Shugaban ƙasa tsohon fursuna da ke bai wa matasan Afirka ƙwarin gwiwa

Fayesupporters

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An yi ta shagulgula a babban birnin Dakar, lokacin da sakamakon farko-farko ya nuna cewa Bassirou Diomaye Faye na kan gaba
    • Marubuci, Daga Leonard Mbulle-Nziege da Nic Cheeseman , masu sharhi kan Afirka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .

Manyan sauye-sauyen siyasa ƙalilan ne za su iya kamo abin da ya faru cikin watan jiya a Senegal.

Kimanin mako biyu, Bassirou Diomaye Faye, jagoran adawa wanda ba kowa ne ya san shi ba, yana can gidan kurkuku, inda aka tsare shi ba tare da shari'a ba a kan tuhume-tuhumen da suka haɗar da ingiza yi wa gwamnati bore, duk da yake bai taɓa riƙe wani muƙamin siyasa ba.

Sai dai a makon da ya wuce, ya kayar da ɗan takarar jam'iyya mai mulki, Amadou Ba a zaɓen shugaban ƙasa, inda ya samu kashi 54% na ƙuri'un da aka kaɗa a zagayen farko.

A ranar Talata ne, ake rantsar da matashin ɗan shekara 44 a matsayin shugaban ƙasar Senegal na biyar, inda zai zamo shugaban wata ƙasa a Afirka mafi ƙarancin shekaru.

A yankin da gagarumin kaso mafi yawa na al'ummarsa 'yan ƙasa da shekara 30 ne, nasarar Bassirou Faye, na ba da wani kyakkyawan fata ga matasan da suka fusata saboda rashin damammakin tattalin arziƙi, yayin da ake ganin manyan gari masu nisan shekaru suna maƙalewa a kan mulki.

Gagarumin tashen Mallam Faye, wata muhimmiyar matashiya ce cewa zaɓuka har yanzu su ne hanya mafi dacewa wajen cire gwamnatin da ta gaza a idon ɗumbin al'ummar Afirka.

Nasararsa ba kawai ta janyo cire gwamnatin da ba ta da farin jini daga mulki ba ne, ta kuma ƙarfafa turakun dimokraɗiyyar ƙasar tare da sake farfaɗo da ƙwarin gwiwar jama'a a kan tsarin dimokraɗiyya a lokacin da juye-juyen mulki a wasu ƙasashen Afirka ta Yamma ya yi saɓanin haka.

Labarin nasarar Bassirou Faye za kuma ta zaburar da sauran shugabanni a faɗin nahiyar, wadda ta yi fama da ƙaruwar danniya tsawon shekaru da razanarwa da kuma yi wa al'umma takunkumi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar tsohon jagoran adawa na ƙasar Uganda, Kizza Besigye, wanda a baya-bayan nan ya yi aiki da takwaransa matashi Bobi Wine wajen yaƙin neman tabbatar da dimokraɗiyya a ƙasar, "tsarin zaɓen Senegal da ya yi fintinkau ya sake nuna cewa abu ne mai yiwuwa a samu sauyin dimokraɗiyya da ake buƙata ba tare da an yi amfani da tarzoma ba a Afirka, ta hanyar tsararren gangami na tsayin daka da kyakkyawan jagorancin al'umma".

Tasirin zaburarwa ta nasarar Mallam Faye za ta ƙara fito da gaskiyar cewa matakin bai zo da sauƙi ba.

Gabanin zaɓen, gwamnatin Shugaba Macky Sall ta ɓullo da matakan kashe dimokraɗiyya a wani abu da ake gani a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙari da kuma ƙanƙame mulki a daidai lokacin da take fuskantar ƙaruwar baƙin jini.

Wannan ya haɗar da musgunawa shugabannin adawa babu ƙaƙƙautawa da masu sukar gwamnati, sai kuma yunƙurin ƙarshe na jinkirin gudanar da zaɓuka a wani ƙuduri ido rufe na kauce wa shan kaye, abin da ya janyo har wasu masharhanta ke tambayar ko mun riƙa hango mafarin mutuwar dimokraɗiyyar Senegal.

Da yawan waɗannan matakai,an ɗauke su ne da nufin dakushe karsashin da jam'iyyar adawa mai farin jini ta Pastef ke da shi.

President Faye

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Mallam Faye (a hagu) da Ousmane Sonko (a dama) yanzu za su yi aiki tare don cika alƙawurran zaɓe da suka ɗauka

Wannan ya ƙunshi tsare jagoran jam'iyyar mai farin jini Ousmane Sonko da Mallam Faye, wanda shi ne babban sakataren jam'iyyar Pastef. Akwai kuma gagarumin razanar da magoya bayan jam'iyyar.

Tsare Mallam Sonko a gidan yari bisa zargin aikata masha'a da wata matashiya 'yar ƙasa da shekara 21 bayan zarge-zargen wata mai sana'ar tausa - tare da wasu matakai na tunzurawa, sun harzuƙa jerin zanga-zanga mafi girma da Senegal ta gani a shekarun baya-bayan nan. Sakamakon haka, tsattsauran matakin jami'an tsaro ya kai ga mutuwar mutane da dama.

Ousmane Sonko ya bayyana tuhume-tuhumen a matsayin ƙage da nufin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Ita da kanta jam'iyyar Pastef, sai da hukumomi suka rusa ta a bara, bayan an zarge ta da ingiza tarzoma a ƙasar - amma shugabancinta ya ci gaba da gudanar da aikace-aikacensa.

An samu wata jarumta ta ban mamaki da aiki tuƙuru daga shugabannin adawar da ƙungiyoyin fararen hula da 'yan jarida da kuma waɗanda ke aiki a wasu cibiyoyin kare dimokraɗiyyar ƙasar, wajen ganin wannan baƙin yanayi ya ƙare da zaɓen da Mallam Faye ya samu nasara.

Sai da mambobin Majalisar Tsarin Mulki, wadda ita ce babbar kotun Senegal suka tabbatar da cewa a ci gaba da gudanar zaɓe kamar yadda aka tsara, lokacin da suka tsaya kai da fata suka yi watsi da matakin shugaban ƙasar, inda suka zartar da cewa yunƙurinsa na canza ranar zaɓe, haramtaccen abu ne.

Shugabancin Pastef shi ma ya taka muhimmiyar rawar gani, inda suka yi tsayin daka duk da gagarumar razanarwa.

Sonko supporters

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Ousmane Sonko sun je su gaishe shi lokacin da ya je kaɗa ƙuri'a ranar zaɓe

Duk da sunan da ya yi na ɗan ta-kife, Ousmane Sonko ya kuma nuna cewa a shirye yake ya tanƙwaro kuma a jingine burinsa na takarar shugaban ƙasa don bai wa abokin tafiyarsa gagarumar damar samun nasara.

Tabbas, da ba don haka ba da mallam Faye bai shiga sahun 'yan takara a zaɓen shugaban ƙasar ba.

An yi tsammanin za a hana Sonko tsayawa takara a zaɓukan saboda kotu ta same shi da aikata laifuka, kuma daga bisani Majalisar Tsarin Mulki ta yi watsi da buƙatarsa ta neman tsayawa takara bisa hujjar cewa "takardunsa ba su cika ba". Duk da ƙoƙarin ganin sunansa ya shiga takardar zaɓe, shugabannin jam'iyyar Pastef sun yanke hukuncin cewa ba abu ne mai yiwuwa ba a bar shi ya tsaya takara.

Fahimtar hakan ce ta sanya aka ga cewa a bayyane take ƙarara, tsayar da Mallam Faye, wanda shi ba a taɓa gurfanar da shi gaban shari'a ba, shi ne zaɓi mafi aminci - duk da yake hakan na nufin shugaban jam'iyyar Ousmane Sonko, zai janye ya koma baya.

Ƙungiyoyin 'yan fafutukar fararen hula su ma sun ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba da kai rahoton ayyukan danniyar gwamnati da take haƙƙoƙin ɗan'adam, duk da kai musu hari da tsarewa da kuma buga musu hayaƙi mai sa hawaye.

Ta hanyar ayyukansu, sun tabbatar da ganin cewa al'ummar Senegal da sauran duniya sun san abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasar,lamarin da ya ƙara matsin lamba a kan Shugaba Sall don ya sarara.

A ƙarshe dai, irin wannan ƙoƙari da ƙarfin tasirin dimokraɗiyyar Senegal sun sanya Macky Sall ya saki Mallam Faye da Ousmane Sonko daga kurkuku - a matsayin wani babban shirin afuwa da masu suka suka ce lallai an ɓullo da shi ne don a bai wa shugabannin gwamnati kariya daga take haƙƙoƙin ɗan'adam da suka yi a lokacin hargitsin siyasar.

Faye supporters

Asalin hoton, AFP

Nasarar da mista Faye ya samu ta zamo wata abar alfahari ga jam'iyyun adawa a nahiyar Afirka.

A makon zaben kasar ta Senegal ne manyan jagororin hamayya a kasashen Angola da Uganda da Zimbabwe suka gana a birnin Cape Town domin tattauna "karuwar gwamnatocin kama-karya da na soji da kuma je-ka-na-yi-kan mulkin dimokradiyya inda ake wulakanta zabe domin dorewa a kan karagar mulki".

Ana tsaka da nuna damuwa dangane da irin halayyar gwamnatoci masu kama-karya, sai kwatsam labarin sauyin gwamnati a Senegal ya iske su, inda ya kara musu kwarin gwiwa da kuma nusar da su muhimmancin jajircewa.

Kamar yadda Dr Besigye ya bayyana yanayin a Senegal "abubuwan da suka faru a Senegal na tunatar da cewa sauyin gwamnati wani abu ne da zai amfanar da al'ummar kasa baki daya, amma juyin mulki na samar da sabon mulkin kama-karya ne."

Hakan ba ya nufin cewa darussan da aka samu daga kasar Senegal za su yi saukin kwatantawa a sauran kasashen ba.

Har yanzu a Senegal, ana iya samun sauyi ta hanyar kada kuri'a kasancewar akwai sauran 'yanci da kuma yanayin yin takara a siyasance.

To amma a wasu kasashen irin su Uganda da Zimbabwe, hakan na da wuyar gaske saboda yadda tsarin zaben kasashen ya zama babu 'yanci sannan kuma fannin shari'ar kasar ya mika wuya bori ya hau, inda su ma jami'an tsaro sun zama mamugunta.

Ƙalubalen da ke gaban shugaba Faye

Nasarori ko akasin gwamnatin mista Faye za su dogara ne kacokan ga irin abubuwan da shugabannin na jam'iyyar Pastef za su aikata daga yanzu.

Abu ne da za a yi sauran mantawa cewa lokacin da shugaba Sall ya zama shugaban kasar Senegal a 2012, an kalli abin da wata gagarumar nasarar dimokradiyya.

To amma bayan sabawa da shika-shikan dimokradiyya da alkawuran da ya dauka da suka janyo jama'a suka ba shi goyon baya, za a rinka tuna shugaba Sall a matsayin wani shugaba wanda giyar mulki ta ruda.

Domin gujewa abin d aya faru da mista Sall, ya kamata mista Faye da Sonko su mayar da hankali wajen sake gina kasa da kuma hada kan 'yan kasar.

Kuma hakan ka iya faruwa ne kawai idan suka guji yanayin da za a kawar da hankalinsu daga aikin da suka zo yi ta hanyar fifita al'amuran kansu da kuma kokarin daidaita gwamnati ta hanyar gasa da juna a fagen iko.

Wani babban abun da jam'iyyun hamayya ya kamata su yi domin inganta dimokradiyya shi ne tafiya da kowa ba tare da nuna banbanci ba da kuma tabbatar da cewa duk 'yan kasa suna da 'yancin siyasa da na rayuwa abun da zai haifar da tattalin arziki da yanayin siyasa mai dorewa.

Leonard Mbulle-Nziege mai bincike ne a jami'ar Cape Town kuma babban kwararre ne a cibiyar Concerto; inda shi kuma Nic Cheeseman darekta a cibiyar nazarin zabuka da dimokradiyya da adalci da kuma wakiltar jama'a da ke jami'ar Birmingham.