Amurka za ta bai wa Philippines kariya a tekun kudancin China

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Shuagaba Biden ya yi alƙawarin bayar da kariya ga Philippines, yayin da jiragen ruwanta na jigila ke ci gaba da fuskantar hari daga China, a tekun kudancin Chinan.
An riƙa samun harin da kuma karo da juna tsakanin jiragen ruwan China da na Philippines a cikin tekun, kuma Mr Biden ya ce, Amurka za ta ƙaddamar da yarjejeniyar taimakon juna da ke tsakanin ta da Manila, idan aka sake kai wa jiragen hari.
A ganawar da ya yi da shugaba Ferdinand Marcos Jr da Firaiministan Japan, Fumio Kishida a fadar White House, Mr Biden ya jaddada goyon bayan Amurka gare su, irin tabbacin da ya bai wa Isra’ila sa’oi 24 da suka gabata.
Shugaba Biden ya ce a shirye Amurka take ta tallafawa ƙawayen ta.
Ya ce: "A yau an buɗe sabon babi a tarihin tarayyar mu, a karon farko an gudanar da taron shugabannin Amurka da Japan da kuma Philiphines. Nan da shekaru masu zuwa za a kafa wani tarihin na alaƙa tsakanin ƙasashen mu uku. A tare, a yau mun ƙulla haɗaka domin cimma nasarar kafa wannan tarihi nan gaba."
Shi ma shugaba Marcos Jr wanda ya bayyana gamsuwa da haɗakar, ya sanar da irin fatan sa game da shiga haɗakar.
Ya ce: "Mun nemi zaƙulo hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin mu, da karfafa yanayi a biranen mu, da kuma inganta walwalar jama’ar mu. Wannan zai wanzar da zaman lafiya mai ɗaurewa a duniya, musamman don amfanin ƴan baya. Taron na yau wata dama ce ta tsara makomar mu, da kuma yadda muke fatan cimma manufar mu a tare."
Mr Biden dai ya mayar da hankali wajen neman inganta alaƙa tsakanin Amurka da ƙasashen Asiya, saboda hamayyar da ke tsakanin ta da China.













