Su wane ne ke zaɓen sabon Fafaroma kuma ina suke zaune?

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88 da kuma binne shi a ranar Asabar, manyan limaman kirista daga sassa daban-daban na duniya za su taru a Vatican domin zaɓar wanda zai gaje shi ta hanyar wani tsarin ganawa a asirce da aka saba yi shekaru aru-aru.

Shin ko daga ina ne waɗannan manyan limaman suke, kuma ko ra'ayoyin siyasa na wasu mambobin cocin zai shafi sakamakon zaɓen?

Su wa ne ke da damar kaɗa kuri'a?

A halin yanzu, akwai manyan limaman kirista 252 a majalisar manyan malamai da ake kira College of Cardinals, inda 135 daga cikinsu ke ƙasa da shekaru 80, wanda ke ba su damar kaɗa kuri'a domin zaɓar sabon Fafaroma.

Wannan shi ne adadin manyan limaman kirista mafi yawa masu damar kaɗa ƙuri'a a tarihin cocin Katolika.

Malaman su ne manyan mambobi na limaman cocin Katolika kuma galibinsu ana naɗa su a matsayin bishof-bishof.

Fafaroma Francis ne ya naɗa mafi yawancin manyan limaman da ke da damar kaɗa ƙuri'a wanda jimillarsu ya kai 108 yayin kuma da sauran aka naɗa su ne ta hannun magabatansa, Fafaroma Benedict XVI da St. John Paul II.

Wasu masana na Vatican na ganin cewa Fafaroma Francis, wanda shi ne Fafaroma na farko daga Latin Amurka kuma Fafaroma na farko ba Bature ba tun ƙarni na takwas, ya tsara majalisar malaman ne da gangan domin tabbatar da ci gaba da abun da ya bari.

Yadda lokacin zaɓen ya sauya

Wakilcin nahiyoyi a majalisar manyan malaman ya sauya a lokacin mulkin Fafaroma Francis na tsawon shekaru 12.

A karon farko a tarihi, Turawa ba su ƙara rinjayar yawancin manyan limaman kirista da ke da damar kaɗa ƙuri'a ba, inda a yanzu suna wakiltar kashi 39 cikin 100 na manyan limamai masu zaɓe da ke ƙasa da kashi 52 da suka kasance a shekarar 2013.

Daga cikin manyan limamai 108 masu damar kaɗa kuri'a da Fafaroma Francis ya naɗa, kashi 38 cikin 100 daga Turai suke, kashi 19 kuma daga Latin Amurka da yankin Caribbean, kashi 19 daga yankin Asiya da Pacific, sai kuma kashi 12 daga Afirka ta kudu da Sahara, kashi 7 daga Arewacin Amurka, sannan kashi 4 daga Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Wanda hakan ya nuna adadin waɗanda ba 'yan Turai ba ya kai 73.

Wannan canjin zuwa ga wata cocin Katolika da ta fi wakiltar duniya gaba ɗaya ya samo asali ne daga cikin wata al'ada da ta fara a ƙarni na 19, in ji Dr. Miles Pattenden, wani masani kan tarihin cocin Katolika a Jami'ar Oxford.

Kafin wannan lokaci, kusan manyan limaman dukkaninsu 'yan Turai ne kuma mafi yawansu 'yan Italiya ne.

Pattenden ya ce Fafaroma Francis ya yi imani cewa ya kamata majalisar malaman ta kasance mai wakiltar kowace al'umma ta Katolika kamar yadda zai yiwu, ko da kuwa su ƙanana ne.

Wannan ya bayyana dalilin da ya sa aka naɗa manyan limamai a ƙasashe kamar Mongolia da Aljeriya, da Iran a lokacin mulkinsa maimakon ƙasar Ireland ko Australia, in ji Pattenden.

Shin ko nahiyar da ƴan takara suka fito na da tasiri a zaɓen?

Duk da cewa manyan limaman ba za su faɗa a bainar jama'a cewa yankunan da ƴan takara suka fito na tasiri a zaɓen ba, amma a zahiri hakan na iya yiwuwa in ji Pattenden.

Da yawa daga cikin manyan limamai daga yankin Kudu na Duniya suna ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata a naɗa sabon Fafaroma daga yankinsu, musamman daga Asiya ko Afirka, yayin da manyan malaman Turawa, musamman 'yan Italiya, suna son Fafaroma ya koma Turai.

Haka nan akwai rarrabuwar kai tsakanin manyan limamai da ke zaune a Roma da waɗanda ba sa zaune a can.

Manyan limaman Italiya, wanda suka yi aiki tare na tsawon lokaci, suna da ƙarfi wajen yin zaɓe a matsayin rukuni ɗaya.

Yadda ake zaɓen Fafaroma

A lokacin zaɓen Fafaroma, ana keɓe manyan limaman daga mutanen waje kuma ba su da izinin amfani da wayoyi ko intanet ko jaridu.

Za su zauna a Casa Santa Marta, wani gida mai hawa biyar a birnin Vatican, sannan kowace rana za su yi tafiya zuwa Capella Sistina domin yin zaɓe cikin sirri.

Kowane babban limami zai rubuta zaɓinsa a cikin takardar kuri'a kuma ya sanya ta cikin babban tukunya da aka yiwa kwaliya da zinariya da azurfa.

Kafin a sami wanda ya lashe zaɓen, dole ne ɗan takara ya samu kashi biyu cikin uku na kuri'un.

Idan an samu wanda ya lashe zaɓen, sabon Fafaroman zai bayyana a kan bene a dandalin St. Peter don karɓar matsayin a gaban majalisar manyan limaman,

Zaɓen Fafaroma mafi tsawo a tarihi ya ɗauki shekaru biyu da wata tara, wanda ya fara a shekarar 1268, amma yanzu ana ɗaukar ɗan ƙanƙanin lokaci a ƙalla kwanaki uku wajen zaɓen tun daga ƙarni na 20.

Fafaroma Francis da magabacinsa Fafaroma Benedict XVI an zaɓe su ne cikin kwanaki biyu kawai.

Tun bayan rasuwar Fafaroma Francis, an riga an ba da sunayen wasu masu yiwuwar maye gurbinsa - daga Italiya zuwa Canada, da Ghana da Philippines.