Waiwaye: Zuwan Buhari da Obasanjo kotun Paris, da ƙarin kuɗin kiran waya
Wannan maƙala ce da kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Buhari da Obasanjo sun gabatar da shaida a kotun Paris

Asalin hoton, SCREEN SHOT/BBC YORUBA
A farkon makon nan ne tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin bayar da bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba.
Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa'idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 300 a matsayin diyya na asarar da aka janyo masa.
Obasanjo da Buhari sun bayar da shaida kan abin da ya sani dangane da wannan kwangila da aka bayar da ita a 2003, lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Hukumar sadarwa ta amince da ƙarin kuɗin kiran waya

Asalin hoton, Others
A farkon wannan makon ne kuma hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin kiran waya.
A cikin wata sanarwar da NCC ta fitar ranar Litinin, ɗauke da sa hannun kakakin hukumar, Reuben Mouka, ta ce an bayar da izinin ƙarin ne bisa ga ikon da take da shi a ƙarƙashin sashe na 108 na dokar sadarwar Najeriya ta 2003 (NCA), don daidaitawa da kuma amincewa da farashi da kuma cajin kuɗaɗen da kamfanonin sadarwa ke yi.
Sanarwar ta ce kamfanonin sadarwa sun miƙa wannan buƙata ce sakamakon yanayin da ake samu a kasuwa.
Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Asalin hoton, Operetion Fansan Yanma
Sojoji Najeriya da ke yaƙi da ƴanbindiga a arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun kashe wani babban mataimakin gawurtaccen ɗanbindigar nan da ke addabar yankin, Bello Turji, mai suna Aminu Kanawa.
A wata sanarwa da sojojin suka fitar ta ce dakarun dai "sun samu nasarar kashe Aminu Kanawa ne lokacin wani samame da suka kai a duwatsun Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi."
"Ɗanbindigar ya yi ƙaurin suna ne wajen addabar al'ummar ƙananan hukumomin jihar ta Zamfara da ma Sokoto da suka haɗa da Zurmi, Shinkafi, Isa da Sabon Birni."
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Lakurawa a matsayin ƴanta'adda

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis ɗin makon ne kuma gwamnatin Najeriya ta haramta ayyuka tare da ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ta ƴanta'adda.
Lakurawa ƙungiya ce ta ƴanbindiga da sunanta ya yi amo a bara, duk da cewa mazauna yankunan Sokoto da Zamfara da Kebbi da suke maƙwabtaka da Nijar sun ce sun daɗe suna shigowa jefi-jefi.
A takardar ƙara da gwamnatin ta shigar a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta zargi ƴan ƙungiyar da aikata ayyukan ta'addanci da sata da garkuwa da mutane da kai hare-hare kan jami'an tsaro da ma'aikatan gwamnati.
Ta kuma zargi ƴan ƙungiyar da gurɓata tunanin mutane, ta hanyar ba su shawarar yi gwamnati bore.
'Boko Haram ta ƙara kashe masunta a Borno'

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Laraba ne kuma rahotonni daga jihar Borno suka ce aƙalla masunta 20 ne ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun hallaka a harin da suka kai kan wani ƙauye da ke jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani jami'i na rundunar ƴan sa-kai ta Civilian Task Force, Modu Ari, na cewa ƴan bindigar sun far wa ƙauyen Gidan Gari inda suka buɗe wuta nan take, lamarin da ya yi ajalin aƙalla masunta 20.
Borno na daga cikin jihohin Najeriya da suka fi shan wahala a rikicin Boko Haram da ISWAP, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama da ɗaiɗaita al'umma.











