Wace ƙungiya ce G20 kuma me ya sa take da muhimmanci?

Shugabannin ƙasashe da firaiministoci daga sassan duniya za su haɗu a taron ƙungiyar G20 na shekara-shekara, wanda za a yi a Delhi babban birnin Indiya tsakanin 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

Babban abin da za a tattauna a taron wannan shekarar shi ne cigaba mai ɗorewa, amma ana sa ran za a tattauna rikicin Ukraine a gefe guda.

Wace ƙungiya ce G20?

Ƙungiyar G20 wata tawagar ƙasashe 20 ce waɗanda ke zaunawa su tattauna kan tattalin arziƙin duniya.

Su ne ke samar da kashi 85 cikin 100 na harkokin tattalin arziƙin duniya kuma su ne ke samar da kashi 75 cikin 100 na kasuwancin duniya.

Su ne ke da biyu cikin uku na al'umar duniya.

Mambobin ƙungiyar su ne Tarayyar Turai da kuma kasashe 19 - Argentina da Australia da Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Japan, Mexico, Rasha, Saudiyya, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, Turkiyya, Birtaniya da kuma Amurka.

Wani ƙaramin rukuni na G20 kan haɗu a matsayin G7.

Me yasa aka kafa G20, kuma me ya sa aka damu da ita?

An kafa ƙungiyar a 1999 bayan rikicin tattalin arziki na nahiyar Asiya. Asali, an tsara ta a matsayin zauren ministocin tattalin arziki da kuma jami'ai don lalubo hanyoyin tayar da komaɗar harkokin kuɗi.

Shugabanni sun fara haɗuwa ne a 2008 sakamakon rikicin tattalin arziki da ya faru a shekarar, da zimmar farfaɗo da haɗin kai tsakanin ƙasashe.

A ƴan shekarun nan, G20 ta faɗaɗa manufofinta don su ƙunshi sauyin yanayi da kuma makamashi mai ɗorewa.

Duk shekara akan sauya ƙasar da za ta jagoranci ƙungiyar kuma ita ce za ta tsara abin da G20 za ta sa a gaba a taron shekarar.

A kan me za a yi taron kuma su wane ne ke halarta?

A matsayinta na jagora a 2023, Indiya na son taron ya tattauna batutuwa kamar:

  • Cigaba mai ɗorewa
  • "Gwagwarmayar tabbatar da cigaban kowa da kowa a duniya ba tare da bambanci ba"
  • Yafe basuka ga ƙasashe masu tasowa

Ana kyautata zaton Shugaban Amurka Joe Biden zai tattauna da shugabannin ƙasashe masu tasowa game da shawarwarin yadda za a sauya fasalin Bankin Duniya, wanda zai iya kaiwa ga samun ƙarin kuɗin kashewa a wajen ayyukan raya ƙasa, da kuma batun sauyin yanayi.

Kazalika, akwai ganawa da yawa da za a yi tsakanin ɗaiɗaikun shugabanni a gefen taron.

Firamininstan Indiya Narendra Modi na son taron ya fito da ƙasarsa a matsayin babbar ƙasa a duniya, da kuma shi kansa a matsayin shugaba mai muhimmanci tsakanin ƙasashe gabanin zaɓen da za a yi cikin 2024 a ƙasar.

Zai yi ƙoƙarin ganin maganar yaƙin Ukraine ba ta mamaye taron ba kamar yadda aka yi a taron 2022 da aka yi a Bali na Indonesiya.

Ce-ce-ku-ce game da rikicin ya sa ba a iya fitar da sanarwar haɗin gwiwa ba bayan kammala taron ministocin harkokin wajen ƙasashen na G20 a watan Maris da ya gabata.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ba zai halarci taron ba. Zai aika ministan harkokin waje Sergei Lavrov.

Shi ma Shugaban China Xi Jinping ba zai je ba. Firimiyan China, Li Qiang, ne zai je a madadinsa.

Waɗanne abubuwa ne kuma za su iya jawo ce-ce-ku-ce?

A watan Mayun 2020, China da Saudiyya suka ƙaurace wa taron G20 kan yawon buɗe-ido da aka yi a yankin Kashmir na Indiya, saboda ita ma Pakistan na iko da wani ɓangare na yankin.

Haka nan, kwanan nan hatsaniya ta ɓarke tsakanin Indiya da China bayan Beijing ta saki wata tasawira inda take iƙirarin mallakar jihar Arunachal Pradesh da kuma tsaunin Aksai Chin a matsayin nata.

Amurka ta nemi China ta jingine rikicin da take yi da Indiya don mayar da hankali kan "taka rawa mai amfani" a taron.

Mene ne G20 ta cimma?

Yayin taron tarukan 2008 da 2009, daidai lokacin rikicin tattalin arziki, shugabanni sun amince da wasu matakai na farfaɗo da tattalin arzikin duniya.

Amma masu sharhi na ganin tarukan da suka biyo baya ba su yi wani tasiri ba, akasari saboda adawar da manyan ƙasashen duniya ke yi da juna.

Sai dai kuma, ganawar da ɗaiɗaikun shugabanni ke yi juna kan amfanar a lokuta da dama.

Misali, a taron 2019 da aka yi a Osaka na Japan, shugaban Amurka na lokacin Donald Trump da takwaransa na China XI Jinping sun amince su ci gaba da tattanawa don kawo ƙarshen rikicin kasuwanci tsakaninsu.

Waɗanne batutuwan tsaro ne za a tattauna kan su a taron?

Tarukan G20 kan jawo zanga-zangar ƙin jinin dunƙulewar duniya wuri guda.

Gwamnatin Indiya na ta tsaurara tsaro a Delhi kafin taron.

AN rufe titunan da ke kaiwa wurin taron, yayin da aka tura jami'an tsaro 130,000 a faɗin birnin.

Haka nan, an ɗauki matakan hana birai masu tsokana zuwa wurin taron.

Birnin Delhi na da birai masu yawa kuma hukumomi na son hana dabbobin kawo matsala ga taron.