Me ya sa maulidin Touba ke ɗaukar hankali a Senegal?

Asalin hoton, Getty Images
A kowace shekara miliyoyin Musulmi kan taru a Touba, wani birni mai tsarki a tsakiyar Senegal don taron halarta taron maulidin Ahmadou Bamba da ake yi wa laƙabi da 'Grand Magal' a ƙasar.
Wani gagarumin taron adduʼoʼi ne da nufin girmama shehin malamin.
Taron na Touba na girmama tafiyar da Sheikh Ahmadou Bamba, wanda ya samar da ɗariƙar Mouridi, ɗaya daga cikin ɗariƙun Sufaye mafi ƙarfi a ƙasar.
Taron ya kasance ɗaya daga cikin tarukan addini mafi girma a Senegal, kuma ɗaya daga cikin tarukan ibada mafi girma ga Musulmi a Yammacin Afirka.
Haɗuwar kan kasance wata haɗuwar ƙarfafa ibada, da nuna alʼada, da ƙarfafa alaƙa tsakanin alʼumma da kuma ƙarfin tattalin arziƙi, wadda ke buƙatar samar da kayan aiki masu yawa a ɗan ƙanƙanin lokaci.
Mene ne asali da maƙasudin taron ibadar?
Taron ibada na Touba ne babban taron addini a Senegal kuma ɗaya daga cikin tarukan ibada masu muhimmanci a Afirka.
Taron da ake yi a ranar 18 ga watan Safar na kowacce shekarar Hijira na girmama tsugunar da Sheikh Ahmadou Bamba, jagoran ɗariƙar Mouridi a Afirka.
Sojojin mulkin mallaka na Faransa ne suka kama shi a shekarar 1895, daga nan suka mayar da shi Gabon kan zargin neman assasa tawaye.
Amma ga Muridai, tunawa da wannan tafiyar ta kasance wata ibada a ɗariƙarsu domin nuna godiya ga Allah saboda a cewar tarihi, Sheikh Ahmadou Bamba ko Serigne Touba - kamar yadda ake kiransa - bai ɗauki wannan tafiyar da ya yi a matsayin horo ba, fyace wata hanya ta samun ɗaukaka a addinance.
Kalmar "Magal" wadda ke nufin nuna murna a yaren Wolof, ta ayyana wannan biki da Muridan ke yi a duk ranar 18 ga watan Safar na kowacce shekara.
Tsawon shekaru, taron Magal ya tashi daga wani ƙaramin biki zuwa babban taro na ƙasa da ke janyo dubban mutane daga faɗin Senegal da ma duniya baki ɗaya.
Babban taron Touba rana ce ta ibada, da nuna ƴan'uwantaka da kyauta da kuma shirye-shiryen aikin alfahari.
Taron ya ƙunshi manyan abubuwa hudu - wato ibada da zumunci da tattalin arziƙi da kuma siyasa.
Wane ne Sheikh Ahmadou Bamba Jagoran Touba?

Asalin hoton, GETTY
An haifi Shehin malamn addinin a shekarar 1853, inda ya rayu har zuwa 1927.
Cikakken sunansa shi ne Ahmadou Bamba Mbacké.
Wani babban mutum ne a tarihin Senegal kuma jagoran addini da ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar addini da zamantakewar ƙasar.
Ana girmama shi ba wai don tsantseni da karatunsa ba kawai, har ma da yadda ya nuna rashin amincewa da mulkin mallakar Faransa ba tare da rikici ba.
An haifi Sheikh Ahmadou Bamba a shekarar 1853 a Mbacké, da ke yankin Diourbel, a tsakiyar ƙasar.
Adawarsa ga mulkin mallakar Faransa ya haifar masa da zaman gudun hijra a wurare da dama, amma hakan ya ƙara masa girma tsakanin mutanen ƙasar.
Shi ne kuma ya assasa garin Touba, wanda tsawon lokaci ya zama wata cibiyar addini da tattalin arziƙi ga tafiyarsa da kuma dukkanin Musulmi.
Touba: Birni mai tsarki

Asalin hoton, Getty Images
Touba, gari ne mai tsarki da Sheikh Ahmadou Bamba ya kafa a 1887, kuma shi ne ruhin tafiyar Muridan ɗariƙarsa.
A garin Babban Masallacin Touba yake, wani wurin ibada mai ɗaukar ido, kuma a nan ne kaburburan manyan jagororin ɗariƙar suke.
Tafiyar Sufanci ta Muridai, wadda aka samar a ƙarni na 19, na daga cikin muhimman ƙungiyoyin Musulmi a ƙasar kuma ƙarfin faɗa a ji na tafiyar a siyasar Senegal na da yawa.
Masu ibada na cincirindo zuwa birnin na Touba, inda babban masallacin yake, hakan ya kasance wata babbar shaida ta girman ga Sheikh Ahmadou Bamba.
Duba da kyakkyawan tsarinsa da kuma yanayi mai kwantar da hankali, Babban Masallacin ya kasance wani dandali na bukukuwa, kuma wata mahaɗa da ke haɗa masu ibada kan wani buri guda.

Asalin hoton, RTS
Tun bayan assasa ɗariƙar ta samu jagorori aƙalla takwas da suka ja ragamar ɗarƙar, inda a halin yanzu Serigne Mountakha Bassirou Mbacké ne Khalifan ɗariƙar tun Janairun 2018.
Khalifan na takwas a tafiyar Mouridan mutum ne da mutane suka amince da shi.
Ana masa kallon wani mutum maras haniyya, mai gaskiya kuma mai son mutane.











