Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Akwai waɗanda ba su son rikicin Boko Haram ya ƙare – Zulum
Gwamnan jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya yi zargin cewa akwai waɗanda ke amfana da rikicin Boko Haram.
A hirarsa da BBC gwamnan na Borno ya ce an kasa kawo ƙarshen matsalar Boko Haram ne saboda wasu da ke amfana da matsalar tsaron yankin arewa maso gabashi da yankin Tafkin Chadi ke fama da ita.
“A wannan tafiyar akwai waɗanda ba su son wannan yaƙin ya ƙare domin ba za su ji daɗi ba,” in ji gwamna Zulum.
Sai dai gwamnan na Borno bai bayyana waɗanda yake nufi ba waɗanda yake zargi.
Gwamnan ya ce duk da an samu ci gaba a yaƙi da matslar tsaron, amma a yanzu mayaƙan na Boko Haram sun kwararo daga Chadi bayan an fatattako su daga can, har ma sun kashe sojojin Najeriya da dama.
Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sun daɗe suna kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya duk da ayyukan soji a yankin.
Mayakan sun kashe mutane da dama tare da raba dubban mutane da gidajensu.
Ko a ƙarshen a watan Nuwamba mayaƙan sun kai hari a wani sansanin sojin Najeriya a yankin ƙaramar hukumar Kukawa inda suka kashe sojoji uku yayin da kuma aka kashe mayaƙan sama da 10.
Ko a kwanan baya ma ba mayaƙan sun kai hari a yankin Gubio inda suka kashe sojoji tare da jikkata wasu da dama.
A watan da ya gabata ne shugaban Chadi ya yi barazanar ficewa daga rundunar hadin guiwa ta ƙasashen Tafkin Chadi wadda ya ce ta gaza kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Kusan sojojin Chadi 40 ne aka kashe a wani harin da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai a karshen watan Oktoba.
Gwamna Zulum ya ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin al’umma da kuma bayar da goyon baya ga jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar Boko Haram a yankin.