Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lamine Yamal ɗanbaiwa ne - Hansi Flick
Kocin Barcelona Hansi Flick ya yaba wa matashin ɗanwasa Lamine Yamal bayan ƙoƙarin da ya yi a wasan suka tashi 3-3 da Inter Milan a gasar zakarun Turai ta Champions League.
Inter ce ta fara cin ƙwallo biyu a wasan na ranar Laraba ta ƙafar Marcos Thuram da Danzel Dumfries, kafin Lamine ya farke ta farko da ƙwallonsa mai ƙayatarwa.
Daga baya kuma Ferran Tores ya farke ta biyu, sannan Sommer na Inter ya ci gidansu.
"Danwasa ne na musamman, kuma na sha faɗa kafin yanzu cewa ɗan baiwa ne," in ji Flick bayan tashi daga wasan.
Yamal ya yi ƙoƙari sosai a wasan, inda ya shot sau shida kuma ya dinga jan ƙwallo zuwa yadi na 18 na Inter domin ƙarfafa wa abokan wasansa gwiwa.
Ya ci ƙwallo biyar cikin wasa 12 da ya buga a gasar ta Champions League ta bana kuma ya bayar aka ci uku. A La Liga kuma, ya ci shida ya bayar an ci 12 cikin wasa 30.
Ya fara taka wa babbar tawagar Barca leda a kakar wasa ta 2022-23, inda ya buga mata wasa ɗaya a La Liga bayan ya fito daga kwalejin horar da matasa ta kulob ɗin.
Ya ci ƙwallo biyar a La Liga a kakar da ta gabata kuma ya taimaka aka ci wasu biyar. Haka ma a Champions League.
A ranar Talata mai zuwa ne Barce za ta ziyarci gidan Inter domin buga falle na biyu na wasan zagayen kusa da ƙarshe, inda za a tantance wadda za ta kai wasan ƙarshen a cikinsu.