Crystal Palace na son rike Eze, Guimaraes na farin ciki a Newcastle

Eze

Asalin hoton, Getty Images

An sanya farashin kan sai da dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Crystal Palace, Eberechi Eze, kan fam miliyan 60, a daidai lokacin da kungiyar Tottenham ke cikin masu son dan wasan. (Mail)

Dole Aston Villa ta samar da fam miliyan 60 na sayar da 'yan wasa a kakar wasan nan domin kaucewa take dokokin dorewa. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, ya ce ya na cike da farin ciki a kungiyar da ya ke takawa leda wato Newcastle, a daidai lokacin da kungiyoyin Arsenal da Manchester United ke zawarcin dan wasan. (Mirror)

Tsohon shugaban Chelsea Frank Lampard, mai shekara 45, na son komawa kungiyar, a bangare guda kuma ya yi watsi da tayin da wasu kungiyoyi ke masa na aiki da shi. (Talksport)

Dan wasan baya na Scotland mai taka leda a Arsenal Kieran Tierney, zai so komawa tsohuwar kungiyar Celtic, yayin da kungiyar ta fara tattaunawa kan tayin da ake yi kan dan wasan mai shekara 27. (Football Insider)

Manchester City na son dan wasan Ingila da Crystal Palace Adam Wharton, kan kwantiragi mai tsawo, kodayake ba a sa ran za su yi wani abu kan dan wasan mai shekara 20 a wannan kakar. (Standard)

Wolves na son dan wasan Portugal Rodrigo Gomes, daga Braga, yayin da ita ma kungiyar Atletico Madrid ke son dan wasan. (Express and Star)

An fara tattaunawa tsakanin Mainz da Liverpool, kan dan wasan baya na Denmark mai shekara 22 Sepp van den Berg. (Sky Germany)

Ta yi wu Liverpool za ta rasa wani mai tsaron ragar a kakar nan, sakamakon nuna son dan wasan da kungiyoyin Celtic da Brentford ke yi kan Caoimhin. (Liverpool Echo)

Tottenham da Bayern Munich na son daukar dan wasan Stuttgart da Jamus Chris Fuhrich mai shekara 26. (BILD)

Real Sociedad ta fara tattaunawa kan dan wasan Sifaniya Sergio Gomez, mai shekara 26 daga Manchester City. (Fabrizio Romano)