Mai sayar da kayan kamshi da masu wasan yoga a cikin hotunan Afirka

fg

Asalin hoton, MAHMUD TURKIA/AFP

Bayanan hoto, Wata mata a Tripoli babban birnin Libya na sayar da kayan ƙamshi a tsohuwar kasuwar garin.
fg

Asalin hoton, ANDREW KASUKU/ANADOLU AGENCY

Bayanan hoto, Cikin ƙawa mutane na farin cikin ranar Talotalo ta duniya a garin Mumbasa da ke Kenya, suna ganin yadda ƙananan talotalo ke tsere zuwa cikin ruwa a ranar Juma’a.
fg

Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar wasu masu wasa a kan titi da ake kira da Zinare da Tagullar ƙasa a bakin wani kanti a tsakiyar birnin Johnnesbirg na Afrika ta Kudu.
fg

Asalin hoton, AMR ABDALLAH DALSH/REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Laraba wasu masu wanke gilashi na wanke gilashin ginin babban bankin Masar wanda sabuwar hedikwatarsa ke kusa da al-Qahira.
fg

Asalin hoton, Issouf Sanogo/AFP

Bayanan hoto, Wata mahaifiya ɗauke da jaririn da ta haifa a wani asibiti a Ivory Coast ranar Litinin.
fg

Asalin hoton, MOHAMED MESSARA/EPA

Bayanan hoto, Masu rawa a Tunis babban birnin Tunisia lokacin da ake murnar bikin ranakun Carthage Choreographers da shekara-shekara a ranar Asabar.
fg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasan kwallon kafar Senegal Habib Dialo daga dama yana murnar kwallon da ya ci tare da abokan kwallonsa a wasan sada zumuntar da suka yi da Brazil a ranar Talata. Ƙasar ta bangaren yammacin Afrika ta yi nasara da ci 4-2.
fg

Asalin hoton, DANIEL BELOUMOU OLOMO/AFP

Bayanan hoto, A Kamaru kuwa a ranar Asabar, magoya bayan Jamhuriyar Afrika Ta tsakiya na ta murna gabanin nasarar da aka yi a kansu da ci biyu da ɗaya. Suna fatan ƙasarsu ta je gasar cin kofin ƙasashen Afrika karon farko a tarihi.
fg

Asalin hoton, ALEX DAVIDSON-ICC/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kwana gudana gabanin nan, mai sauya allon kwallayen da aka ci a wajen wasan kurkad na cikin farin ciki a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta maza tsakanin West Indies da Amurka a Zimbabwe
fg

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Bayanan hoto, ‘Yan Najeriya da ke buga wasan gasar kwamfuyuta da GamrX Afrika ke ɗaukar nauyi a Legas a ranar Asabar.
fg

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba magoya bayan ‘yan adawa a Sierra Leon na kira da shugaban hukumar zaɓe na ƙasar Mohamed Konneh ya sauka daga matsayinsa, bayan zargin cin hanci da ake yi masa gabanin fara zaɓen shugaban ƙasa a ranar Asabar.
fg

Asalin hoton, SIA KAMBOU/AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, ‘yan Mali da ke zaune a Ivory Coast na duba jerin sunayen hukumar zaɓe yayin ƙuri’ar sauraren ra’ayin al’umma kan yi wa kunɗin tsarin mulkinsu gyara da shugabanin soji suka nema.
fg

Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA

Bayanan hoto, A ranar Laraba aka yi bikin ranar motsa jiki ta Yoga ta duniya – wani lokaci na daɗewa ana motsa jiki ga masu yi a ko da yaushe a Johannesburg da kuma wasu waurare a faɗin duniya.
fg

Asalin hoton, ALEXANDER HASSENSTEIN/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Tawagar Eswatini ta shiga cikin jerin sauran tawagogi da suke murnar buɗe wasan Olympics a Jamus ranar Asabar.
fg

Asalin hoton, MAJA HITIJ/AFP

Bayanan hoto, Kwana guda bayan nan – Mitchen Prosper na Mauritius ya kammala wasansa na dogon tsalle.