Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gidan yarin Saydnaya na Bashar al-Assad da ake yi wa lakabi da mayanka
- Marubuci, Matt Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun bayan faduwar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Syria a ranar Lahadin da ta wuce, fararen hula a kasar na ta fatan samun labarin 'yan uwansu da aka kulle a gidan yarin Saydnaya mafi tsaurin tsaro da ya yi kaurin suna.
A shekarun 1980 aka samar da gidan yarin a wani ƙaramin gari da ke da nisan kilomita 30 daga arewacin birnin Damascus.
Gidan yarin Saydnaya, shi ne inda iyalan Assad ke tsare abokan hamayya a lokacin mulkinsu tsawon shekaru.
Gidan yarin da kungiyoyin kare hakkin dan'adam suka yi wa lakabi da mayanka, ana tsare da dubban mutane a ciki inda ake azabtar da su da kuma yanke musu hukunci kowanne iri ne tun shekarar 2011.
Ba kowa ne ya san yanayin gidan yarin ba saboda komai an yi shi ne cikin sirri, kuma ba a taba ganin hoton cikin gidan yarin ba.
Ana samun bayanan gidan yarin ne kadai a lokacin da ake hira da tsoffin masu gadin wajen ko kuma wadanda aka tsare.
Amma bayanan da ake samu daga wajen kungiyoyin kare hakkin dan'adam da kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka na bayar da dama a fahimci yadda cikin gidan yarin yake, wanda ya zamo wani waje da Assad ke aikata zalinci da kuma daukar fansa.
Mayankar gidan yari
A shekarar 1987 ne aka fara kai mutane gidan yarin na Saydnaya wato bayan shafe shekaru 16 da fara mulkin tsohon Shugaba Hafeez al-Assad, mahaifin Bashar al-Assad.
A lokacin da gidan yarin ya fara aiki, akwai wurare biyu na tsare mutane. Akwai wanda ake cewa farin gida, wanda kungiyoyin kare hakkin dan'adam suka ce an kebe shi domin a rika kulle sojoji da kuma mutanen da ake ganin ba sa yi wa gwamnati biyayya. Gini ne da ke da lankwasa da aka gina a kudu maso gabashin gidan yarin.
Sai jan gida, inda nan ne ainihin wurin da ake tsare mutane, shi ne kuma wajen da ake tsare 'yan hamayya. Shi kuma ginin yana da surar gwafa.
Akan ajiye mutum 10,000 zuwa 20,000 a cikin gine-ginen biyu, a cewar kungiyoyin kare hakkin dan'adam din da suka tattauna da fursunonin da aka saka.
Wasu bidiyo da aka rika yadawa a kafafan sada zumunta tun a ranar Lahadi, sun nuna wani katon daki a gidan yarin mai cike da kamarorin tsaro da dama wanda ke hasko lungu da sakon gidan yarin.
Wani rahoton kungiyar kare hakkin dan'Adam ta Amnesty International a 2017, ya ambato tsoffin masu gadin gidan yarin na cewa bayan yakin basasar kasar a 2011, an kwashe duk fursunonin da aka tsare a bangaren farin gida inda aka maye gurbinsu da wadanda aka kama a lokacin zanga-zangar da aka yi ta nuna adawa da gwamnatin Bashar al-Assad.
Wani tsohon jami'i ya shaida wa Amnesty cewa, tun bayan 2011, gidan yarin ya komababban gidan yarin 'yan siyasa.
Kungiyar kare hakkin dan adam din ta kuma ambato tsoffin fursunonin da aka tsare a gidan yarin a bangaren jan gida na cewa su ne wadanda ake azabtarwa ciki har da duka da fyade da kuma hanasu abinci da magani.
Akwai wani daki a cikin karkashin ginin farin gida wanda wadanda Amnesty ta zanta da su ke kira a matsayin wajen da ake kashe mutane, ana kai mutanen da aka tsare a jan gida zuwa wannan dakin a rataye su.
Wani tsohon mai gadin wajen ya ce, ana kai sunayen wadanda za a kashe daga jan gida ne a lokacin da ake cin abincin rana.
Daga nan ne sai masu tsaron wajen su kwashe wadanda sunansu ya fito a cikin jerin sunayen su kai su wanann dakin wanda ke cin mutum 100 kuma daga lokacin an daina dukansu da sauran azabar da ake musu.
Yawanci ana kai mutanen da aka dauke daga jan gida ne a cikin dare musamman idan dare ya raba.
Bayan a mai su sai a rufe fuskokinsu a kai su wannan dakin da ake rataye su.
A cewar Amnesty, a shekarar 2012 aka kara girman dakin.
Amnesty ta ce, bayan kawo karshen gwamnatin Assad, wasu hotunan bidiyo da 'yan tawayen da suka kifar da gwamnatin Assad suka yada an ga gwamman igiyoyin da ake rataye mutane a dakunan da ke gidan yarin Saydnaya.
Kungiyoyin kare dan adam sun kiyasta cewa an kashe fursunoni sama da dubu 30 a gidan yarin wasu ta hanyar rataya wasu saboda ukubar da ake musu wasu kuma sakamakon samun kulawar da ta kamata a lokacin da suke rashin lafiya.A cewar wasu daka tsare a wajen sun ce a tsakanin shekarun 2018 da 2021, an kashe fursunoni 500.
A 2017 ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi ikirarin cewa mahukunta a Syria sun gidan wajen binne mutane a bangaren gidan yarin inda ake binne fursunonn da aka kashe ko suka mutu.
Tsauraran matakan tsaro
A tsawon tarihin gidan yarin, a kewaye yake da cikakken tsaro.
A wajen gidan yarin akwai sojoji 200 na rundunar sojin kasar da ke gadin wajen, da jami'an leken asiri 250, da 'yan sanda, a cewar wani rahoton wata kungiyar kare hakkin dan'adam ta AMDSP.
An zakulo dakaru daga runduna ta 21 ta sojojin kasar domin su kare gidan yarin saboda biyayyarsu ga gwamnatin kasar.
Tun bayan faduwar gwamnatin Assad aka bukaci fararen hula da su guji bi ta gefen gidan yarin, saboda akwai kungiyoyin kare hakkin dan'adam din da suka ce an yi binne-binne a kewayensa.
Wasu hotuna da kungiyar sa kai ta White Helmet a Syria ta fitar sun nuna yadda aka zagaye katangar gidan yarin da wayoyin karfe.
A kodayaushe dai gwamnatin Assad na musanta zarge-zarge da ake mata musamman daga kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen duniya tana mai cewa duk abin da ake fada a game da gidan yarin zancen kanzon kurege ne.
Amnesty International ta ce iyalan mutanen da ake zargin ana tsare da su a gidan yarin na Saydnaya, sun ce sakamakon faduwar gwamnatin Assad, yanzu za su son makomar 'yan uwansu na ko suna gidan yarin ko kuma ba sa nan.