Fararen dawaki da mata a bakin teku cikin hotunan Afirka

Wani mahayin doki a ƙauyen Beni Arous da ke ƙasar Morocco na shirya dawakinsa domin gasar sukuwa ta gargajiya a lardin Laranche a ranar Juma'a.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mahayin doki a ƙauyen Beni Arous da ke ƙasar Morocco na shirya dawakinsa domin gasar sukuwa ta gargajiya a lardin Laranche a ranar Juma'a.
A ranar Juma'a wani mutum na lilo a wani bikin al'adu a ƙasar Tunisia.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Juma'a wani mutum na lilo a wani bikin al'adu a ƙasar Tunisia.
Ɗan ƙasar Kamaru, Emmanual Eseme ya yi mamakin nasarar da ya samu a gasar tseren mita 100 a Morocco.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ɗan ƙasar Kamaru, Emmanual Eseme ya yi mamakin nasarar da ya samu a gasar tseren mita 100 a Morocco.
Ƴar ƙasar Senegal, Saly Sarr a gasar tsalle-tsalle ta Seiko Golden Grand Prix a Tokyo, Japan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ƴar ƙasar Senegal, Saly Sarr a gasar tsalle-tsalle ta Seiko Golden Grand Prix a Tokyo, Japan.
Yadda mutane suka yi dandazo a lokacin da aka rantsar da Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban ƙasar Chadi a ranar Alhamis inda ƙasar za ta koma tsari na mulkin demokuraɗiyya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda mutane suka yi dandazo a lokacin da aka rantsar da Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban ƙasar Chadi a ranar Alhamis inda ƙasar za ta koma tsari na mulkin demokuraɗiyya.
Wani mutum a Afirka ta Kudu da ke neman aiki yayin da ƙasar ke fama da matsalar tattalin arziƙi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum a Afirka ta Kudu da ke neman aiki yayin da ƙasar ke fama da matsalar tattalin arziƙi.
Sojojin ƙasar Kamaru lokacin da suke maci a bikin cikar ƙasar shekara 52 da samun ƴancin kai a birnin Yaounde.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojojin ƙasar Kamaru lokacin da suke maci a bikin cikar ƙasar shekara 52 da samun ƴancin kai a birnin Yaounde.
A ranar Asabar, wasu mata biyu na tafiya a gefen teku da ake kira Yoff Beach a Dakar, babban birnin ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar, wasu mata biyu na tafiya a gefen teku da ake kira Yoff Beach a Dakar, babban birnin ƙasar Senegal.