An yi babbar zanga-zangar nuna goyon bayan juyin mulki a Nijar

Dubban mutane ne suka gudanar da maci ranar Alhamis a Niamey, babban birnin Nijar don nuna goyon baya ga juyin mulkin da ya kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokraɗiyya.

Ana zanga-zangar ne yayin da damuwar da ake ita game da tsaro ke ƙaruwa a tsakanin ƙasashen Yamma.

Masu zanga-zanga a tsakiyar birnin Niamey, wasunsu na kaɗa manyan tutocin Rasha, suna rera taken ƙin jinin Faransa a lokacin gangamin, wanda aka kira don bikin samun 'yancin kan ƙasar daga tsohuwar uwargijiyarta Faransa a 1960.

Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na Nijar sun yi kira ga al'ummar ƙasar su yi watsi da takunkuman karya tattalin arziƙi da Ecowas ta sanya wa Nijar.

Ƙungiyar Ecowas dai ta ce za ta yi amfani da ƙarfin soji matuƙar masu juyin mulkin ba su mayar da Bazoum kan karagar mulki ba.

Duk da wannan nuna goyon baya da fararen hula ke yi wa sojojin, akwai 'yan Nijar masu yawa da ke adawa da juyin mulkin.

Wasu na zargin cewa sosjojin ne suka kitsa zanga-zangar domin gudun kawar da su daga kan mulki.

To amma yanzu a ƙoƙarinsu na kafa hujja kan juyin mulkin, sojojin na yunƙurin harzuƙa batun ƙin jinin Faransa.

Abin da kuma ya faru kenan a Mali da Burkina Faso, inda jagororin mulkin sojin ke ƙara ƙulla ƙawance da Rasha.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa ɗaruruwan matasan riƙe da tutocin ƙasar Rasha sun taru a dandalin samun 'yanci da ke tsakiyar birnin Yamai.

Issiaka Hamadou ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya ce ''magana ce a kan matsalar tsaro, muna buƙatar taimakon sojoji, kuma muna maraba da shi daga ko'ina ne ba lallai sai Rasha kaɗai ba, ko China ko Turkiyya ne, matuƙar za su taimaka mana''.

"Ba ma son Faransa, waɗanda ke sace mana ma'adanai, tun cikin 1960 suke nan kuma babu abin da ya sauya'', in ji shi.

Faransa na da dakarun soji kimanin 1,500 a Nijar a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi na yankin Sahel.

"Na kasa samun aiki bayan kammala karatu a ƙasar nan, saboda gwamnatin Bazoum da ke samun goyon bayan Faransa,'' in ji wani matashi da ya bayyana sunansa da Oumar.

Masu goyon bayan gwamnatin sojin ƙasar na cewa Faransa ta kasa magance musu matsalar masu iƙirarin jihadi, yayin da suke ganin Rasha ce ta fi cancanta da ƙulla ƙawance.

Biden ya buƙaci a gaggauta sakin Bazoum

A ranar Alhamis ne kuma, Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga sojoji masu mulki su gaggauta sakin hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum wanda aka zaɓa a turbar dimokradiyya.

"Ina kira da a gaggauta sakin shugaba Bazoum da iyalansa, domin kare martabar dimokradiyyar Nijar," kamar yadda Biden ya bayyana cikin wata sanarwar da ya fitar kan cikar Nijar shekara 63 da samun 'yancin kai.

Ya ci gaba da cewa "A wannan mayuwacin lokaciI, Amurka na goyon bayan Nijar domin martaba gomman shekarun da muka kwashe muna mutunta juna ta fuskar dimokradiyya da taimakon gwamnatin farar hula''.

Shugaban dakarun da ke tsaron fadar shugabna ƙasar ne ya jagoranci kifar da gwamnatin Bazoum cikin makon da ya gabata, a wani juyin mulkin soji da Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Turai suka yi Allah wadai da shi.

Shugaban na Amurka ya ce "Al'ummar Nijar na da 'yancin zaɓar shugabanninsu, sun kuma yi hakan ta hanyar sahihin zaɓe, don haka dole a martaba zaɓinsu''.

Mohamed Bazoum ya zama shugaban ƙasar Nijara a shekarar 2021, bayan da ya samu nasara a zaɓen da gwamnatin farar hula ta karɓi mulki a hannun farar hula karon farko a tarihin ƙasar.

A ƙarshen makon jiya ne dai shugabannin ƙasshen kungiyar Ecowas suka bai wa sojojin Nijar din wa'adin mako guda su mayar da mulki hannun Bazoum ko su fuskanci fushin sojojin ƙungiyar.