Yadda sojoji suka taka wa Nyesom Wike burki a Abuja

Asalin hoton, X/Lere Olayinka
An samu wata hatsaniya tsakanin ministan Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Nyesom Wike da jami'an sojin Najeriya bayan da sojojin suka hana ministan shiga wani fili.
Rikicin ya fara ne a lokacin da ministan ya yi tattaki da kansa zuwa filin, wanda tuni aka jibge sojoji a wurin.
Nyesom Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers, mai arziƙin man fetur ne, yana daga cikin ministocin da ake yi wa kallon masu ƙarfin iko a gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu.
An ga yadda Wike ya fusata a lokacin da jagoran sojojin ya dakatar da shi, tare da tabbatar masa cewa ba za a bari ya shiga filin ba.
Ministan ya ƙalubalanci sojojin kan su gabatar da takardun filin da na izinin gini.
Sai dai jami'in sojan ya tsaya cikin tsanaki a gaban ministan yana ba shi amsa kan duk wata tambaya da ya yi.
"Ku nuna min takardun da kuke da su, ba ku da takardu. Ni minista ne, ba za ka faɗa min wata magana ba. Babu yadda za a yi mu ci gaba da irin wannan danniya, ba zai yiwu a ci gaba a haka ba."
"Ina takardun naku, me ya sa mutumin da ya kai wannan matsayin, idan ma yana da wata matsala ba zai rubuto min ba, sai ya turo sojoji suna yi wa mutane barazana, wa za a yi wa barazana."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A nasu ɓangaren sojojin sun ce suna bin umarnin da shugabanninsu suka ba su ne.
Nyesom Wike ya fusata, inda ya riƙa tsawa a gaban sojan, yana cewa babu wanda ya fi ƙarfin gwamnati, kuma babu wanda za a yi wa barazana.
"Ba ku isa ku ce kun fi ƙarfin gwamnati ba, ba zai yiwu ku ɗauki bindiga kuna yi wa mutane barazana don kada su yi aikinsu ba," kamar yadda Wike ya riƙa furta wa sojojin yayin da suka hana shi shiga filin.
Jagoran sojojin ya bayyana wa Wike cewa suna da takardum filin kuma an same su ne a kan doka, sai dai Wike bai nuna gamsuwa ba.
Yayin da lamarin ya yi zafi, Wike da sojan sun riƙa musayar zafafan kalamai, sai dai yayin da za a iya ganin cewa Wike ya fusata, shi kuwa sojan ya kasance a natse yana mayar wa Wike da amsa, inda yake sake jaddada cewa suna bin umarnin da aka ba su ne.
''Akwai takardun filin nan da aka samu bisa doka. Ni jami'in tsaro ne mai ƙima. Ba zan yi shiru ba, ba ka isa ka sa na yi shiru ba,'' in ji sojan.
Yayin da gardama ta ƙara yin zafi, ministan ya kira sojan a matsayin 'wawa', a lokacin ne sojan ya amsa a fusace cewa shi ba wawa ba ne.
''Ka yi min shiru, kai wawa ne. Lokacin da na gama makaranta kai kana firamare," kamar yadda Wike ya faɗa wa sojan.
''Oga ni ba wawa ba ne. Ina bin umarni ne," kamar yadda sojan ya mayar wa Wike da martani.
Mene ne ya haifar da hatsaniyar?
Bayan kammala musayar yawu, ministan Abuja Nyesom Wike ya yi wa ƴan jarida ƙarin bayani kan abin da ya kai shi domin duba filin.
Wike ya shaida wa manema labarai cewa filin na ƙarƙashin kulawar hukumar Abuja ne, inda suka samu labarin cewa sojoji sun kori jami'an da ke wurin, a dalilin haka ne ya sanya ya je domin ganin abin da ke faruwa da kansa.
''Wannan abin takaici ne, irin haka ne ke hana mu ci gaba. Sashen kula da filaye na da ƴancin duba wuraren da ake gini ba bisa ƙa'ida ba, da kuma inda ake mamaye filaye."
Lokacin da jami'ai suka zo, sun ce sojoji sun kore su, na yi tunanin cewa sun yi hakan ne ba bisa ƙa'ida ba. Lokacin da suka kira ni ina ofis sai na ce bari na zo na gani da kaina."
Wike ya ce ya buƙace su su nuna masa takardun filin da kuma takardar amincewa a yi gini a filin, "to amma ba su da shi".
''Kun ji abin da sojan ya faɗa, ya ce tsohon hafsan sojin ruwa ne ya turo shi. Na gaza fahimtar yadda mutum mai matsayi irin wannan zai samu matsala, kuma ya kasa zuwa ofishina. Wannan shi ne abin da ke faruwa," in ji Wike.











