Kotu ta wanke mutumin da aka zarga da cin hancin dala 8 bayan shekara 39

    • Marubuci, Alok Putul
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hindi
    • Aiko rahoto daga, Raipur
  • Lokacin karatu: Minti 5

Jageshwar Prasad Avadhiya tsoho ne mai shekara 84 da ke zaune a birnin Raipur na India, wanda a kwanan nan aka sako shi daga kurkuku, a shari'ar da aka yi ta yi tsawon shekara 39 kan karɓar cin hanci na dala takwas.

An kama Mista Avadhiya ne wanda ke aiki a matsayin akawu a kamfanin sufuri na gwamnatin jihar Madhya Pradesh da ke tsakiyar ƙasar a shekrarar 1986 a kan zargin karɓar cin hanci na rupee 100 kwatankwacin dalar Amurka takwas.

Za ka ga kuɗin da ya karɓa ba wani mai yawa ba ne - da ya taka kara ya karya, to amma fa ya janyo masa babbar asara.

Bayan zaman da ya yi na shekaru kullum cikin fargabar tura shi gidan sarƙa, a ƙarshe dai an wanke shi a watan Oktoba na wannan shekara, to amma ba ya cikin wani yanayi da zai yi murnar wanke shin da aka yi.

"Wannan abin da aka yi min ba shi da wani amfani a gareni yanzu. Saboda na rasa aikina. Al'umma sun juya min baya. Ba zan iya ilmantar da 'ya'yana ba. Ba zan iya yi musu aure ba. 'Yan'uwa sun yanke alaka da ni.Matata ta rasu saboda rashin kula da ita da ba ta da lafiya. Akwai wanda zai iya dawo min da duka waɗannan abubuwan?"

Harkar shari'a a Indiya tana da sarƙaƙiya sosai da jinkiri. Ministan shari'a na ƙasar ya taɓa gaya wa majalisar dokokin ƙasar cewa akwai shari'u miliyan 52 da ke zaman jiran a kammala a faɗin ƙasar.

Takardun kotu sun nuna cewa jami'an yaƙi da cin hanci sun kama shi ne bisa zargin karɓar cin hanci a ɓangaren biyan kuɗi na kamfanin sufurin da yake aiki.

Mista Avadhiya ya ce : "Wani ma'aikaci ne ya neme ni da in shirya masa takardar biyan kuɗin da ake binshi."

"Sai na ce masa fayil ɗin zai zo wajena ne kawai, idan wani babban jami'i na gaba da ni ya bayar da umarnin hakan a rubuce, sai an yi hakan ne zan iya shirya takardar biyan bashin. Daga na sai wannan ma'aikaci ya yi ƙoƙarin ba ni cin hanci na rupee 20. Sai na nuna ɓacin raina na ce masa kar ya sake zuwa ofishin."

Ya ce wannan abin da ya yi na ƙin yarda, ashe ya ɓata wa mutumin rai, 'yan kwanaki bayan abin, " a lokacin da nake barin ofis sai wannan ma'aikaci ya biyo ni ta baya ya sa min wani abu a aljihuna".

Kafin ya farga da abin da ya faru sai kawai wasu 'yansanda cikin farin-kaya suka kama shi, suka ce suna zarginsa da karɓar cin hanci.

Jinkirin shari'a

Mista Avadhiya ya ce wannan rana ita ce farkon samun kansa cikin doguwar fafutuka ta neman adalci, da kuma hukunci ba a kan shi kaɗai ba har ma da iyalinsa gabaɗaya.

Ba a tuhume shi ba har tsawon ƙarin shekara biyu sai a 1988, kuma an dakatar da shi daga aiki daga 1988 zuwa 1994.

Daga nan sai aka ɗauke daga Raipur zuwa Rewa, mai nisan kilomita 460 a arewa, nesa da matarsa da 'ya'yansa huɗu, kuma aka rage albashinsa zuwa rabi.

Ya ce a tsawon wannan lokaci, ba wani ƙarin girma ko ƙarin albashi da aka yi masa.

Ɗaya bayan ɗaya 'ya'yansa suka riƙa ficewa daga makaranta saboda ba mai iya ɗaukan nauyinsu.

Ƙaramin ɗansa, Neeraj, wanda a lokacin yana shekara 13, kuma yanzu shekararsa 52, ya ce da wannan abin da aka yi wa mahaifinsa an hana shi cin moriyar ƙuruciyarsa.

"Ban ma san mene ne cin hanci ba a lokacin, amma mutane za su kalle ni su ce min, ''ai ɗan mai cin hanci ne ,'" ya gaya wa BBC.

Yana share hawaye, ya ce: "Yara suna tsokanata. Ba wanda yake abokantaka da ni a makaranta, maƙwabta da dangi duk sun yi watsi da mu. An kore ni daga makaranta sau da dama saboda gaza biyan kuɗin makaranta."

Cin hanci da rashawa a harkokin gwamnati abu ne da ya zama ruwan dare a India:

Dole mutane su bayar da cin hanci don a haɗa musu wutar lantarki da yi musu takardar shedar haihuwa da kuma samun aikin gwamnati.

Duk da haka ba kasafai ake hukunta jami'ai da 'yansiyasa a kan karɓar rashawa.

Ita ma matar Mista Avadhiya, Indu, ta ɗanɗani aƙubar halin da mijin nata ya samu kansa, daga al'umma, abin da ya kai a ƙarshe ta rasu a sanadiyyar ciwon zuciya a1997.

"Matata ta rasu saboda damuwa," ya ce. "Ta samu kanta cikin damuwa tsawon lokaci saboda zargin cin hancin da ake min da kuma dakatar da ni da aka yi daga aiki, kuma a ƙarshe wannan hali ya kwantar da ita.

Ba ni isasshen kuɗin da zan yi mata magani. Na tuni ranar da ta mutu, ba ni da ko da kuɗin da za a yi jana'izarta. Wani abokina ne ya ba ni rupee 3,000 , daga nan ne na samu aka yi mata jana'iza."

Gwagwarmayar kare kai

A 2004, kotu ta samu Mista Avadhiya da laifi kuma ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya da tarar rupee 1,000, duk da cewa dukkanin shedu sun janye bayanan da suka bayar.

Ya je babbar kotun jihar Chhattisgarh, inda ya shigar da ƙara ya kuma yi nasara aka ɗage tuhumar saboda haka ba za a ɗaure shi ba , amma kuma an ci gaba da jan shari'ar.

Domin kula da iyalinsa, ya riƙa yin ayyuka daban-daban, wani lokaci ya yi direba. Duk da tsufansa sai ya yi aiki tsawon sa'a takwas zuwa goma a rana.

Wannan shari'a ta rupee 100 ta jefa shi cikin fargaba tsawon kwana 14,000.

Babbar kotun ta duba shari'ar daga 2004 zuwa 2025, kuma a tsawon wannan lokaci ta yi nazari a kan shedun da aka gabatar, ta saurari bahasi daga shedu da kuma kowa ne ɓangare na shari'ar.

A 2025, kotun ta wanke Mista Avadhiya daga tuhumar, inda ta ce masu gabatar da ƙara ba su iya tabbatar da laifin ba a kansa.

Mista Avadhiya, ya ce : ''An yi adalci, amma ba za a iya dawo da lokaci ba. Matata ba za ta dawo ba, ƙuruciyaar yara ba za ta dawo ba."

Yanzu dai lauyoyi na duba yuwuwar yadda za a biya shi diyya.

Mista Avadhiya na son gwamnati ta biya shi fansho da albashin da aka yanke masa, amma kuma ya ce ba ya son ya ja wata rigimar.