Yadda ‘yan fashin daji suka mayar da wasu mazauna kauyukan jihar Katsina bayi

'Yan fashin daji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan fashin daji sun mamaye makarantu da dama

Bayanai daga Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya na nuna yadda 'yan fashin daji suka mayar da wasu mazauna kauyuka bayi inda suke gallabarsu da hare-hare.

Girmar matsalar hare-haren da ‘yan fashin daji suke kai wa kauyuka a jihar ta Katsina ya wuce yadda ake tsammani.

A baya, sai da 'yan fashin daji suka hallaka wani babban jami'in 'yan sanda tare da kai wa kwambar motocin shugaban kasa hari a Katsina.

Game da haka ne wasu dattijan gari a ƙarƙashin wata kungiya mai suna Shirin Tabbatar da Tsaro ga al'ummomin Katsina suka yi kira ga duk wani dan kasa nagari ya ba da gudunmawa a yaki da 'yan fashin daji.

Dattijan sun ce baya ga kashe kashe da satar dukiya da shanu , abin ya kai ga cin zarafin mata.

Daya daga cikin jagororin wannan kungiya, Dr. Bashir Kurfi, ya shaida wa BBC cewa shi ganau ne game da irin ta'asar da ‘yan fashin dajin suke aikatawa.

“A yanzu za ka ga an zo an shigo gari an dauki matan aure ko a tada su a wurin a yi musu fyade. Yanzu ma akwai garuruwa da yawa inda barayi za su zo su yi maka waya kai kana maigida a ce ka je ka kai matarka ko diyarka su maido ta bayan sati guda.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

“Akwai wadanda muka taba kai wa asibiti, mata tara ne kuma ‘yan bindiga 40 sun rika yi musu fyaden taron-dangi. A karshe masu asibitin cewa suka yi a kai matan asibitin yoyon fitsari”.

Akwai rashin maida hankali a fadan da ake yi da ‘yan fashin daji

Kungiyar dattijan ta nuna damuwa a kan yadda ‘yan fashin dajin ke ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Dr Bashir Kurfi ya yi zargin cewa akwai rashin mayar da hankali daga wurin jami'an gwamnati.

 "Mutanen dai a kan babura suke tafiya. Mashin ba allura ba ne, ina suke samun mashin-mashin? Ina suke samun yawan bindigogi da suke da su? Sannan ga kwayoyin da ake shigowa da su? Shin me ke faruwa cewa har yanzu abubuwan nan an kasa shawo kansu?

 “Mu fahimtarmu tunda muka shigo tun da mu ba mutanen gwamnati ba ne, mun gane cewa akwai matsaloli da yawa a cikin gwamnatocin jihohi.

''Ma’aikatan za ka ga kamar abun ba ya cikin zuciyarsu watau babu mayar da hankali a yakin da ake yi da ‘yan fashin daji”, in ji shi.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa a kan yadda wasu gwamnatocin jihohi ke sasantawa da wasu jagororin ‘yan fashin daji ba tare da sun samar da wani shiri ko tsari a kan yadda za a taimaka wa wadanda aka cutar ba.

 “Za ka ga cewa su tunaninsu shi ne kullum gara ayi sasanci da barawo, toh duk sasanci nan da ake yi da barayi ba wanda ya taba tunanin wadanda aka cutar da su. Duk jihohin da na sani ba bu inda aka samar da wani shiri na musaman domin taimaka musu”, in ji Dr Kurfi.

'Yan fashin daji sun mamaye makarantu da dama

Kungiyar dattijan ta ce a halin yanzu ba bu wata makaranta da ke aiki a kauyukan jihar Katsina. Ta ce ‘yan fashin dajin sun maida makarantu sansanoninsu.

A cewar Dr Bashir Kurfi '‘yan fashin dajin na kwace gonakin mutane inda suke sa su su yi musu noma.

“Madugun ‘yan fashin dajin zai je wani kauye duk yaranshi za su shiga gidajensu kuma sai ku fita ku je ku sa wasu ‘yan rumfuna inda za ku zauna kuma ku zauna da su, su yi ma ‘ya'yanku fyade su kwashe duk dukiyar da ke gare ku kuma yanzu su ne suke yi musu noma, sun maida su kamar yadda ka san bayi na da," a cewar dattijon.