Nawa ne albashin Tinubu da ministocinsa kuma me ya sa ake son yi masu ƙari?

Shugaba Bola Tinubu sanye da shuɗiyar kaftani da shudiyar hula da farin gilashi a fuskarsa

Asalin hoton, Presidency/X

Lokacin karatu: Minti 4

Batun sake nazarin albashin masu riƙe da mukaman siyasa a Najeriya na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar raba arzikin ƙasa ta Najeriya (RMAFC) ta sanar da cewa ta fara shirin sake nazarin yadda ake rarraba arzikin ƙasa tsakanin matakan gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananana hukumomin ƙasar.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban hukumar ta RMAFC Mohammmed Shehu ya yi iƙirarin cewa albashin da masu riƙe da mukaman siyasa ke karɓa bai taka kara ya karya ba, yayin da kuma ake fama da matsin tattalin arziki a ƙasar.

Shugaban ya ce a halin da ake ciki yanzu shugaba Bola Tinubu na karɓar naira miliyan 1.5 ne kowanne wata, yayin da abin da ministoci ke karɓa bai kai naira miliyan ɗaya ba.

''Ana biyan shugaban ƙasan Najeriya naira miliyan 1.5 kowanne wata, a ƙasar da ke da yawan al'umma sama da miliya 200''.

''Ba za a biya minista albashin ƙasa da naira miliyan ɗaya kowanne wata tun shekarar 2018 kuma a yi tunanin cewa zai mayar da hankali kan aikinsa ba tare da ya shiga wasu harkoki ba,''in ji shi

Shugaban ya ce a halin da ake ciki, Gwamnan Babban Bankin Najeriya ko Darakta Janar na karɓar albashin da ya ninka na shugaban ƙasa sau goma.

"Hakan bai dace ba. Ko kuma za ka biya shugaban hukuma albashin da ya ninka na babban lauyan ƙasa na tarayyar Najeriya sau ashirin.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Shehu ya bayyana cewa shekarar 1992 ne karo na ƙarshe da aka gudanar da cikakken nazari kan tsarin rabon arzikin ƙasa, sai dai a yi ta yin gyaran fuska kaɗan kaɗan ta hanyar umarnin shugaban ƙasa daga 2002 zuwa yau.

Ya ce saboda haka ne ake son a gudanar da cikakken garambawul kan tsarin na yanzu don tabbatar da al'amura sun daidaita da yadda yanayin tattalin arzikin ƙasar ke sauyawa.

Ya bayyana aikin a matsayin nauyin da kundin tsarin mulki ya rataya masa wanda ya zama wajibi bisa la'akari da irin sauye-sauyen da ake samu a fannin tattalin arziki da kuma yanayin siyasar Najeriya.

Yayin da aka tambaye shi ko hukumar za ta za ta sake nazari kan albashin ma'aikatan gwamnati, shugaban hukumar ya ce wannan aikin ya shafi masu riƙe da muƙaman siyasa ne kawai, wato gwamnoni, da ƴan majalisar dattawa, da duk ƴan majalisun dokokin, da ministoci da shugabannin hukumomi, da kuma sauran masu riƙe da muƙaman siyasa.

"Lokaci ya yi da mutane kamar ku ya kamata ku bai wa hukumar cikakken goyon baya don samar da albashi mai ma'ana ga ministoci da shugabannin hukumomi har ma da shugaban ƙasa.

Me ya sa za a ƙara wa ƴan siyasa albashi?

Mohammmed Shehu ya ce hukumar za ta duba yiwuwar yi wa masu riƙe da muƙaman siyasa ƙarin albashin ne la'aƙari da yanayin tattalin arzikin ƙasar.

"A bisa la'akari da alhakin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya rataya mana, sannan duba da sauye-sauyen da ake samu a fannin tattalin arziki da siyasa da na kasafin kuɗin ƙasarmu, hukumar ta yanke shawarar sake duba tsarin rabon arzikin ƙasa domin daidaito da yanayin tattalin arzikin da ake fuskanta a halin yanzu,'' in ji shi.

Ya kuma yi ƙarin bayani kan sakin layi na 32 (b) kashi na ɗaya a kundin tsasrin mulkin kasar na 1999, wanda ya tilasta wa hukumar RMAFC ''sake nazari daga lokaci zuwa lokaci tsarin rabon arzikin ƙasa domin tabbatar da ya daidaita da yadda al'amura ke tafiya a ƙasar.''

''Sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulki da suka ɗora nauyi da suka haɗa da, samar da wutar lantarki da layukan dogo, da samar da gidajen yari a wuyan gwamnaticin jihohi sun ƙara yawan ayyukan da waɗannan gwamnatocin za su gudanar kuma hakan na buƙatar ƙarin kuɗaɗen aiwatar da su,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin tsarin raba arzikin ƙasa na yanzu, gwamnatin tarayya na samun kashi 52.6 cikin ɗari yayin da jihohi ke samun kashi 26.7 cikin ɗari sai kuma ƙananan hukumomi suna samun kashi 20.6 cikin ɗari.

Ana kuma bai wa ma'aikatar birnin tarayya da asusun kula da yanayi, da ɓangaren albarkatun ƙasa kashi ɗaya cikin ɗari a ƙarƙashin tsarin rabon arzikin ƙasar.

Ra'ayoyin ƴan Najeriya

Tuni wasu ƴan ƙasar suka fara tofa albarkacin bakinsu kan sanarwar ta hukumar RMAFC, inda wasu ke sukar matakin da hukumar za ta ɗauka na ƙara wa ƴan siyasa albashi bayan a halin da ake ciki suna rayuwa ta ƙasaita yayin da ƴan ƙasar ke cikin halin ƙunci, kuma har yanzu ana ta kai komo kan batun mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar.

Yayain da wasu kuma ke jinjina wa hukumar bisa wannan mataki da take shirin ɗauka.