Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Indiya ta aika kumbonta na farko zuwa rana
Indiya ta harba kumbonta na farko zuwa rana, kwanaki kaɗan bayan da ƙasar ta kafa tarihin zama ta farko da kumbonta ya sauka a ɓaryar kudu na duniyar wata.
An harba mumbon mai suna Aditya-L1 daga tashar Sriharikota ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:50 agogon kasar.
Kumbon zai yi tafiyar kilomita miliyan 1.5 daga doron duniya zuwa inda rana take.
Hukumar sararin samaniyar ƙasar ta ce kumbon zai yi tafiyar wata huɗu.
Manufar wannan sabon shirin tura kumbon ita ce samar da wata tasha ta musamman da za ta rinƙa bincike - inda ta ke muradin zama ƙasa ta farko da za ta rinƙa lura da tauraruwar (rana) da ke kusa da duniyarmu da kuma gudanar da wani nazari game da ɗabi'u da yanayin falaƙai da yanayin iskar da ake samu kewaye da su.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka soma gudanar da bincike a kan rana ba - NASA tare da Hukumar Nazarin Sararin Samaniya ta Turai sun taɓa tura wasu kumbuna domin binciken - sai dai wannan na Indiya ya sha bamban ta wasu fuskokin.
Shin wane kumbo ne ma ake kira Aditya-L1? Ga cikakken bayanin dukan abin da kuke son sani game da wannan tafiya.
Ya tsawon lokacin da zai ɗauka kafin ya isa kusa da Rana?
Babu alamun kumbon zai ci gaba da ziyarar tauraruwar, wato rana.
Nisan tafiyar da kumbon zai yi ya kai kilomita miliyan ɗaya da rabi - wato dai nunki huɗu na nisan da ke tsakanin duniyarmu da wata ke nan, amma tafiyar ɗan wani yanki ce kawai da ba ta fi kaso ɗaya cikin ɗari ba domin cikakken ainihin nisan da ke tsakanin duniyarmu da rana zai kai kilomita miliyan 151.
Idan aka kwatanta da kumbon Parke na hukumar Nasa, da ya yi wata tafiyar da ta wuce tauraruwar Venus da aka sani da Zahra, shi ma zai yi tafiyar da nisanta ya kai kilomita miliyan 6.1 daga doron kasa.
Zai ɗauki kombon Aditya-L1 lokaci kafin ya isa a can.
Kamar yadda Cibiyar Nazarin Sarararin Samaniyar Indiya ta bayyana a shafin sada zumunta na X da aka fi sani da Twitter a baya,"Gaba ɗayan lokacin da za a ɗauka daga ƙaddamar da Aditya L-1 zai ɗauki tsawon wata huɗu".
To me ya sa ake wannan fama duk da cewa rana na da matuƙar nisa tsakanin ta da duniya?
Me ake nufi da sarari maras fizgar maganaɗisu?
Wannan dai wani wuri ne da ake samun rashin fizgar maganaɗisu da ke tsakanin duniya da rana. Sararin wanda ake wa laƙabi da Lagrange a kimiyyance yakan samar da wani daidaito da kan taimaki jiragen jigilar 'yan sama jannati da sauran kumbuna rage shan mai.
Sunan ya samo asali ne daga wani Bafaranshe masani ilmin lissafi mai suna Joseph-Louis Lagrange, wanda shi ne ya fara nazari game da wannan wuri tun a ƙarni na 18.
Mece ce manufar wannan tafiyar ta kumbo Aditya-L1?
Kumbon binciken na Indiya zai ɗauki na'urori bakwai tare da shi, zai kuma yi nazarin wasu rigunan tururin haske mai zafi da talgen zafi da ke zagaya rana - da ake kira photosphere da chromosphere a turancinkimiyya, ta hanyar amfani da wasu na'urori masu gano karfin maganaɗisun.
Zai gudanar da binciken abin da ke samar da mabambancin yanayi a sararin falaƙai da kuma gano tushen da yadda iska ke fitowa daga tsirkiyyar rana irin wadda ke ƙawata kudanci da arewacin yankunan duniya, amma kuma yake haifar da damuwa sakamakon fizgar maganaɗisu.
Idan aka tura wannan kumbo zuwa sarararin falaƙai "zai ci gaba da tattara bayanan da ya samu ta hanyar nazarin rana kai tsaye".
"Wannan zai ƙara samar da bayanai game da ita kanta rana da yadda ta ke shafar yanayin sararin falaƙai', in ji Hukumar Kula Da Sararin samaniyar Indiya, ta Isro.
Zai kuma ci gaba da lura da yadda tsirkiyar zafi take, abin da aka kasa gudanar da bincike kansa a doron duniya saboda iskar duniya ta riga ta tace shi.
Huɗu daga cikin na'urorin za su ci gaba da sanya ido kan rana sauran uku kuma za su kula da yanayin iskar da ta yi gangami a yankin Lagrange, inda za su samu muhimman bayanai game da abubuwan da ke haddasa sauye-sauyen rana a cikin sararin da ke tsakanin falaƙai.
Isro ya yi fatan wannan tafiyar kumbon za ta kai ga samar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen ƙara fahimtar yadda rana take kamar tsananin zafin da talgen da ta ke amayarwa da kuma yadda yanayin sararin falakai ke sauyawa.
Nawa ne kudin da wannan tafiyar binciken da kumbon Aditya-L1 zai yi za ta laƙume?
Tun a 2019 Gwamnatin Indiya ta amince ta kashe dala miliyan 46 domin gudanar da wannan shirin.
Kawo yanzu dai Hukumar binciken sararin samaniyar Indiya ba ta bayar da cikakken bayanin ko nawa ne aka kashe wajen gudanar da wannan gagarumun aiki ba, duk da kuwa yau fiye da shekara biyar ke nan da ƙera wannan kumbon domin ya soma aiki.
Hukumar Isro kan yi amfani da kumbo marasa nauyi. Dubarar hakan ita ce zai fi sauri da kuma iya jure fizgar maganaɗisu. Wannan zai ba su damar isa duniyar wata ko Mars cikin sauri. Sai dai ba kasafai irin waɗannan kumbunan suka cika tsada wurin ƙera su ba.
Kumbon Chandrayaan-3 - "kumbon duniyar wata" ke nan a harshen Sankrit, wanda ba shi da matuƙi - a makon jiya ne ya sauka a doron duniyar wata, abin da ya sa Indiya ta zama ta huɗu a duniya bayan Amurka da Rasha da Chana da suka fara zuwa.
A shekarar 2014, ta zama ta farko a nahiyar Asiya da ta tura kumbo zuwa duniyar Mars (Mas) kuma a shekara mai zuwa ma ta na shirin tura 'yan sama jannati inda za su zagaya falaƙin duniya.
Wannan ya sa a baya-bayan nan hukumar lura da sararin samaniyar Indiya ta ƙayyade kasafin wajen ƙera kumbo, domin cimma wasu muhimman nasarori.