Me baje-kolin sabbin miyagun makamai da China ta yi ke nufi kan ƙarfin sojinta?

Armoured vehicles carrying the YJ-15 supersonic anti-ship cruise missile are seen during the military parade

Asalin hoton, ANDRES MARTINEZ CASARES/EPA/Shutterstock

    • Marubuci, Tessa Wong
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Asia Digital Reporter
  • Lokacin karatu: Minti 6

China ta yi baje-kolin wasu tarin sabbin makamanta, da jirage marasa matuƙa da manyan kayan aikin soji a wani gagarumin faretin sojoji da wasu ke kallo a matsayin aikewa da wani babban saƙo ga Amurka da ƙawayenta.

A lokacin faretin, shugaba Xi Jinping ya karɓi baƙuncin sama da shugabannin ƙasashe 20, ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin da na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, wadanda dukkaninsu ke dogaro da China kan tallafin tattalin arziƙi.

Wannan ya zama tamkar baje-kolin haɓɓakar ƙarfin China a doron duniya, da kuma murza gashin baki domin nuna ƙarfin sojinta.

Makaman da aka baje-koli sun hada da makami mai linzami na "Guam killer" da jirgi maras matuƙi na "loyal wingman" da kuma butumbutumin kyarkeci na tsaro.

Ga abubuwa biyar da hakan ke nunawa:

1. China na da tarin makamai. Ta yaya za ta yi amfani da su?

Abin da ya fito fili daga bajen-kolin makaman na ranar Laraba shi ne China ta ƙera makamai kala daban-daban cikin hanzari.

Shekara 10 baya, fasahar makaman da suka nuna ta kasance "tamkar kwafi ne mai rauni" na makaman zamani da Amurka ta ƙirƙira, in ji Michael Raska, mataimakin farfesa a fannin ci gaban ayyukan soji da ke jami'ar ƙere-ƙere ta Nanyang da ke Singapore.

To amma baje-kolin na yanzu ya bayyana ƙarin hazaƙar da ƙasar ta nuna wajen faɗaɗa makamanta, musamman ɓangaren jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami - wani abu da ke nuna ci gaba da aka samu a ɓangaren tsaro na ƙasar.

Tsarin ɓangaren tsaro na China ya ba ta damar ƙirƙiro sabbin makamai cikin hanzari fiye da sauran ƙasashe da dama, kamar yadda Alexander Neill na ƙungiyar Pacific Forum ya bayyana.

Haka nan za ta iya samar da waɗannan makamai masu matuƙar yawa, wanda hakan zai iya ba ta ƙarfi a fagen daga ta hanyar yi wa abokin gaba ruwan makamai.

"To amma ta yaya China za ta iya tsara ayyuka da wadannan makamai?

"Za su iya yin baje-kolin makaman masu ƙayatarwa to amma ko suna da kyakkyawan tsarin da za su iya amfani da su yadda ya kamata?" In ji Dr Raska.

Ya ƙara da cewa abin ba mai sauƙi ba ne ganin cewa China tana da rundunar soji mai girman gaske, sai dai ba a taɓa gwada ƙwarinsu ba kasancewar China ba ta fafata a wani babban yaƙi ba a baya-bayan nan.

2. China ta mayar da hankali kan makamai masu linzami don ƙalubalantar Amurka

China ta baje-kolin nau’i-nau’i na makamai masu linzami daban-daban.

Daga cikin su har da wanda ake yi wa lakabi da Dongfeng-61, wanda zai iya daukar makaman nukiliya da dama; makami mai linzami na Dongfeng-5C mai karfin ratsa nahiyoyi, wanda idan aka harba shi daga arewacin China zai iya kai wa har Amurka; makamin “Guam Killer” Dongfeng-26D mai matsakaicin zango, wanda zai iya yin nisan da zai kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Guam.

A graphic with annotation for the DF-61 missile reads "China's new intercontinental missile capable of carrying nuclear warheads"
Bayanan hoto, Wannan ne karo na farko da aka nuna makami mai linzami na DF-61 a bainar jama’a
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka nan kuma akwai makamai masu linzami masu gudun fitar hankali kamar makamin YJ-17 da YJ-19, wanda kedan karen gudu tare da kwarewa wajen zulliya domin kauce wa makaman kakkabo makami masu linzami.

Akwai dalilin da ya sa China ta mayar da hankali kan makamai masu linzami.

China na kera makamai masu linzami da rokoki ne a wani bangare na bunkasa shirinta na kare kai - da kuma domin kalubalantar zarrar da Amurka ta yi a harkar yakin ruwa, in ji Mr Neil.

Babu wanda ya kai Amurka kwarewa a fagen yakin ruwa a duniya, inda take da tarin jiragen ruwa masu daukar jiragen saman yaki da mayaka - har yanzu China ba ta yi kusa ba a yawansu.

Sai dai Mr Neil ya bayyana cewa wasu a yammacin duniya na ganin cewa wadannan kayan yakin ruwa na Amurka na cikin hadari, kasancewar za su iya zama “masu saukin tarwatsawa“ ta hanyar amfani da makami mai linzami.

Ba kawai matakin kariya China take bunkasawa ba, tana kuma samar da makaman mayar da martani, wanda shi ne kargin da kasa ke da shi na mayar da biki a lokacin da aka kai mata hari.

Sauran wasu makaman da China ta yi holi sun hada da LY-1, wanda wata makekiyar tocila ce mai hasken da za ta iya kona ko kuma lalata laturonin makami ko kuma ma ta kashe wa matukan jirgi isi, wanda za si zamo garkuwa daga jiragen saman yaki na zamani kamar J-20 da J-35.

3. China na amfani da ƙirkirarriyar basirar AI waje hada jirage marasa matuƙa

Akwai jirage marasa matuka daban-daban da aka yi baje-koli, kuma waau daga cikinsu na amfani ne da Kirkirarriyar basira, amma wanda ya fi daukar hankali shi ne AKX-002 mai tafiya a kasan ruwa.

Ana kuma kiran shi da makekeiyar na’urar da ke tafiya a kasan ruwa (XLUUV) mai tsawon mita 20, wanda za a iya amfani da shi wajen tattaro bayanai.

A graphic with annotation for the AJX-002 drone reads "A giant, 60-foot (18m) underwater nuclear-capable unmanned vehicle"

China ta kuma fito da jirgin yaki maras matuki mai wuyar gani, wanda ake yi wa taken GJ-11, wanda zai iya tafoya tare da jirgi mai matuki yana taimaka masa wajen kai hari.

Baya da jerin jirage marasa matuka, haka nan kuma China ta nuna wa duniya wasu “butumbutumin karnuka”. Masana sun ce ana iya amfani da su wajen yin abubuwa da yawa, kamar tattara bayani da cire nakiyoyi, da kuma kai hari kan abokan gana.

Baje-kolin na makamai na nuna cewa China na son ta kara inganta aikin soji, a inda take baya, sannan kuma ta maye tsofaffin kaya da sababbi”.

Ya nuna a karara cewa ta dauki darasi daga abin da ke faruwa a Ukraine, inda ake amfani da jirage marasa matuka wajen gajiyar da abokin fada, in ji Dr Raska.

A bangare daya masanin ya ce yayin da wasu kasashe ke dari-dari wajen amfani da kirkirarriyar basira a fagen hada makamai, ita China ba ta damu da hakan ba. “Suna ganin cewa za su iya sarrafa AI din shi ya sa suka saka shi a makamansu.”

A graphic with annotation for the robot wolves reads "Can be equipped to perform different roles alongside soldiers, such as reconnaissance and transporting ammunition"

4. China ta samu ci gaba wajen kera makamai amma har yanzu Amurka ce a gaba

Wannan baje-kolin makamai ya nuna karara cewa China na kokari wajen ganin ta kamo Amurka a fannin fasahohin soji, sannan kuma tana da karfin samar da makamai cikin hanzari.

To amma har yanzu Amurka ce ke kan gaba idan ana maganar tafiyar da lamarin makamai, a cewar masana.

Bangaren sojin Amurka “ya yi zarra” a harkar soji saboda akwai tsarin da ya fi bai wa Amurka damar yin sauyi cikin kankanin lokaci, in ji Dr Raska.

A graphic with annotation for the GJ-11 stealth drone reads "Part of China's fleet of unmanned combat aerial vehicles"

“China za ta iya mallakar makamai masu kyawu to amma babu wanda ya isa ya yanke shawarar yin amfani da su sai ya samu umarni daga sama”.

5. Tallar makamai - da kuma damar nuna wa Amurka kwanji

Ganin yadda aka gayyato sama da shugabannin kasashe 24 wajen bikin baje-kolin, wannan zainiya zama wani gagarumin taron tallata makamai ga wadanda ake ganin za su so su sata, in ji Mr Neil.

Wasu kasashen da suka halarta, kamar Myanmar, an san dama suna cikin kasashen da ke kan gaba wajen sayen makamai daga China.

To amma damar samun karin kwastomomi ya ta’allaka ne kan yadda China ta iya fadada tasirinta a sassa daban-daban na duniya, in ji Dr Raska.

A graphic with annotations that highlight President Xi and his wife, Russian Putin, North Korean leader Kim, Iranian President Pezeshkian, Azerbaijiani President Aliyev in a group photo

Daga cikin masu sayen makaman akwai wasu da ke tsaye a gaba a lokacin tare da Xi - Vladimir Putin da Kim Jong Un.

Wannan babban sako ne ga Amurka, in ji Mr Neil: idan har Amurka na son ta kalubalanci wadannan mutane uku “to sai dai ta “kara da su a wurare uku daban-daban a lokaci daya - Yankin Koriya, da Taiwan da kuma a Ukraine.”