Morocco za ta sake karɓar baƙuncin Wafcon karo na uku a jere a 2026

Lokacin karatu: Minti 2

Morocco za ta sake karɓar baƙuncin kofin Afrika na Mata Wafcon karo na uku a jere a 2026, yayin da aka sanar da wasannin share fagen shiga gasar a ranar Alhamis.

Ƙasashe 38 ne za su fara fafatawa a gasar, an samu ragin ƙasashe hudu da za su buga gasar 2024.

Kowacce ƙasa za ta buga wasa biyu – gida da waje, domin samun 11 da za su haɗu da mai masaukin baƙi su buga gasar Wafcon ta 2026.

Ƙasashe shida da ke saman jerin jadawalin Afrika da suka haɗa da Najeriya da South Africa da Ghana da Cameroon da kuma Ivory Coast – za su samu tikitin zuwa zagaye na biyu ko da ba su fafata ba.

Za a yi wasan zagaye na farko ne a watan Fabirairun 2025, sannan a yi na biyu a watan Oktoban shekarar mai zuwa.

Har yanzu dai hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ba ta sanar da ranar da za a fara gasar ba.

Botswana da Dr Congo da suka je matakin ƙarshe na 2024 bai zama dole su halarci gasar ta 2026, saboda koma bayan da suka fuskanta.

Za su kara da juna a wasan farko sannan wanda ya yi nasara zai fuskanci gwarzuwar gasar Afrika ta Kudu.

Gasar Wafcon ta 2024 da za a yi a Morocco aka jinkirta za a gudanar da ita ne daga ranar 5 ga watan Yuli zuwa 26 na shekara mai kamawa, saboda matsar da ita baya da aka yi saboda gasar Olympics ta 2024 da aka yi a birnin Paris.

An sanar da gasar ta ƙasashe 12 ne a watan Yunin da ya gabata.

Ƙasar da ke Arewacin Afrika ta kai wasan ƙarshe a gasar ta 2022.

Jadawalin wasannin shiga gasar Afrika ta mata ta 2026

Wasannin zagayen farko

  • Angola v Zimbabwe
  • Malawi v Congo-Brazzaville
  • Botswana v DR Congo
  • Tanzania v Equatorial Guinea
  • Uganda v Ethiopia
  • Eswatini v Namibia
  • Burundi v Burkina Faso
  • Djibouti v Togo
  • South Sudan v Algeria
  • Rwanda v Egypt
  • Kenya v Tunisia
  • Niger v The Gambia
  • Benin v Sierra Leone
  • Guinea v Cape Verde
  • Gabon v Mali
  • Chad v Senegal

Za a yi wasannin gida da wajen ne daga ranar 17 ga watan Fabirairun 2025 zuwa 26

Wasannin zagaye na biyu

  • Angola or Zimbabwe v Malawi or Congo-Brazzaville
  • Botswana or DR Congo v South Africa
  • Tanzania or Equatorial Guinea v Uganda or Ethiopia
  • Eswatini or Namibia v Zambia
  • Burundi or Burkina Faso v Djibouti or Togo
  • South Sudan or Algeria v Cameroon
  • Rwanda or Egypt v Ghana
  • Kenya or Tunisia v Niger or The Gambia
  • Benin or Sierra Leone v Nigeria
  • Guinea or Cape Verde v Gabon or Mali
  • Chad or Senegal v Ivory Coast

Za a yi wasannin gida da wajen ne daga ranar 20 ga watan Oktoba 2025 zuwa 28