Jerin shugabannin da aka gayyata wurin jana'izar Sarauniya Elizabeth II - da wadanda ba a gayyata ba

Jana'izar da za a yi ta Sarauniya Elizabeth II ranar Litinin za ta kasance daya daga cikin manyan taruka da aka hada sarakuna da 'yan siyasa a Birtaniya a cikin shekaru aru-aru.

A karshen makon jiya ne aka aika da takardun gayyatar zuwa jana'izar ga shugabanni da sarakuna da sauran manyan mutane a fadin duniya, inda ake sa ran shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 za su halarce ta.

An shaida wa galibin shugabannin cewa su halarci jana'izar a jiragen sama na fasinja inda kuma aka gaya musu cewa za a dauke su a motocin bas daga filin jiragen saman zuwa yammacin London.

Za a yi taron jana'izar ne a babban dakin Westminster Abbey, wanda zai iya daukar kusan mutum 2,200.

Ga abubuwan da muka sani game da mutanen da za su halarci jana'izar da wadanda ba za su je ba.

Iyalan Gidan Sarautar Turai

Sarakunan kasashen Turai, wadanda da dama daga cikinsu suna da alaka ta jini da Sarauniyar Ingila, na cikin wadanda ake sa ran za su halarci jana'izarta.

Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde sun tabbatar da cewa za su halarci jana'izar, yayin da shi ma Sarki Willem-Alexander da matarsa, Sarauniya Maxima, tare da mahaifiyarsa, tsohuwar sarauniyar Dutch Gimbiya Beatrix za su halarci jana'izar.

Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya sun amince su halarci jana'izar, kuma su ma iyalan gidan sarautar Norway, Sweden, da Demark ake sa ran za su je wurin jana'izar.

Shugabannin Amurka

Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaba Joe Biden tare da mai dakinsa Jill Biden za su halarci jana'izar, ko da yake an fahimci cewa ba sa cikin wadanda za a dauka a motocin bas.

Ana ta tattaunawa kan ko Shugaba Biden zai gayyaci mutumin da ya gabace shi, Donald Trump, domin shiga tawagar Amurka da za ta halarci jana'izar, sai dai da alama tsofaffin shugabannin kasar ba za su iya halartar jana'izar ba saboda adadin mutanen da aka ware wa Amurka ta tafi da su ba shi da yawa.

Ana ta rade radin cewa wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kasar da matansu - musamman Obama - sun samu katin gayyatar zuwa jana'izar.

Jimmy Carter, wanda ya yi shugabancin kasar daga 1977 zuwa 1981, bai samu katin gayyata ba, kamar yadda ofishinsa ya shaida wa jaridar Politico.

Shugabannin kasashen kungiyar Commonwealth

Ana sa rai shugabannin kasashen kungiyar Commonwealth, wadda Sarauniya ta shugabanta, za su halarci jana'izarta.

Firaiministan Australia Anthony Albanese ya ce zai amsa gayyatar, haka kuma Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern da takwaranta na Canada Justin Trudeau.

Su ma masu rike da mukaman gwamna janar wadanda suka taka rawa a matsayin wakilan Sarauniya a kasashen Commonwealth ana sa ran za su halarci jana'izar.

Rahotanni sun ce dadaddiyar Firaministar Bangladash Sheikh Hasina da shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe sun amince su halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth II.

Sai dai ya zuwa wannan lokaci babu tabbataci kan ko Firaiministan India Narendra Modi zai halarci jana'izar.

Sauran shugabannin kasashen duniya

Sauran shugabannin kasashen duniya da aka ce sun amsa gayyatar halartar jana'izar sun hada da Firaiministan Ireland Micheal Martin, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, da takwaransa na Italiya Sergio Mattarella da kuma shugabar majalisar tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Kazalika shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-Yeol da na Brazil Jair Bolsonaro sun tabbatar da cewa za su je wurin jana'izar.

Haka kuma ana sa ran Basaraken Japan Naruhito, da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron za su halarci jana'izar.

Ba a sani ba kawo yanzu ko shugaban kasar China Xi Jinping, wanda ziyarar aikin da zai kai Kazakhstan da Uzbekistan a wannan makon za ta zama karon farko da ya bar kasar tun bayan barkewar annobar korona, ya samu gayyata ko kuma zai halarci jana'izar.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda aka dade da sanya mata takunkumai kan shirinta na kera makamin nukiliya, za ta tura wakilai, a cewar majijoyi na Whitehall.

Shugabannin da ba a gayyata ba

Ba a gayyaci wakilan Rasha, Belarus, da Myanmar zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth ba, a cewar wakilin BBC James Landale.

Dangantakar difilomasiyya tsakanin Birtaniya da Rasha ta yi matukar tsami tun bayan da ta kaddamar da yaki a Ukraine, kuma a makon jiya kakakin Vladimir Putin ya ce "ba shi da niyyar" halartar jana'izar.

An kaddamar da mamayar ne daga wani bangare na kasar Belarus, wadda shugabanta, Aleksandr Lukashenko, aboki ne kut da kut na Shugaba Putin.

Kazalika Birtaniya ta janye harkokin difilomasiyyarta da dama daga Myanmar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Fabrairun 2021.