Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake cinikin takardun kuɗi don kauce wa tsadar rayuwa a Zimbabwe
"Kowa na ganin sayar da kaya a kan titina ita ce hanya mafi sauki ta tafiyar da rayuwa, amma dole sai ka zama mai basira."
Noel Ngwenya, mai shekaru 44, daga gundumar Chivi da ke Lardin Masvingo kan shafe kwanakin aikinsa a tsakiyar Bulawayo, birni na biyu mafi girma a kasar, yana tallata hajarsa ta hanyar yin amfani da lasifika.
Ya kan karbi lalatattu ko yagaggun takardun kudaden kasar waje da manyan shaguna ko wasu ‘yan kasuwa ke kin karba – akasari dalolin Amurka ko kudin rand na Afirka ta Kudu, kudaden da aka amince a yi amfani da su a Zimbabwe.
Mista Ngwenya na biyan abokan huldar kasuwancinsa kashi 50 bisa dari na darajar ko wane irin takardar kudi suka kawo masa – don haka suna samun dalar Amurka daya kan yagaggiyar dalar Amurka 2 ko rand 100 a kan yagaggiyar takardar kudi 200 ta rand.
"Abubuwa sun tabarbare lokacin annobar korona, kamar kowa ya fito kan titi yanzu yana sayar da wani abu, tun da babu wani gurbin aiki a masana’antu,’’ kamar yadda ya bayyana.
Alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Zimbabwe ya fuskanci koma baya tun a watan Agustan shekarar 2022 lokacin da ya kai kashi 285 bisa dari.
Amma kuma a cikin watan Maris din wannan shekarar har yanzu yana tafiya a kan kashi 87.6 bisa dari, tare da tilasta wa ‘yan kasar ta Zimbabwe neman wata hanyar tafiyar da rayuwa.
Wani sabon rahoton Kungiyar Kwadago ta kasa da kasa a birnin Harare ya bayyana cewa kashi 76 bisa dari na guraban aiki a kasar Zimbabwe yanzu a bangaren da ba na gwamnati ba ne, alal misali sayar da kayyaki da gudanar da ayyuka ba tare da yin rajista da hukumomi ba.
Tattalin arzikin da ba na bangaren gwamnati ko kamfani ba, da karuwar cajin kudi a bankuna da rashin yarda da harkokin bankuna na nufin ‘yan kasar Zimbabwe sun fi bukatar yin hada-hada ta takardu ko tsabar kudi ko kuma kudi ta manhajar intanet.
Mista Ngwenya ya bayyana kansa a matsayin wakili na wadanda ke da mutane a Amurka da Afirka ta Kudu da bankunan kasar, inda suke musayar yagaggun takardun kudin ko wadanda suka yi datti da sabbin takardun kudin.
Su kan ba shi kamasho a duk lokacin da suka karbi yagaggun takardun kudin.
Mista Ngwenya mai aure da ‘yaya biyar, na hada sana’arsa ta sayen yagaggun takardun kudin da sayar da ‘yayan itatuwa da gasasshiyar masara.
"Abubuwa na tafiya daidai a baya, amma a yanzu kasuwancin ya ja baya,’’ ya ce. ‘’ A wasu lokuta ka kan taki sa’a ka samu wani ya kawo maka yagaggun takardun kudi na dala 100, wasu ranakun sai ka ga ka tashi da takardun kudin dala daya ko dala biyu.’’
Shekaru da dama na cin hanci da rashawa da durkushewar tattalin arziki sun haifar da lalacewar hanyoyin kasar da na cikin manyan birane. Hakan na nuni da wata dama ga Mayibongwe Khumalo, mai shekaru 25, daga yankin Cowdray Park, da ke da nisan kilomita 25 daga yammacin birnin Bulawayo.
Daya daga cikin mutane da dama ne da ke yi wa ramukan hanyoyi ciko a fadin birnin da kan samu ladan kudi kadan daga masu wucewa a kan ababan hawa da kan tausaya.
"Mu kan cike ramukan kan titina saboda yadda yanayinsu ke ci wa direbobi tuwo a kwarya. Ba ni da kudi, don haka ina fatan zan samu abin kashewa amma ba na son in yi bara kamar wani makaho,’’ Mista Khumalo ya bayyana.
"Muna da masu larurar gani da dama a Bulawayo da masu ababan hawa yanzu ba su damu da matsalolinsu ba. Ina da karfi da koshin lafiya don haka babu wanda zai jefe ni da kudi.
"Na yi amanna da gyara hanyoyi, wadanda ke mutunta irin abin da nake yi kan bani wani abu. A rana mai kyau irin ta yau, ina samun dala 9 da kuma rand 100 da kuma daruruwan dalolin Zimbabwe (ZWL$).
"Hakan na nufin ba zan koma gida wajen iyalai na babu komai a hannu ba. ‘Yayana uku da matata za su iya yin juriya, gobe ma wata rana ce.’’
Mista Khumalo ya yi aikin tukin wata ‘yar karamar motar bas da kuma na tashar mota, kana yakan yi sana’ar waka a matsayin dan amshi ga wani fitaccen mawaki da ke yin wakar tjibilika – salon wakokin da kan tabo harkokin zamantakewa.
Cikin ‘yan kasuwar Zimbabwe miliyan biyar da dubu dari biyu da aka kididdige a fannin tattalin arzikin da ba na aikin gwamnati ko kamfanoni ba, kashi 65 bisa dari daga ciki mata ne.
Gwamnati na son ta bunkasa wannan bangaren tattalin arziki mai bunkasa, a wani bangare ne tsare-tsaren kasa wajen kara samun kudin shiga na haraji.
Tana kuma matsa wa kananan masana’antu da ‘yan kasuwa, tare da aikewa da jami’an tsaro don duba lasisin kasuwanci tare da cin tarar wadanda basu bi doka ba
Sukoluhle Christine Malima, mai shekaru 36, na tafiyar da wani wurin cin abinci a cikin wani tsohon bodin motar tirela a wata tashar mota a birnin Bulawayo.
Ta kuma bayyana cewa yana da matukar wahala a iya ajiye kudin yin rajistar kasuwancin, don haka ana tilasta mata biyan tarar dala hudu.
"Shirin da nake yi shi ne in tara kudin da zan yi lasisin kasuwancina amma yawan kame da karuwar gogayyar kasuwanci sun sa abubuwa kara tsauri. A ko wane lokaci ka ware wasu kudade ka ajiye, ‘yan sanda kan dawo su duba lasisi don haka dole ka biya tarar da ba ka shirya biya ba.’’
Ms Malima na sayar da Sadza, kunun da ake yi da masara ko gero, da kuma miyar dage-dagen kaza kan dala daya kowane farantin cin abinci ga direbobin kananan motocin bas-bas da sauran masu sayar da kaya.
"Na kan sayi kazar gidan gona kan dala shida in datsa ta gida 12 wadda ke samar mani da faranti 12 na abincin Sadza da kaza, da kan samar min da dala 12 a ko wace rana.
Daga nan na kan rage dala daya na nau’in abincin da aka sarrafa da masara, sai dala daya da rabi na man girki kana sauran dala daya da rabi na sayen tumatiri da albasa, don haka ribata dala biyu ko dala daya da rabi ke nan a ko wace rana, wanda nake kokarin adanawa saboda tara kudin yin lasisi. Amma karaf sai ‘yan sanda su sake zuwa, sai in sake dawowa gidan jiya.’’
Mercy Tafirenyika, mai shekaru 51, wadda ke zayyanawa da dinka rigunan ma’aikatan jinya a tsakiyar birnin Bulawayo tun a shekarar 1999 ta kara bayyana irin yanayin damuwar da Ms Malima ke ciki.
Ta bayyana cewa gogayyar sana’ar na dada karuwa ne a yayin da sauran mutane suka koma sana’ar dinki don samun karin kudaden shiga. Yawan daukewar wutar lantarki a kasar na rage yawan sa’oin da za ta iya yin aiki sannan ga tsadar kayan aiki na karuwa.
Ms Tafirenyika na yin aiki daga cikin wani rukunin gidaje da aka mayar zuwa shaguna da ofisoshi ga kanana da manyan ‘yan kasuwa. Ta kuma ce kasuwancinta na bin dokar yin rajista da kuma biyan haraji, amma kuma karamar hukumar birnin Bulawayo ta shaida mata cewa lasisin shaguna ba su da tasiri a cikin gidaje, kuma ba za ta iya sauya wuri ba.
"A baya a yau, na je wajen bikin jana’iza, kuma ‘yan sanda sun zo sun tafi da daya daga cikin matan da nake aiki tare da su inda suka bukaci a biya tarar dala dubu 28 a madadin lasisin shagon.
"Abin da ke damuna shi ne cewa ba sa bayar da hadin kai. Wancan lokacin da suka zo nan na tambaye su su fada min irin takamaimen lasisin da suke bukata, amma a maimakon ba ni amsa sai suka fusata suka tasa keya ta zuwa caji ofis inda na sake biyan wata tarar.
"Ba ina kokarin kin bin doka ba ne; Kawai dai ina bukatar karin haske a kan lasisin amma babu wanda ya iya bayar da wata gamsasshiyar amsa.’’
Ms Tafirenyika ba ta san yadda makomarta za ta kasance ba. A yayin da fadi-tsahin rayuwa ke kara tsauri, wanda tsananin hauhawar farashin kayyaki, da tsadar rayuwa, da rashin aikin yi a ko ina suka kara haddasawa, ga kuma yadda ‘yan kasar Zimbabwe da dama ke cikin damuwa.
Kamar yadda wani sanannen batu a shafin sada zumunta ‘yan kasar Zimbabwe ke cewa: " Cikar burin dan Zimbabwe shi ne ka bar kasar Zimbabwe."