'An lalata komai': Sojojin Ukraine sun bayar da labarin tashin hankalin da suka gani a fagen daga

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jonathan Beale
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Ukraine
- Marubuci, Anastasiia Levchenko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Ukraine
- Lokacin karatu: Minti 6
Sojojin Ukraine da ke fafatwa a yankin Kursk na kasar Rasha sun bayyana abubuwan da suka faru a yankin a matsayin 'tashin hankali' yayin da suke janyewa daga fagen daga.
BBC ta samu bayanai masu yawa daga sojojin Ukraine, waɗanda suka bayyana "mummunan" yanayin da ya sanya suka janye daga bakin daga yayin da ake musu ruwan wuta, inda jerin hare-haren jirage marasa matuƙa na Rasha suka lalata makamansu.
Dakarun sojin Ukraine da ke yaƙi a yankin Kursk na Rasha na bayyana halin da suke ciki a matsayin "fim ɗin shan jini" yayin da suke tserewa daga filin daga.
BBC ta ji labarai masu yawa na sojojin da suka ce an janye saboda hare-haren Rasha, sannan jirage marasa matuƙa na Rasha sun lalata jerin gwanon motocin yaƙi da dama.
Sojojin da suka yi magana ta kafar sada zumunta, mun sauya sunayensu domin kare su daga wata barazana. Wasu sun ce "komai ya rushe" bayan Rasha ta ƙwace Sudzha, gari mafi girma daga hannun Ukraine ɗin.
Haramcin da Ukraine ta saka na hana zuwa filin dagar na nufin ba zai yiwu a samu cikakken bayanin abin da ke faruwa ba. Amma dai ga yadda sojojin Ukaraine biyar suka bayyana yanayin.
Volodymyr: 'Jirage marasa matuƙa babu ƙaƙƙautawa'
A ranar 9 ga watan Maris, Volodymyr ya tura wa BBC saƙo ta Telegram cewa har yanzu yana Sudzha, inda suka fuskanci "fargaba da kuma guduwa daga filin dagar".
Dakarun Ukraine "na ƙoƙarin guduwa. Wasu daga cikinsu ma jiragen Rasha sun ƙone su a kan hanya. Ba zai ma yiwu ba mutum ya motsa da tsakar rana".
Hanya ɗaya ce suka dogara da ita inda ake jigilar mutane da kayan yaƙi, wadda ke tsakanin Sudzha da kuma yankin Sumy na Ukraine.
Volodymyr ya ce wata ɗaya da ya wuce sukan iya bin hanyar lafiya ƙalau. Amma zuwa 9 ga Maris "wuta ce kawai ke sauka a kanta - jirage marasa matuƙa a kodayaushe. Kana iya ganin jirgi biyu ko uku cikin minti ɗaya," in ji shi.
Jim kaɗan kafin Rasha ta karɓe Sudzha, Volodymyr ya ce ana kai wa dakarun Ukraine hari ta ɓari uku.
Maksym: Tarkacen ababen hawa sun mamaye hanya
Zuwa 11 ga watan Maris, dakarun Ukraine sun yi ta faman hana katse titin da dakarun Rasha ke yi, a cewar saƙonnin da Maksym ya turo ta Telegram.
"'Yan kwanakin da suka wuce, an umarce mu mu bar wurin da muke karewa ta hanyar guduwa cikin tsari," in ji shi.
Ya ce Rasha ta tattaro dakaru masu yawa domin ƙwace garin ciki har da sojojin Koriya ta Arewa masu yawa".
Ƙwararru kan harkokin yaƙi na cewa Rasha ta tattara kusan dakaru 70,000 don ƙwato Kursk - har da kusan dakaru 12,000 daga Koriya ta Arewa.
Sannan ta tura rundunar jiragenta marasa matuƙa mafi ƙwarewa, ga kuma nau'in first-person-view (FPV) "duka domin ragargaza hanyar da ake iya yin jigila".
Cikinsu akwai jiragen da ke aiki da layin sadarwa na fibre-optic - wanda ba zai yiwu a iya daƙile su ba ta hanyar katse layi.
Maksym ya ce sanadiyyar haka "maƙiyan sun yi nasarar lalata gomman kayan aiki", kuma wannan ɓaraguzan sun jawo cunkoso a kan hanyoyin yin jigilar kaya".

Asalin hoton, EPA
Anton: Matsalar guduwa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abin da ya faru a ranar 11 ga watan Maris, ya zama kamar "bala'i", kamar yadda Anton ya faɗa.
Wannan ya yi magana ne da BBC yayin da yake hedikwatar yaƙi ta Kursk.
Shi ma ya bayyana ɓarnar da jiragen FPV ɗin ke yi.
"A da mu ne ke da ƙarfi a ɓangaren jiragen, amma yanzu babu," a cewarsa.
Anton ya ce an katse hanyoyin jigilar kayayyaki. "Babu wasu kaya da ake iya kaiwa - babu makamai, ko harsasai, ko abinci da ruwa ba a iya kaiwa".
Anton ya ce ya samu ya gudu daga Sudzha a ƙafa da tsakar dare - "Mun sha tsallake rijiya da ba. Kodayaushe jirage marasa matuƙa na saman kanmu."
Sojan ya yi hasashen cewa Ukraine za ta rasa duka ikon da take da shi a Kursk, "amma kuma idan ana maganar yaƙi ne, dakarun da ke Kursk sun gaji. Babu wani amfanin cigaaba da zama a can".
Shugabannin Turai na cewa Ukraine ta kai harin ne da dakaru kusan 12,000, mafi yawansu su ne mafiya ƙwarewa a ƙasar ɗauke da makaman da ƙasashen suka bayar.
Masu shafukan intanet a Rasha sun sha wallafa bidiyon yadda dakarunta ke lalatawa da kama wasu makaman.
A ranar 13 ga watan Maris, Rasha ta ce ita ce "ke iko da yanayin da Kursk ke ciki" kuma dakarun Ukraine "sun gudu sun bar" kayayyakinsu masu yawa.
Dmytro: Tsallake rijiya da baya
Cikin saƙonnin da ya aiko ranar 11 da 12 ga wata, Dmytro ya kwatanta guduwar da sojojin Ukraine suka yi daga fage dagar da wani "fim na shan jini".
"Tituna sun cika da ɓaraguzan motoci, motoci masu sulke, da na shiga daji wato All Terrain Vehicles. Akwai dakaru da yawa da aka kashe ko aka raunata."
Ya bayyana yadda tsallake rijiya da baya lokacin da motar da yake ciki ta hantsila saboda hari. Shi da abokan tafiyarsa sojoji na ƙoƙarin janyo motar tasa lokacin da wani jirgin daban ya kawo musu hari.
Bai samu motar ba amma ya jikkata ɗaya daga cikinsu. Ya ce sai da suka ɓuya a daji tsawon awa biyu kafin a ceto su.
Ya ce 'yan Ukraine da yawa sun tsere ne a ƙafa inda suke yin "tafiyar kilomita 15 zuwa 20".

Asalin hoton, Reuters
Artem: 'Mun fafata kamar zakuna'
Soja na biyar ya ɗan nuna ƙwarin gwiwa game da lamarin. A ranar 13 ga Maris Artem ya turo saƙo daga wani asibitin soji, inda ake kulawa da shi bayan ɓaraguzai sun ji masa rauni a harin jirgi maras matuƙi.
Artem ya ce ya fafata a yammaci - a kusa da ƙauyen Loknya - inda dakarun Ukraine suka yin tunga kuma suka fafata "kamar zakuna".
"Abu ne mai muhimmmanci cewa har yanzu dakarun Ukraine na iya kare yankunan da suka hana sojin Rasha shiga Sumy," a cewarsa.

Asalin hoton, Getty
Me ya rage wa Ukraine yanzu?
Babban kwamandan Ukraine, Oleksandr Syrskyi, ya dage cewa dakarunsa sun koma "wasu wurare ne da ɗan fi", za su ci gaba da zama a Kursk "har zuwa lokacin da ya zama dole".
Ya ce Rasha ta ji jiki inda suka kashe mata dakaru 50,000 a hare-haren.
Sai dai kuma yanayin na yanzu ya sha bamban sosai da watan Agusta da ya gabata.
Masu hasashen yaƙi sun ce biyu cikin uku na garuruwan da Ukraine ta mamaye Rasha ta ƙwace su.
Duk wani fata na Ukraine domin amfani da Kursk a matsayin musayar wasu yankunanta da Rasha ta mamaye yanzu babu shi.
A makon da ya gabata, Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce ya yi imanin hare-haren Kursk "sun cimma manufarsu" ta hanyar tilasta wa Rasha janye wasu dakaru daga gabashin ƙasar wanda hakan ya sa dakarunsa suka samu sauƙi a yankin Pokrovsk.
Amma kuma har yanzu babu tabbas game da irin asarar da hakan ta jawo.











