Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan matakin CBN na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa kullum

Na'urar cirar kuɗi ta ATM

Asalin hoton, Getty Images

'Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da sabon matakin da babban bankin ƙasar CBN ya ɗauka na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

A ranar Talata ne dai babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar.

A cikin sabbin dokokin, CBN ya ce daga ranar tara ga watan gobe yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

Haka kuma CBN ɗin ya ce yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na'urar cirar kuɗi ta ATM a sati shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a rana naira 20,000 ne kacal a na'uran ATM da kuma wajen masu amfani da POS.

Tun bayan fitar da sabbin dokokin 'yan ƙasar ke tofa albarkacin bakinsu, a yayin da wasu ke sukar matakin wasu kuma cewa suka yi suna maraba da matakin.

Haka kuma tun bayan da muka wallafa labarin a shafinmu na Facebook ranar Talata da yamma, zuwa ranar Laraba da safe mutum 26,000 ne suka so labarin, sannan kusan mutum dubu bakwai ne suka yi tsokaci game da labarin inda aka raba shi fiye da sau 1,000.

Ga ra'ayoyin wasu daga cikin masu bibiyar shafin namu:

.
,

A yayin da wasu ke sukar wannan mataki, a gefe guda kuma wasu maraba suke yi da sabon matakin da CBN ɗin ya ɗauka.

.
.

Asalin hoton, OTHER

Me masu sana'ar POS ke cewa?

.

Asalin hoton, Getty Images

Wasu mutanen kuma da wannan sabon mataki zai shafa su ne masu sana'ar cire kuɗi ta na'urar POS, waɗanda a cewarsu ke sauƙaƙa wa mutane shafe dogayen layuka a na'urar cirar kuɗi ta ATM.

Abdulganiyyu Muhummad wani mai sana'ar POS ne a ƙasar ya kuma shaida wa BBC cewa haƙiƙa wannnan mataki zai shafi duka masu sana'ar tasu.

''Akwai mai zuwa ya cire 200,000, ko 300,000 ko ma 500,000 a lokaci guda, kuma a kowacce 100,000 akan ba mu naira 500, to ka ga idan a ka ce a rana iya 20,000 kawai mutum zai cire to ka ga abin da zai ba mu bai fi 200 ba, to ka ga ai ya shafe mu sosai," in ji Abdulganiyyu.

Ya ƙara da cewa ba iya su kaɗai abin zai shafa ba har bankunan da suke hulɗa da su, da manyan 'yan kasuwa masu zuwa cire kuɗi masu yawa domin sarin kaya su ma abin zai shafe su.

Abin da masana ke gani

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Suma masana na ci gaba da tsokaci kan wannan batu, Farfesa Kabiru Isa Dandago wani masanin tattalin arziki ne a Najeriyar ya kuma shaida wa BBC cewa adadin ya yi kaɗan.

''Wannan tsari ne wanda ba shi da wani muhimmanci ga rayuwar al'umma, abu ne da za a takurawa mutane da dama wajen hada-hadarsu ta cinikayya''

''Na biyu kuma mutanen da suke da bankuna mutane ne da ke zaune a birane mutanen karkara ba su ma san menene ke guda na ba'', in ji ji.

Farfesan ya ƙara da cewa duk da cewa matakin na da fa'ida ta rage yawan hada-hadar da takarkar kuɗi a hannu, tare da komawa amfani da hada-hadar kuɗi ta banki.

To amma ya ce mutanen da suke da dama hada-hadar banki a ƙasar ba su kai yawan da ake buƙata ba.

''In dai kuɗi bai zo hannun mutane ba to hada-hada ma ba za ta yi wa ba, yayin da kuwa aka tsaurara, to su waɗanda suke da halin da ke sa ran za su riƙa bayar da gudunmowa ga waɗanda ke ƙasa-ƙasa marasa ƙarfin tattalin arziki, sai ka ga ƙuncin ya daɗa yi wa mutane yawa''.

A wani jawabi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi a lokacin ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin ƙasar ranar 23 ga watan Nuwamba ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar.