Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda likitocin kasar waje ke fadawa halin da ka iya cutar da marasa lafiya yayin aiki a Birtaniya
Wasu likitoci da aka dauka aiki daga kasashe marasa galihu zuwa asibitocin Birtaniya sun ce ana bautar da su - kuma sun ce ana sa su yin aiki da ya zarce kima, lamarin da ka iya sa su fada cikin matsalar rasa kulawa da marasa lafiya kamar yadda ya kamata.
Wani binciken BBC ya gano yadda wani kamfanin Birtaniya ke daukar likitoci aiki daga Najeriya kuma ana sa su yi aiki a wasu asibitoci masu zaman kansu a wani yanayi da hukumar NHS mai kula da harkokin kiwon lafiya ta Birtaniya ba ta amince da shi ba.
Kungiyar likitoci ta Birtaniya, BMA ta kira halin da likitocin ke ciki "abin takaici" kuma ta bukaci a mayar da wannan sashen karkashin kulawar hukumar ta NHS.
BBC ta tattauna da wasu likitoci 'yan kasar waje, ciki har da wani likita daga Najeriya wanda ya taba yin aiki a asibitin Nuffield Health Leeds a 2021.
Augustine Enekwechi ya ce yakan yi aiki na lokaci mai tsawo a kullum - yana yin aiki na tsawon sa'a 24 a kullum na tsawon mako guda a jere - har ba ya iya barin harabar asibitin.
Ya ce yin aiki a asibitin ya kasance tamkar yana cikin "kurkuku" ne.
Gajiyar da yake ji mai tsanani ce, in ji shi, har a wasu lokutan ya rika tunanin cewa ba zai iya yin aiki ba samsam.
"Na san cewa yin aiki a yanayin gajiya na iya saka lafiyar wadanda nake dubawa cikin mummunan hali kuma ina iya fada wa cikin matsalar da za a kai ni kara kotu," in ji shi.
"Ba ni da ikon yin komai... na kasa kawai, saboda matsananciya damuwa kan abin da ka iya zama matsalar a gare ni."
Sai dai Nuffield Health ya musanta cewa yana tilasta wa likitocin yin aiki na lokuta masu tsawo, kuma yace yana ba su isasshen hutu, har ma da damar sauya lokutan aikinsu da wasu likiocin idan suna so.
Kamfanin NES Healthcare mai zaman kansa ne ya dauki Augustine aiki kuma ya tura shi asibitin na Nuffield health aiki.
NES Healthcare ya yi fice wajen dauko likitoci daga kasashen waje yawancinsu daga Najeriya, inda yake amfani da su a matsayin likitocin da ke aiki da zama a ckin asibitoci wato Resident Medical Officers a turancin Ingilishi.
Augustine ya ce saboda murnar da yayi ta samun aiki, shi ya sa bai mayar da hankalinsa kan takardun daukar aikin da aka ba shi ya sanya hannu a kai ba.
A takaice takardar daukar aikin ta dora shi bisa wani tsari mai wahalarwa - kuma mafi muhimmanci ma shi ne ba shi da kariya daga dokokin Birtaniya da ke kare hakkokin ma'aikata daga yin aiki mai cutar da su - har ta kai ga yana iya rasa wani bangare na albashinsa idan ya yi kuskure a aikinsa.
Ba Augustine ne kawai ke fuskantar wannan matsalar ba. Kungiyar likitoci ta Birtaniya, BMA da wata kungiyar mai fafutukar kare hakkin likitoci sun ba shirin BBC File on 4 da na BBC Newsnight dama ta musamman ta ganin sakamakon wasu tambayoyi da aka yi wa likitoci 188.
Kamfanin NES ne ya dauki yawancin likitocin aiki sai dai akwai wadanda wasu kamfanoni na daban ne suka dauke su aiki.
Sakamakon ya gano cewa kashi 92 cikin 100 na likitocin daga Afirka aka dauko su kuma yawancinsu - kashi 81 cikin 100 - daga Najeriya suke.
Kuma yawancin likitocin sun koka kan tarin aikin da ake ba su da yawan kudaden da ake cire wa daga albashinsu.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta dade tana gargadin kasashe da su kauce wa tsarin raba kasashe mas tasowa da 'yan likitocin da suke da su.
Hukumar ta tara sunayen kasashe 47 - wadanda yawanci na nahiyar Afirka ne.
Ita ma Birtaniya na da irin wannan tsarin, wanda a takaice ya saka Najeriya cikin kasashe masu tasowa da aka haramta daukan likitoci daga can.
Tambaya a nan ita ce - ta wace hanya wadannan likitocin suka sami damar yi aiki a Birtaniya ma tun da farko?
BBC ta tafi Najeriya, inda ta gano wani abin takaici kan wannan badakalar.
Mun ziyarci wani dakin da ake shirya jarabawa a Legas, babban birnin kasuwancin kasar, inda ta gano daruruwan likitoci sun yi layi suna shirin rubuta wata jarabawa da ake kira da turancin Ingilishi Professional and Linguistic Assessments Board - wato PLAB 1.
Mun kuma gano cewa hukumar da ke kula da kiwo lafiya ta Birtaniya da ke Landan ce keshirya wannan jarabawar wanda shi ne matakin farko da gwmatin Birtaniya ke bukata mutum ya cika idan yana sha'awar samu damar yin aiki a Birtaniya.
Likitocin da muka tattauna da su sun ce fatan samun albashi mai tsoka ne ya ja hankulansu da kuma damar yain aiki a wuraren da suka fi na gida Najeriya tsari.
Sannan ma'aikata daga ofishin gwamnatin Birtaniya na British Council ne ke sa ido kan wannan jarrabawar - wanda ofishi ne da ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ke daukar nauyin ayyukansa.
Hukumar GMC na shirya irin wannan jarabawar a kasashen da ke cikin jerin kasashen da ke fuskantar karancin likitoci - kamar Ghana da Sudan da Pakistan da kuma Bangladesh.
Hukumar GMC da British Concil sun ce ba su da hannu cikin daukar likitocin "kai tsaye", amma wai "suna taimaka" wa dukkan likitan da ke son zuwa Birtaniya a matsayinsa na mutum ba a kungiyance ba.
Mun tattauna da likitoci 'yan Afirka masu yawa da NES ya dauke su aiki ta wannan hanyar. Dukkansu sun bayyana mana cewa an gindaya mu su dokoki masu tsauri a kwantiragin da aka dauke su aiki - wadda ta fayyace irin aikin da za su yi da zarar an tura su zuwa asiitocin Birtaniya masu zaman kansu domin su kama aiki.
An tura likita Femi Johnson zuwa asibiti na daban da aka tura Augustine, amma ya ce an sa shi aiki na tsawon sa'a 14 zuwa 16 a kullum sannan ya kan kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kowane dare.
"Na kasance gajiyayye baki daya" inji shi. "A gajiye nake, Ina bukatar barci. Babu yadda mutum zai iya yin aikin likita a kullum na tsawon kwana bakwai."
Sannan idan gajiyar ta kai wani maysayin da dole ya huta, NES na da damar ta yanke wani bangare na albashinsa.
Kamfanin ya ce yana zaftare albashin likitocin ne domin ya sami na biyan likitan da zai karbi aiki daga hannun wanda ya tafi hutu.
Wasu likitocin na NES sun sami taimako daga Likita Jenny Vaughan ta kungiyar Doctor's Association.
Ta kan karbi koke mai yawa daga likitoci kamar Augustine kuma ta ce tsarin kiwon lafiya na Birtaniya ya rabu gida biyu - daya na likitocin da ke aki a karkashin kulawar ukumar NHS ta gwamnatin Birtaniya, dayan kuma na likitocin da aka dauko su aiki daga kasashen waje da ke aiki a asibitoci masu zaman kansu.
Likitocin NHS na yin aikin da bai zarce sa'o'i 48 ba, amam idan sun bukaci kari, ba sa zarce sa'a'i 72 a kowane mako.
"Babu likitan da ke aikin kwana da ya wuce kwanaki hudu a jere saboda mun sa yin haka na tattare da hadari", inji Likita Vaughan.
"Wannan aikin ya yi kama da na bauta da ke da sa'o'i masu yawa, irin wanda muke zaton an kawar da shi shekaru 30 da suka gabata."
"Bai dace yanayin ya kasance ga marasa lafiya ba, haka kuma bai dace likitoci ma su sai kansu cikin wannan mawuyacin halin ba."
Mun tura wa kungiyar likitocin Birtaniya BMA sakamakon bincikenmu - da kuma ga mataimakiyar kungiyar Emma Runswick.
Ta shaida mana cewa "wannan tsarin abin kunya ne ga tsarin kiwon lafiya na Birtaniya."
Ta ce "abokan aikinmu daga kasashen waje sun yi tafiya mai nisa zuwa nan Birtaniya, inda suka ci karo da tsari mai cutarwa har ya kai ga hankali ma ba ya iya daukarsa."