Hotunan yadda aka gudanar da jana'izar sarkin Zuru

Lokacin karatu: Minti 2

An gudanar da jana'izar, marigayi sarkin Zuru, Manjo Janar Muhammadu Sami II mai ritaya, wanda ya rasu ranar Lahadi.

Mataimakin shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa wajen jana'izar

Marigayin ya rasu ranar Lahadi a wani asibiti da ke Landan

An yi wa marigarin jana'izar soji, kasancewarsa tsohon babban janar a rundunar sojin Najeriya.

Mutane da dama a ciki da wajen Najeriya sun halarci jana'izar marigayin

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanui II na daga cikin manyan baƙin da suka halarci jana'izar marigayin

Marigayi Manjo Janar Muhammadu Sami II mai ritaya, ya jima yana aiki a rundunar sojin Najeriya, kafin ya yi ritaya, a kuma naɗa shi sarkin Zuru.