Tashar WhatsApp ta BBC Hausa da bayani kan tsare muhimman bayananku

Lokacin karatu: Minti 2

Amanar da ke tsakanin mu da ku na da matuƙar muhimmanci a gare mu. Hakan na nufin BBC ta yi alƙawarin tsare bayananku. Yana da muhimmanci ku karanta wannan bayani domin sanin yadda muke amfani da bayananku da kuma dalilin yin hakan.

Wannan maƙala kan sirranta bayanai na ƙunshe da bayyani kan yadda za mu karɓa tare da yin amfani da bayananku a lokacin alaƙarku da mu, bisa tsarin dokar kare bayanai.

Waɗanne bayananku BBC za ta karɓa da kuma yadda za mu yi amfani da su

BBC za ta karɓi bayanan rayuwarku da kuka zaɓi a yi amfani da su a wani ɓangare na shiga da kuma bin tasharmu. Waɗannan bayanan sun haɗa da wasu ko ma duka bayanan da ke ƙasa.

Bayanan rayuwa

Bayanan rayuwa da za a iya karɓa sun ƙunshi:

  • Sunan da ku ke amfani da shi a manhajar WhatApp
  • Lambar waya
  • Hotonku da ke a manhajar WhatsApp

BBC za ta iya amfani da bayanai masu muhimmanci bisa yanayin hotonka a manhajar da kuma tsari na bayanan sirrin mai amfani da manhajar da aka sani da rukunin bayanai na musamman da ka zaɓi bayyanawa. Suna iya haɗawa da:

  • Ƙabilarka
  • Bayanan lafiyarka
  • Addininka ko aƙida
  • Jinsi
  • Ra'ayin siyasa

Sirranta hotonka na manhajar WhatsApp

A sani cewa idan ka bada dama kowa ya kalli hotonka a WhatsApp, BBC ma na iya ganin wannan bayanin. Ana shawartarka da ka sauya tsarin bayanan sirrinka zuwa 'iyakar waɗanda nake da lambobinsu' domin taƙaita bayanan rayuwarka da za mu iya samu ta WhatsApp.

Wane ne mai lura da bayanan da ake tattarawa?

BBC ce take sarrafa duk wasu bayanan mutane da ta tattara yadda take so, waɗanda ake ajiyewa a manhajohin BBC.

WhatsApp na sarrafa bayanai yadda yake so na duk bayanan da ka aika ta manhajar. A kiyaye cewa kana kewaye da tsarin sirranta bayanai na WhatsApp da ƙa'idojin amfani da manhajar. WhatsApp na iya tura bayananka zuwa wasu kamfanonin Meta.

Duk kafafen na yanke shawara kan yadda zai sarrafa bayanan rayuwarka, abin da za a yi amfani da su da hanyoyin da za a sarrafa. Domin kauce wa shakku, za a karɓi bayanan rayuwarka sannan BBC ta sarrafa su bisa dalilan da ta bayyana a sanarwar tsare bayanai, wanda shi ne, shiga da kuma bin Tashar BBC WhatsApp. Kowane mai sarrafa bayani na da nauyin bin dokoki da ƙa'idojin dokar kare bayanai.

Halastattun hanyoyin sarrafa bayananka

Muna dogaro ne da amincewarka kafin yin amfani da bayanan rayuwarka. Dalili shi ne ka yarda ka shiga Tashar WhatsApp ɗinmu. Idan ka zaɓi ka daina samun rahotanni, kana iya janye amincewarka a kowane lokaci ta hanyar cire kanka daga tashar.

Wallafa bayananku

BBC ba za ta tura bayanan rayuwarku zuwa wasu kamfanoni daban ba tare da amincewarku ba.

Riƙe bayananka

BBC za ta yi amfani da bayananku ne tsawon lokacin da ake buƙata domin cika manufofin da muka zayyana a wannan sanarwar tsare bayanai.

Haƙƙoƙinku da ƙarin bayanai

Kana da iƙo a ƙarƙashin dokar tsare bayanai ta Burtaniya. Kana iya neman kwafin bayananka da BBC ta riƙe, da suka haɗa da bayananka da BBC take riƙe da su kamar yadda aka bayyana a sama.

Kana iya tuntuɓar mu ta imel ta adireshi: [email protected]. Idan kuna da tambaya ko kuna son ƙarin bayani kan ƴancinku, ku ziyarci http://www.bbc.co.uk/privacy

Idan kuna da damuwa kan yadda BBC ke riƙe bayananku, kuna iya tura ƙorafi zuwa ga hukumar da ke sanya ido a Birtaniya, ofishin kwamishinan bayanai https://ico.org.uk/.

Sabunta sanarwar tsare bayanai

Za mu riƙa sabunta sanarwar sirranta bayanai idan akwai muhimman sauye-sauye kan yadda muke amfani da bayanan rayuwarku da muka samu daga gare ku.