Kotu ta ɗaure ɗan'uwan Pogba kan yunƙurin yi wa ɗanwasan ƙwace

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Lana Lam
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 2
Kotu ta ɗaure yayan tsohon ɗanwasan Manchester Tunited, Paul Pogba, shekara uku a gidan yari bayan samun sa da laifin yunƙurin yi wa ɗan'uwan nasa ƙwace.
Mathias Pogba wanda kotun ta kuma ci shi tarar yuro 20,000 (£16,500), zai yi zaman gidan yarin na shekara ɗaya ne kawai amma zai saka maɗauri a ƙasa mai aiki da lantarki.
Kotun ta kuma samu wasu mutum biyar da laifin ƙwace da sauran laifuka, inda ta yanke musu hukuncin shekara huɗu zuwa takwas a ranar Alhamis.
Paul Pogba mai shekara 31 ya ce "abokansa sun yaudare shi" ta hanyar tsira shi da bindiga a 2022 kuma suka nemi ya ba su yuro miliyan 13. Ya ce ya ba su yuro 100,000.

Asalin hoton, Reuters
Lauyan Mathias Pogba, Mbeko Tabula, ya faɗa wa kafar RMC Sport cewa hukuncin "ya yi tsauri sosai" yana mai cewa "ina ganin za mu ɗaukaka ƙara".
A shekarar da ta gabata ne Paul Pogba ya faɗa wa gidan talabijin na Aljazeera cewa ya yi tunanin yin ritaya daga taka leda saboda yunƙurin yi masa ƙwacen.
"Idan mutum yana da kuɗi dole ne ya yi taka-tsantsan," in ji shi. "Kuɗi na sauya halayyar mutane. Za su iya ruguza iyali. Za su iya haddasa yaƙi."
Mathias Pogba tsohon ɗan ƙwallo ne da ya buga wa ƙungiyoyi kamar Partick Thistle, da Wrexham, da Crewe Alexandra, da Crawley Town. Kulob ɗinsa na ƙarshe shi ne Belfort a Faransa wanda ya bari a 2022.











