Waiwaye: Nasarar Tinubu da hukuncin kotun koli kan tsofaffin kuɗi

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

Bola Tinubu ya zama sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya

Tinubu

Asalin hoton, FACEBOOK/ BOLA AHMED TINUBU

A cikin makon da ya gabatan ne hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen Najeriya na 2023.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da tsohon gwamnan na jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen bayan samun ƙuri'a miliyan 8,794,726.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ne ke biye masa da ƙuri'a miliyan 6,984,520.

Sai kuma ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu ƙuri'a miliyan 6,101,533.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya zo na huɗu da kuri'u miliyan 1,496,687, kamar yadda INEC ɗin ta bayyana

Za mu ƙalubalanci zaɓen shugaban ƙasa -Atiku Abubakar

Atiku

Asalin hoton, Getty Images

To sai dai bayan ayyana Tijnubu da INEc ta yi ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Atiku Abubakar ya ce dole ne kowa ya ƙalubalanci zaɓen da aka yi na ranar 25 ga watan Fabarairu.

A taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce, abin da ya faru a kan zaɓen fyaɗe ne aka yi wa dimukuraɗiyya.

Kotu ce za ta raba ni da INEC - Obi

Obi

Shi ma ɗan takarar jam’iyyar hamayya ta Labour Party, Peter Obi ya ce shi ne ya ci zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu 2023.

A cewarsa zai bi duk wani matakin shari’a domin ya ƙwato nasararsa.

Mista Obi ya ce wannan ne karon farko da ya fito duniya yake magana tun bayan kaɗa ƙuri’ar da ya yi a zaɓen, saboda haka ya ce duk wani saƙo ko magana da aka danganta da shi a baya ba shi ya fada ba.

"Mun ci zaɓen kuma za mu tabbatar wa da 'yan Najeriya hakan," in ji Obi.

To sai dai a martaninta jam'iyyar APC mai mulki ta ce a shirye take ta haɗu da Peter Obin a kotun da yake iƙirarin zuwa.

Kotun kolin Najeriya

Tsoffin kuɗi

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Juma'ar da ta gabata ne kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al'umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al'umma.

Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.

Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.

Tun da fari gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar da gwamnati ƙara, kuma ƙarar da suka shigar aka yi amfani da ita a matsayin hujja wajen yanke wannan hukunci.

Ƴan bindiga sun sace matan sarki a Jihar Taraba

'yan bindiga

Asalin hoton, AFP

A cikin makon da ya gabatan ne kuma masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa sun kai hari ƙaramar hukumar Ibbi a Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya inda suka sace mutane ciki har da matan Sarkin biyu.

Bayanai sun nuna cewa al'ummomin yankin suna zaune cikin zullumi kan yadda a cikin makon ɓarayin mutanen suka addabe su.

Rahotanni sun ce a ranar Alhamis da daddare ne aka shiga garin aka sace matan Sarkin Kudu guda biyu kuma har yanzu babu labarinsu.