Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin Boko Haram a babban masallacin Juma'a na Kano: 'Na ɗauka tashin ƙiyama ne'
Ɗaya daga cikin hare-haren tashin hankali da jihar Kano ta taɓa gani a tarihi, shi ne lokacin da ƴan Boko Haram suka tayar da bama-bamai da harbin mai uwa da wabi a Babban Masallacin Juma'a na Birni.
Farmakin na ranar 28 ga watan Nuwamban 2014 na cikin miyagun hare-haren ta'addanci da aka gani a tsawon shekarun da Boko Haram ta yi harkokinta ta gama a babban birnin kasuwancin na arewacin Najeriya.
Hukumomi a lokacin sun ce mutane sama da 100 aka kashe a tsararren harin rashin imani da aka kai ana tsaka da taron sallar Juma'a.
Kodayake akwai yiwuwar adadin mutanen da aka kashe a harin ya fi haka.
Rayuwar mutane da yawa ta canza sanadin hare-haren da Boko Haram riƙa kai wa kan jami'an tsaro da fararen hula, talakawa da sarakuna, Musulmai da Kiristoci a faɗin Kano.
Hukumomi a lokacin sun ɓullo da matakai iri daban-daban don katse hanzarin mahara kamar taƙaita zirga-zirga da hana fitar dare a wasu lokuta da datse hanyoyi da kafa shingayen bincike da caje masu shiga wuraren ibada da sauransu.
Sai dai bayan waɗancan miyagun al'amura da Kano ta gani a baya, mutane yanzu sun fuskanci gaba, inda sannu a hankali harkoki ke ci gaba da farfaɗowa.