Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Girgizar ƙasar Moroko: 'Masu aikin ceto na fuskantar cikas'
Ƙungiyoyin agaji na kokawa kan rashin samun damar isa ƙauyukan da girgizar ƙasa ta yi wa illa domin kuɓutar da mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.
Caroline Holt jami'a a ƙungiyar agaji ta 'Red Cross' da 'Red Cresent' ta ce matsalolin da masu aikin ceton ke fuskanta suna da tarin yawa.
Ta ƙara da cewa ana buƙatar manya-manyan motoci gyaran titi domin share wa ƙungiyoyin agaji hanyar isa ƙauyukan da ke tsananin buƙatar agajin.
A ranar Juma'a da daddare ne girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske ta afka wa ƙasar Moroko, lamaroin da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 2,000
Yadda aikin ceton ke gudana
Fadar Masarautar Moroko ta ayyana makokin kwana uku a ƙasar, domin alhinin waɗanda suka mutu.
Haka kuma gwamnatin ƙasar ta umarci dakarun sojin ƙasar su tallafa wajen kai kayan abinci da magunguna da barguna ga mutane da lamarin ya shafa.
Tuni dai sojojin ƙasar suka share babban titin ɗaya daga cikin nyankunan da bala'in ya shafa, domin samun damar kai kayan agaji ga mutanen yankin.
Zaizayar ƙasa ta rufe titin ƙaramin garin Asni mai manyan tsaunuka.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 300,000 ne girgizar ƙasar ta shafa a garin Marrakesh da garuruwan da ke zagaye da shi.
'Na rasa duk 'yan uwana'
Wata mata a birnin Agadir, ta shaida wa BBC cewa ta rasa duka 'yan uwanta huɗu sanadaiyyar girgizar ƙasar da ta shafi yankinsu.
Matar mai suna Hakima, ta ce makwabta ne suka fitar da su daga cikin ɓaraguzan gidansu da ya rushe a ƙauyen Msouna.
"Dangina sun rasa gidajensu, tare da duk abubuwan da suka mallaka, babu abin da ya rage musu," in ji Hakima.
Ta bayyana yanayin da ''mummunar bala'i'' tare da cewa babu wani kayan agaji da ya isa ƙauyen Msouna da sauran ƙauyuka.
An samar da asibitocin wucin-gadi
Asibitin garin Amizmiz ya kasance tamkar kufai, sakamkon yadda girgizar ƙasar ta lalata wani ɓangare na asibitin.
A don haka ne, mutanen garin suka samar da wani tanti a wajen asibitin, inda aka riƙa kwaso marasa lafiyar da ke kwance a asibitin zuwa wannan tanti.
Motocin daukar marasa lafiya da kekuna ɗaukar marasa lafiya na ci gaba da jigilar marasa lafiya zuwa asibitin.
Wani jami'i a asibitin da ya buƙaci BBC ta sakaya sunansa ya ce kusan gawarwaki 100 aka kai asibitin a ranar Asabar.
“Na yi kuka saboda akwai mutane da dama da suka mutu, musamman ƙannan yara,"
Unesco za ta maitaka wa Moroko sake gina wuraren tarihi
Hukumar raya al'adu da ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya Unesco ta ce za ta taimaka wa Moroko domin sake gina wuraren tarihin ƙasar da girgizar ƙasar ta shafa.
Tsohon birnin Marrakesh - wanda girgizar ƙasar ta shafa sosai - na da wuraren tarihi na duniya masu yawa.
Shugaban Unesco na ƙasar Eric Falt ya ce yana da matuƙa muhimmanci a tsara yadda za a sake gina wurare da abubuwan tarihin da suka lalace.
Marrakesh ne babban wurin da masu yawon buɗe ido suka fi ziyarta a Moroko. Ana sa ran birnin zai karɓi baƙuncin masu ziyara miliyan 13 a shekarar 2023.
Adadi mafi yawa da birnin da taɓa samu tun bayan wucewar annobar Korona.
Tallafin masu aikin ceto daga ƙasashen duniya
Gidauniyar UK-Med ta Birtaniya na shirin aike wa da tawagar ƙwararun masu aikin ceto zuwa Moroko ranar Litinin domin tallafawa wajen kuɓutar da mutanen da suka maƙale cikin ɓaraguzai.
Wightwick na daga cikin tawagar masu aiken ceton da za a aike zuwa Morokon, ya kuma shaida wa BBC cewa babban abin da suke buƙata shi ne isa yankunan da girgizar ƙasar ta fi ƙamari, musamman wurare masu taunuka.
"Za mu duba yadda za mu kafa ƙananan cibiyoyin lafiya na wucin-gadi a wuraren, tare da duba yiwuwar samar da manyan asibitoci a yankunan".
"Muna tattaunawa da ma'aikatar lafiyar ƙasar, da hukumomin asibitocin ƙasar da sauran al'umma yadda za mu tunkari aikin".
Majalisar Dinkin Duniya na tsara yadda za a samar da masu aikin ceto daga ƙungiyoyin agaji na duniya domin taimaka wa Moroko.
Ƙasashen Sifaniya da Jamhuriyar Czech sun tura tawagogin aikin ceto, yayin da Faransa ta ce za ta tallafa wa Moroko da taimakon da take buƙata.