Ana ce-ce-ku-ce kan Firaiminista da ta je wurin casu

Firaiministar Finland, Sanna Marin, tana fuskantar suka bayan bullar wani bidiyo da ke nuna ta tana cashewa.

A bidiyon da ake tunanin an dauka daga kafafen sada zumunta, an ga Firaiministar da kawayenta har da wasu fitattu a kasar suna rawa suna waka.

Ta fuskanci caccaka daga jam'iyyun hamayya inda shugabar wata jam'iyya ta nemi a yi mata gwaji don gano ko tana ta'ammali da kwayoyi.

Ms Martin mai shekara 36 dai ta musanta shan miyagun kwayoyi sai dai ta ce barasa kawai ta sha sannan kuma ta cashe cikin farin ciki.

A baya ita ce jami'ar gwamnati mafi kankantar shekaru a duniya - matsayin da a yanzu ya koma wajen Shugaban Chile - Ms Marin ba ta cashewa a boye kuma an sha daukan hotonta a wuraren waka.

A shekarar da ta gabata, ta nemi afuwa saboda zuwa wajen cashewa bayan ta yi mu'amala da wani mai cutar korona.

Ko a makon da ya gabata ne wata kafar yada labarai ta Jamus ta ayyana Ms Marin a matsayin Firaminista mafi saukin kai a duniya.

Da take magana kan bidiyon ranar Alhamis, Ms Marin ta ce ta san ana daukarta a bidiyo amma takaicinta shi ne yadda bidiyon ya fita idon jama'a.

"Na yi rawa, na yi waka kuma na cashe - duk abubuwa ne da shari'a ta sahale. Kuma ban taba kasancewa cikin yanayin da na gani ko sani na amfani da kwaya ba," kamar yadda ta fada.

Shugabar Jam'iyyar adawa Riikka Purra ta bukaci a yi wa Ms Marin gwaji inda ta ce tana da shakku kan Firaministar.

Shi kuwa Mikko Karna, daga Jam'iyyar Centre Party wanda ke karkashin gwamnatin hadaka ta Ms Marin, ya wallafa sakon Tuwita cewa zai fi dacewa ta kai kanta a yi mata gwajin shan kwaya.

Ms Marin ta nuna alamar amincewa da shawarar, inda ta fadawa manema labarai cewa ba ta taba amfani da kwaya ba kuma ba ta da matsala idan ta kama ta je gwajin.

"Ina da iyalina, ina aiki kuma ina da lokacin da zan kasance tare da abokanai . Kamar dai yadda sauran mutane masu shekaruna," in ji Ms Marin.

Ta kara da cewa ba ta ga bukatar sauya dabi'un ta ba. Zan ci gaba da zama a yadda nake kuma ina fatan za a amince da hakan," a cewar Firaiministar.

An yi ta cece-kuce kan bidiyon a kafafen yada labaran Finland - wanda ke tabbatar da yadda bidiyon ya karade ko ina.

Amma sauran yan siyasa daga bangaren hamayya sun soki Firaministar da kuma kafafen yada labarai saboda yin magana kan party din a maimakon mayar da hankali kan matalolin cikin gida.

Tun Disambar 2019 ne Ms Marin ke shugabanci kuma ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam'iyyarta.

Wa ce ce Sanna Marin?

  • A 2019 ne Sanna Marin, mai shekara 34, ta zama Firaiminista mafi kankantar shekaru a duniya bayan da jam'iyyarta ta zabe ta inda ta gaji tsohon shugaba Antti Rinne
  • Ta fito daga nutsattsen gida. Iyayenta sun rabu a lokacin da take matashiya kuma mahaifiyarta ce ta rike ta
  • A 2015, ta yi magana kan tsangwamar da ta fuskanta lokacin da mahaifiyarta ta kulla soyayya da yar uwarta mace
  • Bayan kammala karatu a Jami'ar Tampere da yin aiki a karamar hukuma, an dauke ta aiki a majalisar dokokin Finland a 2015 tana shekara 29

Wani dan jarida Robert Sundman ya fada wa BB cewa "akwai mutanen da ke ganin babu wani abu ga macen da ke da shekarunta ta shakata da kawayenta, wasu kuma na mamaki."

Amma wani abu daya shi ne, hotunan da aka dauka na baya ba su shafi farin jinin da take da shi ba a Jam'iyyarta."

Mista Sundman ya ce mutane na sa ido kan irin kawancen da take da fitattun mawaka abin da ya ce muhimmin abu ne da ya banbanta ta da sauran Firaministoci.

A bidiyon da ya bulla, an ga Ms Marin tare da mawakiya yar Finland Alma, da Petri Nygard da dan jarida Tinnu Wikstrom.

Wasu fitattu da wasu yan majalisar dokoki daga Jam'iyyar Social Democratic duk sun bayyana a wajen.

A makon da ya gabata, Firaiministar ta samu yabo saboda yanayin hoton da aka dauke ta tare da Janita Autio, wata kwararriyar mai daukan hoto wadda ita ma ta bayyana a bidiyon a wani bikin waka a Helsinki.