Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra'ila na neman Syria ta janye dakarunta daga kudancin ƙasar
- Marubuci, Sebastian Usher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan Gabas ta Tsakiya
- Aiko rahoto daga, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 2
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nemi a janye dakarun soja gaba ɗaya daga kudancin ƙasar Syria.
Buƙatar ka iya jawo rikici tsakanin Isra'ila da sabuwar gwamnati a Syria bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Yayin wani jawabi ga kuratan sojojin Isra'ila ranar Lahadi, Netanyahu ya ce ƙasarsa ba za ta ƙyale dakarun ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS) - ta 'yantawayen da suka jagoranci kifar da gwamnatin Assad - ko kuma na sabuwar gwamnatin Syria "su shiga yankin da ke gabashin biinin Damasucus ba".
"Muna neman a kawar da dukkan ayyukan soji a yankunan kudancin Damascus na Quneitra, da Deraa, da Suweida," a cewarsa. "Haka nan, ba za mu yarda da duk wata barazana ga al'ummar Druze ba da ke kudancin Syria."
Ya kuma ce dakarun Isra'ila za su ci gaba da zama har sai baba ta gani a cikin yankunan Syria da suka ƙwace tun bayan kifar da gwamnatin Assad a watan Disamban 2024.
Kafin yanzu, Isra'ila na cewa kutsen da ta yi cikin yankunan da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ayyana ba na kowa ba a Tuddan Golan a matsayin na wucin gadi domin tabbatar da tsaron Isra'ila.
Hikimarsu ita ce kare kansu daga hare-haren masu tsattsauran ra'ayi da ka iya shiga yankin na Golan.
Amma yanzu da yake yin waɗannan kalamai, Netanyahu ya bayyana ƙarara cewa sabuwar gwamnatin Syria da ke da tarihin yin jihadi a baya za ta iya kawo musu irin wannan barazanar.
Isra'ila ta kame mafi yawan Golan daga Syria yayin yaƙin shekarar 1967 kuma daga baya ta mamaye shi. Sai dai ƙasashen duniya ba su amince da matakin ba, kodayake Amurka ta amince da shi a 2019.
Shugaban riƙon ƙwarya na Syria kuma shugaban HTS, Ahmad al-Sharaa ya yi yunƙurin tabbatar wa Isra'ila cewa ba shi neman rikici kuma a shirye yake ya yi aiki da yarjejeniyar da aka daɗe ana aiki da ita tsakanin ƙasashen tun daga 1973.
Ya kuma jaddada cewa ba zai bari a yi amfani da Syria a matsayin dandalin kai wa Isra'ilar hari ba.
Amma shi ma ya nemi Isra'ila ta fice daga yankin da aka ayyana ba na kowa ba da ta ƙwace.
Sabuwar gwamnatin ta Syria na ganin rage tasirin ƙasashen waje a ƙasarsu da suka dinga neman gindin zama yayin yaƙin basasa na da muhimmanci wajen tsara makomar ƙasar.
Tuni suka rage tasirin Rasha da Iran a Syria.
Akwai yiwuwar Amurka ma za ta janye daga ƙasar ƙarƙashin sabbin manufofin Shugaba Trump bayan tallafin da Amurka ta daɗe tana bai wa mayaƙan Kurdawa a arewa maso gabashin ƙasar.
Turkiyya ma na ƙara samun gindin zama, wadda ta taimaka wa HTS wajen kifar da gwamnatin Assad.
Sai dai Isra'ilar ka iya kawo wa sabuwar gwamnatin Syria cikas wajen tabbatar da 'yancin ƙasar.
Abu ne mai wuya gwamnatin ta Syria ta aminceda wannan umarni da Netanyahu ya bayar na hana dakarunta walwala a cikin ƙasarsu duk da yadda take son nuna zaman lafiya.