Ƴan ƙwallon premier ta Najeriya huɗu da aka gayyata Super Eages

Lokacin karatu: Minti 3

Ana cigaba da tattaunawa kan jerin sunayen ƴanwasan da sabon kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya, Eric Chelle ya fitar waɗanda za su taka leda a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

Daga cikin ƴanwasan akwai sababbin ƴanƙwallo guda takwas waɗanda ba su taɓa wakiltar ƙasarsu ta Najeriya ba, sai wannan karon da Najeriya za ta fafata da Rwanda da Zimbabwe a wannan watan.

Sababbin gayyatar su ne Papa Mustapha da Ifeanyi Emmanuel Onyebuchi da Christantus Uche da Akor Adams da Tolu Arokodare da Igoh Ogbu da Anthony Dennis da Kayode Bankole.

Sai dai abin da ya ɗauki hankalin mutane shi ne yadda a wannan lokacin an gayyaci ƴan wasan da suke taka leda a gasar premier ta Najeriya domin su wakilci tawagar Super Eagles.

Wannan ya sa BBC ta rairayo ƴanwasan guda huɗu:

Ahmed Musa - Kano Pillars

Ɗaya daga cikin waɗanda aka fi mayar da hankali a game da su shi ne Ahmed Musa, wanda kyaftin ne na tawagar ta Super Eagles, amma ya daɗe ba a gayyace shi ba, wanda hakan ya sa ake tunanin ko dai don ya koma premier Najeriya ne da taka leda.

Wannan ya sa aka fara tunanin ko sabon kocin zai gayyaci shi, ko zai manta da shi.

Amma fitaccen ɗanwasan, wanda yanzu yake ƙungiyar Kano Pillars ta Kano ya samu shiga cikin jerin ƴanwasa na farko da kocin ya fitar.

Ahmed Musa dai ya buga ya Najeriya ƙwallo sau 110, inda ya fi kowane ɗan ƙwallo wakiltar ƙasar.

Kayode Bankole - Remo Stars

Kayode Bankole, mai shekaru 22 matashin mai tsaron gida ne da yake tashe a gasar kofin premier ta Najeriya.

Matashin golan ya fara tsaron gidan ƙungiyar Remo ne a kakar shekarar 2020. Kafin nan ya tsare ragar ƙungiyar Shooting Stars a kakar 2019 zuwa 2020.

An haifi Kayode Bankole a garin Ipokia da ke da ke jihar Ogun.

Ifeanyi Onyebuchi - Rangers International

Onyebuchi ɗan wasan baya ne da yake taka leda a ƙungiyar Rangers International FC da ke jihar Enugu.

Matashin ɗanwasan mai shekara 24 mazaunin jihar Kaduna ne, inda ya fara buga ƙwallo.

Ya taka leda a ƙungiyoyin Plateau United da MFM FC da ƙungiyar FC Shkupi da ke ƙasar Macedonia ta Arewa kafin ya koma Rangers.

Papa Mustapha - Niger Tornadoes

Papa Mustapha Daniel ɗan wasan tsakiya ne da ke taka leda a ƙungiyar Niger Tornados da ke birnin Minna na jihar Neja.

Matashin mai shekara 23 ɗan jihar Legas, kuma ya koma taka leda ne a ƙungiyar Niger Tornados a watan Agustan shekarar 2024.

Kafin ya koma Niger Tornados, ya taka leda a ƙungiyar Adanaspor da ƙasar Turkiyya, sannan ya wakilci tawagar ƴan Najeriya masu taka leda a cikin gida.