Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ce-ce-ku-ce a kan hukuncin 'cakumar mace daƙiƙa 10 ba iskanci ba ne'
- Marubuci, By Sofia Bettiza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .
- Aiko rahoto daga, BBC News, Rome
Shin yana iya zama laifin cin zarafin lalata, idan wani ya auka wa mutum da cakumar iskanci tsawon daƙiƙa goma?
Matasa da yawa a ƙasar Italiya na bayyana ɓacin rai a shafukan sada zumunta bayan wani alƙali ya wanke wani jami'in makaranta daga laifin taɓa wata matashiya, saboda kawai bai shafe tsawon lokaci yana shafawar ba.
Lamarin ya shafi wata ɗaliba ce 'yar shekara 17 a wata babbar makaranta da ke birnin Roma.
Ta bayyana yadda kawai tana cikin hawa bene don zuwa aji da wata ko wani ƙawa ko aboki, lokacin da ta ji wandonta ya saluɓe, kuma sai ta ji hannu ya kai kan mazaunanta inda ya kama ɗan duros ɗin ta.
"Abar ƙauna, Kin san dai wasa nake yi ko," mutumin ya faɗa mata lokacin da ta juyo ta dube shi.
Bayan faruwar lamarin, wanda ya faru a cikin watan Afrilun 2022, ɗalibar ta kai ƙorafi a kan jami'in Antonio Avola mai shekara 66 ga 'yan sanda.
Ya amsa cewa ba shakka ya taɓa ɗalibar ba tare da yardarta ba, amma dai ya ce duk a cikin raha ne.
Wani mai gabatar da ƙara a Roma ya nemi kotu ta ɗaure jami'in tsawon shekara uku da rabi a gidan yari, sai dai a wannan mako, kotu ta wanke shi daga duk tuhume-tuhumen cin zarafin lalata.
A cewar alƙalan, abin da ya faru "bai kai laifi ba" saboda cakumar ƙasa da daƙiƙa goma ce kawai.
Tun daga nan ne hukuncin, palpata breve - 'yar cakuma - ya karaɗe shafukan sada zumunta yana tashe a dandalin Instagram da TikTok a ƙasar Italiya, tare da #10secondi.
Italiyawa sun riƙa wallafa bidiyo suna kallon kyamara su yi shiru kawai suna tattaɓa tsiraicin jikinsu tsawon daƙiƙa goma.
Sau da yawa, bidiyon ba shi da daɗin gani, sai dai kawai suna yi ne don nuna yadda mutum zai iya ji idan ya shafe tsawon daƙiƙa goma a irin wannan yanayi.
Na farko Paolo Camilli, jarumin wani fim mai suna White Lotus ne ya wallafa, kuma tun daga nan sai dubban mutane suka bi sawu.
Akwai ma bidiyon da Chiara Ferragni, 'yar ƙasar Italiya mafi shaharar tasiri a shafukan sada zumunta da take da mabiya 29.4 a shafin Instagram.
Shi ma wani, Francesco Cicconetti ya rubuta a TikTok: "Wane ne ya yanke hukuncin cewa daƙiƙa goma ba lokaci ba ne mai tsayi? Wane ne ya ƙididdige daƙiƙoƙin, lokacin da ake cin zarafin matashiyar?"
"Maza ba su da 'yancin taɓa jikin mace, ko da tsawon daƙiƙa ne - balle ma a ce daƙiƙa biyar ko goma."
Ya ci gaba da cewa hukuncin alƙalan na wanke jami'in makarantar ya nuna yadda ake ba da ɗaurin gindi ga masu cin zarafin lalata a tsakanin al'ummar Italiya.
Wani labari da aka wallafa a shafin Instagram na Freeda ya ce: "Wannan hukunci sakarci ne. Tsawon lokacin cin zarafin lalata bai kamata ya rage girman abin da aka aikata ba."
Sai dai a cewar alƙalai, jami'in makarantar bai daɗe ba. Ya yi cakumar ne ɗan lokaci kaɗan, abin da ya yi "dabarbarcewa ce kawai ba tare da nuna sha'awa ba".
"Alƙalai sun yanke hukunci raha ce? To, ni dai a gare ni, ba wasa ba ne," ɗalibar ta faɗa wa jaridar Corriere della Sera.
"Jami'in ya zo ne ta baya ba tare da ya ce min uffan ba. Kawai sai ya sa hannu a cikin wandona, kafin wani abu kuma ya zurƙuma cikin ɗan duros ɗina.
"Ya cafki mazaunaina. Sannan, sai ya damƙa, ya ja ni - har na ji zafi a tsiraicina. Ni, a wajena wannan ba wasa ba ne. Wannan ba haka ya kamata a ce tsoho ya yi 'wasa' da matashiya ba."
"Cafkar 'yan daƙiƙoƙi da jami'in ya yi mini, ta isa ta sanya har na ji ɗumin hannunsa a jikina."
Ta ce ba shakka ta ji tamkar an ci amanarta - daga makarantarta da tsarin shari'ar.
"Har na fara jin cewa ban yi daidai ba da na yi amanna da hukumomi. Wannan ba adalci ba ne."
Dalibar ta bayyana fargabar cewa hukuncin alƙalan zai iya hana 'yan mata da mata fitowa suna kai ƙorafi idan an far musu da irin wannan cin zarafi.