Bincike ya gano Bobrisky ya yi zaman kurkuku, amma me ya sa aka sake kama shi?

Hoton Bobrisky ya shafa fankeke da kwalli a ido, da garin gashin ido, ya kuma yi shanfo a kai da rangada jan baki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An tanadar wa Bobrisky kayan alatu a dakinsa na kurkuku da suka hada da talbijin, da na'urar sanyaya daki da wayar tarho
    • Marubuci, Danai Nesta Kupemba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Kwamitin da ke bincike kan shahararren dan Daudun nan Idris Okineye, wanda aka fi sa ni da Bobrisky, ya yi watsi da zargin da aka yi cewa bai zauna a gidan yari ba a hukuncin da kotu ta yanke ma sa na wata shida a kurkuku.

An yi zargin Bobrisky bai zauna a kurkuku ba, maimakon haka ya zauna ne a wani kayataccen gida, kuma bai yi cikakken zaman hukuncin wata shida ba, kan laifin wulakanta takardar naira.

Rahotanni sun bayyana cewa, Idris Okuneye, dai ya samu zarafin ganin 'yan'uwa da abokan arziki da ke kai masa ziyara kurkuku, kuma an kayata masa dakin da kayan alatu da suka hada da gado, da talbijin, da na'urar sanyaya daki, da firji da kuma wayar salula.

Bobrisky ya fada komar jami'an tsaro ne bayan wani bikin nuna wasan kwaikwayo da aka yi a watan Afirilun 2024, inda ya dinga liƙa kudi babu kakkautawa. Sannan aka zarge shi da halasta kudin haram, amma daga bisani kotu ta yi watsi da wannan zargin.

Kwamitin da ma'aikatar cikin gida ta Najeriya ta kafa domin binciken ikirarin da wani fitacce a shafukan sada zumunta ya yi mai suna Martins Otse, da aka fi sa ni da VeryDarkMan, kan cewa jami'ai sun bukaci Bobrisky ya ba da cin hanci a wanke shi daga zargin halasta kudin haram, sai dai ya musanta hakan.

Wannan dambarwa ta janyo an dakatar da wasu manyan jami'an gidan kurkukun a watan da ya gabata.

Kwamitin ya ce ana bukatar gudanar da karin bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru na wadata Bobrisky da kayan alatu a zaman da ya yi a gidan yarin; haka siddan ya faru, ko da gaske cin hanci ya bayar kafin ya samu wannan jin dadin.

Sun kara da cewa Bobrisky ya take duk wasu dokokin da suka kafa kurkukun Najeriya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Liki ko watsa kudi sama ba bakon abu ba ne a Najeriya, ko dai a gidajen biki ko wasu shagulgula. Sai dai aikata hakan haramun ne karkashin dokokin babban bankin kasar CBN.

Ma fi kankantar hukuncin da za a yanke wa wanda aka samu da laifin hakan shi ne zaman kaso na wata shida, sai dai ba yanke hukunci makamancin wannan ba sai a shekarar nan.

Bayan sako shi a watan Agusta, wani bidiyo ya yi ta wadari a shafukan sada zumunta da aka ji muryar wani mutum na cewa Bobrisky ya bai wa jami'an gidan yari cin hancin dala 9,000 domin a cire zargin halasta kudin haram cikin zarge-zargen da ake masa, lamarin da ya janyo wannan bincike.

Akwai ikirarin ya kuma biya miliyoyin naira domin a kama masa gidan haya a kusa da kurkukun, inda ake zargin a nan ya yi zaman hukuncin da aka yanke masa maimakon ainahin kurkukun.

Sai dai Bobrisky, mai kusan mabiya miliyan biyar a Instagram, ya musanta cewa ba muryarsa aka ji a cikin bidiyon ba.

Ana tsaka da wannan danbarwa, sai kuma jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya suka ce sun kama Bobrisky yayin da yake kokarin tserewa daga kasar ta iyakar Najeriya da Benin.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Bobriksy ne a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga Najeriya a iyakar Seme, kuma tuni suka mika shi hannun jami'an tsaro domin gudanar da bincike.

Sai dai jaridar Punch ta ambato sashen binciken manyan laifuka na Najeriya reshen Alagbon da ke jihar Lagos na cewa Bobrisky ya kwana a hannunsu, kuma ya shafe daren Talata a wurin da ake tsare mata a ofishin.

Punch ta rawaito cewa majiya mai tushe daga ofishin ta ce an tsare shi a dakin mata ne saboda shigar da yake yi ta mata mai janyo cecekuce, kuma babu mace ko daya a dakin a lokacin da aka kai shi da misalin karfe 10:00 na daren Talata, dan haka shi kadai ya kwana a wurin.