Wa ya ƙirƙiro jirgin sama?

Santos Dumont

Asalin hoton, BBC/Getty Images

    • Marubuci, Camilla Veras Mota
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 7

Wa ya ƙirƙiro jirgin sama?:Wannan tambaya ce kamar mai sauƙi, amma ko alama ba ta da sauƙin amsawa saboda an daɗe ana ja-in-ja a kanta - game da ainahin wanda ya ƙirƙiro jirgi.

Amurkawa da yawa na ganin Orville da Wilbur Wright - waɗanda masu gyaran keke ne da suka koyi aikin injiniya da kansu su - su ne ainahin waɗanda suka ƙirƙiro jirgin sama na farko da suka yi gwaji a 1903.

Amma kuma su ma mutanen Brazil da dama na ganin ba wanda ya cancanci kambin wannan gwaninta illa Alberto Santos Dumont, magajin wasu iyalai attajirai masu samar da gahawa, wanda ya tashi da jirgin sama na farko da hukumar kula da tashin jiragen ta duniya a Paris ta tabbatar a 1906.

To a nan wanne ne daidai?

Santos Dumont a jirgin samansa na farko (14-bis) wanda ya yi shawagi na farko a Paris

Asalin hoton, National Library of France

Bayanan hoto, Santos Dumont a jirgin samansa na farko (14-bis) wanda ya yi shawagi na farko a Paris

Tashin jirgin farko na Santos Dumont

A farkon ƙarni na 20, gomman masu ƙirƙire-ƙirƙire ne suke ta faman samar da na'urar da za ta kai ga cika burin da ɗan'Adam ya jima yana fatan cimmawa - wato tashi sama a na'ura.

Da dama daga cikin irin waɗannan masu basirar ƙirƙire-ƙirƙire sun tattaru a Paris daga sassan duniya - birnin da a lokacin yake da kyawawan makarantun koyar da ilimin injiniya da kuma kuɗaɗen gudanar da bincike a kan fannoni da dama na fasaha da kimiyya.

''Magana ce ta lokaci kawai a wannan lokaci,'' in ji masanin tarihi na Faransa Farfesa Jean-Pierre Blay.

A wannan lokacin waɗanda ke kan gaba wajen sha'awa da fatan ganin an ƙirƙiro jirgin sama, sun sa wasu sharuɗa da duk na'ura ko jirgin da aka ƙirƙira zai cimma kafin a ce ya tabbata jirgin sama na farko a tarihi.

Waɗanan sharuɗa sun haɗa da cewa jirgin zai tashi da kansa ba tare da an tura shi da gudu ba, da kuma cewa ya yi ta shawagi ko tafiya a sama zuwa tsawon wani lokaci.

To a ranar 12 ga watan Nuwamba na 1906, Santos Dumont ya cika dukkanin ƙa'idojin da aka shinfiɗa, inda ya tashi sama ya yi tafiyar mita 220 da jirginsa mai suna 14-bis, a gaban tarin 'yan kallo a Paris

Shekara mai zuwa kuma mutumin dan Brazil ya sake ƙirƙiro wani samfurin jirgin mai suna Demoiselle, wanda shi ne samfurin jirgin sama na farko ƙarami da aka samar da yawa a duniya.

Demoiselle na shawagi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Demoiselle shi ne jirgin sama na farko da aka samar da yawa a duniya

Gabatar da shaida

Amma kuma a shekarar 1908 sai 'yan'uwa (wa da ƙani) Wright, Amurkawa suka yi iƙirarin cewa ai su tun shekara biyar baya sun tashi da jirgin sama.

'Yan'uwan sun ce tuni sun ƙirƙiri jirgin saman sun kuma jarraba shi abin da ya rage musu a lokacin shi ne su samu takardar 'yancin mallakar fasaharsu, kuma suna tsoron kada a saci fasaharsu.

To amma kuma matsalar ita ce mutum biyar ne kaɗai aka ce sun ga tashin wannan jirgi na su ranar 17 ga watan Disamba na 1903 a garin Kitty Hawk da ke arewacin Carolina.

Kuma daga cikin shedun da aka gani na tashin wannan jirgi akwai saƙon telegram da hotuna kaɗan da kuma mujallar Orville.

Jirgin saman Amurkawan ya yi ƙoƙarin tashi a 1903

Asalin hoton, Library of Congress

Bayanan hoto, Jirgin saman Amurkawan ya yi ƙoƙarin tashi a 1903
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Wannan rana ta 17 ga watan Disamban 1903, ita ce ta farko da waɗannan 'yan'uwa biyu suka tashi sama da jirgin nasu.

Kuma sun gamsu cewa sun kawar da wannan matsala bayan sun yi shawagi sosai a sama,'' in ji Tom Crouch masanin tarihi a ɗakin adana kayan tarihi na jiragen sama da sararin samaniya na Smithsonian kuma marubucin littattafai da ma a kan 'yan'uwan biyu na Wright.

Ya ce ''akwai abubuwa da dama da za su daidaita a lokacin, amma dai sun ƙera jirgin sama kuma ya tashi.''

Duka sun yi waɗannan gyare-gyare ne cikin sirri, ba su fito fili ba sai a 1908, lokacin da suke fafutukar ganin an ce su ne na farko da suka ƙirƙiro jirgin sama.

'Yan'uwan biyu sun je wani rangadi na Turai inda suka yi gwajin jirgin har sama da 200 a ƙasashe irin su Faransa da Italiya, inda suka yi tafiyar da ta kai ta kilomita 124 a tashi ɗaya.

To daga wannan lokacin ne mutane irin su Ferdinand Ferber masani na farko-farko a harkar jirgin sama daga Faransa, suka yarda da iƙirarin iylan gidan na Wright cewa su ne na farko da suka ƙirƙiro jirgin sama.

Masanin ya ƙara da cewa ba ta yadda za a iya ƙirƙiro jirgin sama da zai iya tashi da shawagi da walankiya a lokaci ɗaya.

Wata jarida kenan ɗauke da labarin tashin jirgin saman 'yan gidan na Wright

Asalin hoton, US Library of Congress

Bayanan hoto, Sai bayan shekaru ne labarin tashin jirgin saman na 'yan'uwan biyu na Wright ya bayyana

Tura jirgi kafin ya tashi

Samfurin jirgin saman Amurkawan kenan da aka nuna a Turai, sai dai kuma ba shi da tayoyi, wanda hakan ya sa sai an tura shi sannan ya tashi.

Wannan ya kasance abin taƙaddama.

Masu sharhi sun ce injin jirgin ba shi da ƙarfi sosai, kuma jirgin ya iya tashi ne sakamakon tura shi da aka yi.

To amma kuma 'yan'uwan sun ce sun tsara a riƙa tura shi ne ya tashi saboda suna son ya riƙa tashi a ko'ina.

To sai dai kuma Santos Dumont da 'yan'uwan biyu na gidan Wright ba su kaɗai ba ne suke iƙirarin fara ƙirƙiro jirgin saman ba a duniya.

Tsohon hoton Gustav Weisskopf yana zaune kusa jirgin saman da ya ƙirƙiro

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gustav Weisskopf, ɗan ƙasar Jamus da ke zaune a Amurka shi ma yana daga cikin mutanen farko-farko da suka ƙirƙiro jirgin sama

Gustav Weisskopf ɗan ƙasar Jamus ne da ke zaune a Amurka, kuma ana ganin ya tashi da jirgin sama a 1901.

Haka shi ma Richard Pearse, ɗan ƙasar New Zealand an ce ya tashi da jirgin sama a watan Maris na 1903.

Haka kuma akwai wasu shedu da ke nuna cewa John Goodman da mutanen gidansa sun tashi da jirgin sama na farko da ke da matuƙi da sauran ma'aikata - kodayake ba mai inji ba ne - a wajen birnin Howick na Afirka ta Kudu tun ma kafin shekarar 1871.

Kuma har zuwa yanzun nan akwai kayan tarihi na tunawa da jirgin.

To saboda wannan wasu ƙwararru a kan harkar jirgin sama ke ganin maganr wanda ya fara ƙirƙiro jirgin sama ba ta da wani muhimmanci.

Babban editan mujallar harkokin jirgin sama (Jane's All the World's Aircraft) tsawon shekara 25, Paul Jackson, babu ta yadda za a ce rana ɗaya wani ya tashi kwatsam ya yi zane ya ce wannan shi ne jirgin sama da zai yi aiki.

Ya ce ƙoƙari ne kawai na tarin mutane da suka yi aiki tare.

Girmama waɗanda ba su cancanta ba

Jackson na ganin mutanen da suka kasance na farko-farko wajen ƙirƙiro jirgin sama kamar su Santos Dumont da Weisskopf da wasu da dama sun cancanci yabo fiye da yadda aka yi musu.

To amma abin takaicin shi ne mutanen da suke da alaƙa da manyan mutane da kuma manyan lauyoyi su ke samun wannan yabo da duk wani abu da ke tattare da bajintar, in ji ƙwararren na harkar jirgin sama ɗan Birtaniya.

Ya ce abin takaicin shi ne idan ka duba yawancin mutanen da ake alaƙantawa da ƙirƙire-ƙirƙiren ƙarni na 19 da na 20 za ka ga ana dangantawa ne da mutanen da ba su dace ba.

Ya bayar da misalin masanin kimiyya Alexander Graham, ɗan Scotland, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya ƙirƙiro wayar tarho, kodayake yanzu ana taƙaddama a kan hakan.

A shekarar 2002, majalisar dokokin Amurka ta zartar da cewa duk da cewa shi Graham ya samu haƙƙin mallakar fasahar ƙirƙirar tarho, ainahi Antonio Meuci ne wani talaka ɗan Italiya, da suke amfani da wajen aiki ɗaya da Bell, ya ƙiriro na'urar.

Glenn Hammond Curtiss

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Glenn Hammond Curtiss ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiri jirgin sama wanda 'yan gidan Wright suka kai ƙara

Marcia Cummings dangin Glenn Hammond Curtiss, wanda yana daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro fasahar jirgin sama a farko-farko, wanda 'yan'uwan na gidan Wrights, suka kai ƙara a 1909 - bisa zargin keta haƙƙin mallakara fasaha.

A yanzu Cummings na aiki a kan wani shafin intanet da ke tuhumar bayanan 'yan'uwan na Wright a kan iƙirarinsu na tarihin abubuwan da suka kasance na zama na farko da suka ƙirƙiri jirgin sama.

Cummings ta ce tana ganin 'yan gidan na Wright suna maƙarƙashiya ne ta kawar da tarihin mutane irin su Curtiss daga tarihi.

Sai dai Amanda Wright Lane, wadda dangin Orville da Wilbur ce, wadda kuma take aiki domin kare tarihinsu, ta musanta haka:

"Sanin yadda Orville yake [Wilbur ya rasu a 1912] ba zai taɓa ɓata wani ba da niyya."

"Amma zai kare abin da shi da Wilbur suka yi da kuma gaskiyar abin da suka yi," in ji ta.