Ina son yin nasarar da babu magudi a cikinta.
"Na yarda na yi rashin nasara ta ko ina, amma banda cuta."
Ragin da aka yi masa ya fara aiki ne daga ranar 11 ga watan Satumba 2023, yayin da wasu makusantan Pogba suka shaida wa BBC cewa zai fara atisaye daga watan Janairu sannan zai iya fara buga wasa daga watan Maris.
"Na amince da wasu kurakurai saboda ina amfani da kwayoyi," in ji Pogba.
Pogba ya koma Juventus a watan Yunin 2022 bayan kwantaraginsa da Manchester United ta ƙare.
Bayan komawarsa wasa 12 kacal ya iya buga wa ƙungiyar ta Turin, rauni ne ya taƙaita wasannin da ya buga a kakar 2022-23, ya buga wasa biyu ne kacal a kakar bara gabanin a dakatar da shi saboda gwajin da aka yi masa.
Har yanzu Pogba na da sauran kwataragi da Juventus kuma za ta ƙare ne a ƙarshen kakar 2026, a kuma shirye yake ya koma atisaye tareda sauran abokan kwallonsa.











